Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
5.12 Rashin Zaɓi Ga Wanda Ake
Ba
Wata falsafar da ake iya hangowa a
cikin waƙoƙin bara ita ce
rashin zaɓi ga
wanda ake baiwa. Idan mutum roƙo yake yi, to
ba ya da zaɓi ga
abin da za a ba shi. Zaɓi na ga
hannun mai bayarwa. Misali:
Ni ne ɗan kwalak-kwalak,
Ni ne ɗan kulodo mai bara.
Komi anka ba ni ci nikai.
Ko kashi anka ba ni ci nikai.
Amma ban da kashin bulala.
(Ɗan Kulodo)
Layi na uku da na huɗun na ɗan waƙar da ya gabata
ya nuna almajirai na sane da cewa wanda za ba ba ya da zaɓi, sanin haka ya sa suke ambatawa a cikin waƙoƙin na bara cewa
suna sane da haka tare da nuna kada mai ba su ya ga kamar abin da zai ba su ba
zai karɓu ba, a’a ya ba
su za su yi amfani da shi haka nan yadda yake. Ke nan sun nuna suna sane da
maganar hikimar Bahaushe mai cewa “mai jiran a ba shi ya sha tasko.” Haka ma
Bature na cewa “a begger has no choice.” Daɗaɗɗar
maganar hikima ce cewa duk wanda zai roƙa a ba
shi to zai iya fuskantar kowane wulakanci. Sai dai su masu bara musamman
Almajirai suna daure ma haka ne domin cim ma wata biyan bukata a nan gaba duk
da yake suna sane da wulakanci kuma suna ambaton haka a cikin waƙoƙin nasu na
bara. Ga ma ƙarin wani
misali:
Jagora: Inna ki
hanƙure ki ba ni na Allah.
Amshi: Karigizo.
Jagora: Inna ko
hurar da ta kwan goma.
Amshi: Karigizo.
(Karigizo)
A wannan ɗan ma a layi na biyu an nuna komai abu ya lalace mai bara
shirye yake ya karɓe shi
domin ba ya da zaɓi kuma
ya shirya fuskantar wannan tasko.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.