Ticker

6/recent/ticker-posts

Allazi Wahidun

5.13 Allazi Wahidun

Wannan ma wasa ne na yara maza. Misalin yara biyu ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa.

5.13.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Wasan na dandali ne.

ii. An fi gudanar da shi da dare, musamman yayin da akwai farin wata.

5.13.2 Kayan Aiki

i. Takalma

ii. Ƙwallon goruba

iii. Bishiya ko katanga ko wani abin da aka sanya a matsayin sha.

 

5.13.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya ba bisa ƙa’ida ba. Sannan wannan wasa ba ya da shugaba ko limami. Kowanne daga cikin ‘yan wasa zai nemi takalmi ya riƙe a hannunsa. Daga nan za a sanya ƙwallon goruba a tsakiya, sannan a yi waƙa kamar haka:

Allazi wahidun,

Mai rabo sa’a,

Marar rabo sai haƙuri.

 

Daga nan za a fara hanƙoron buga wannan ƙwallon goruba da takalman da ke hannun yara. Kowa zai riƙa ƙoƙarin buga ƙwallon gorubar zuwa ƙafar wani. Wanda aka bugo zuwa gare shi kuma zai yi tsalle don kada ta taɓa ƙafarsa, ko kuma ya sanya takalmi ya buge ta zuwa wurin ƙafafun wani daban. Haka za a ci gaba da yi, kowanne yaro yana ƙoƙarin ƙwallon gorubar ta taɓa ƙafar wani.

Duk wanda ƙwallon gurubar ta taɓa ƙafarsa, to shi ne allazi, kuma za a bi shi da duka da takalman da ke hannun ‘yan wasa. Wanda ake duka zai yi ta gudu domin ya je wurin sha. Da zarar ya sha to ya tsira.

 

5.13.4 Sakamakon Wasa

Sakamakon wanda ƙodagon goruba ya taɓa ƙafarsa shi ne duka da takalma. Zai yi ta gudu domin ya sha. Ba za a bar shi ba har sai ya sha.

 

5.13.5 Tsokaci

Wannan wasa yana koyar da jarumta da juriya ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Sannan masu wasa sukan samu nishaɗi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments