Ticker

6/recent/ticker-posts

5.5.2 Lansika

 

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.5.2 Lansika

 Jagora: Lansika, inna lansika.

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Mata dangin Fatima.

Amshi: Kulle.

 Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi.

Amshi: Kulle

Jagora: Mata dangin Fatima.

Amshi: Kulle.

Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi.

Amshi: Kulle.

(Mata Dangin Fatima)

Ita ma wannan waƙa kalmar “kulle” ita ce amshinta. Kalmar kulle ba ta ɗauke da wata ma’ana da aka sani a harshe wadda za a ce ga abin da take nufi, don haka ita ma kalmar amshi ce maras ma’ana. A lura da cewa rubutattun waƙoƙin da ake amfani da su wajen bara, mabarata na ƙoƙarin su sama masu amshi ko da ba su da shi. Haka na faruwa a cikin taro ko a kaɗaice. Misali, a waƙar Imfiraji mabarata na yi mata amshi da:

 Mai sadaka Ala karɓa,

 Ala sa mu ga shugaban Ma’aika.

Haka ma sauran waƙoƙi mabarata kan yi ƙoƙari su sa mata amshi wanda zai yi daidai da baransu.


Post a Comment

0 Comments