Ticker

6/recent/ticker-posts

5.13 Naɗewa - Daga littafin “Bara Da Wasu Waƙoƙin Bara A Ƙasar Hausa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa 

5.13 Naɗewa

Kamar yadda aka gani an yi tsokaci a kan irin sigogi da falsafar da ake iya samu a cikin waƙoƙin bara waɗanda ba a cika samunsu a sauran waƙoƙi ba. Wannan ya haɗa da kasancewar waƙoƙin gajeru ta fuskar yawansu da yawan layuka a cikin ɗiya da rawa da amshi na kalmomi masu ma’ana da marasa ma’ana. Ta ɓangaren falsafa kuma an ambaci abubuwa kamar matsayin masu bara da dangantakar Almajirai da mata da girmama ma’auraci da saka lalama ga neman abu da rashin tara/zaɓi ga wanda za a ba.

A lura! Bayanan da aka yi game da sigogin waƙoƙin bara ba a ambaci rubutattun waƙoƙin da ake bara da su ba. Dalili shi ne su ba domin a yi bara da su aka wallafa su ba. Wannan shi ya sa suke bisa sigogin da falsafar rubutattun waƙoƙi waɗanda aka saba da su. Abinda kawai aka amabata na siga wanda masu bara ke saka masu ita ce amshi kamar yadda aka ambata. Bayan siga da falsafa sai kuma saƙo, wato jigogin waƙoƙin. Sai a babi na gaba mu shiga cikinsu domin tantance yadda lamarinsu yake.


Post a Comment

0 Comments