Ticker

6/recent/ticker-posts

5.1.1.1 Gajartawa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.1.1.1 Gajartawa

Gajartawa a nan na nufin taƙaita abu, wato a yi shi taƙaitacce domin wata manufa. Gajartawa na ɗaya dag cikin sigogin da waƙoƙin bara suke da ita saɓanin waɗanda ba na bara ba. Ga dukan alama, an fara bara ne da waƙoƙin baka kafin a fara yi da rubutattu domin sai da aka yi almajirci ne kafin a zama malam har a iya rubuta waƙa. Haka ma ga dukan alama baran almajirci ne aka fara yi a ƙasar Hausa kafin na manya masu naƙasa da masu lalurori kamar yadda aka ɗan nuna haka a babi na uku. Wannan shi ya sa waƙoƙin bara suke gajeru, domin yara ne ke amfani da su, su kuwa waƙoƙin da yara ke ta’amulli da su gajeru ne kamar yadda Dunfawa (2020) ya ambata. Wannan siga ta gajarta ga waƙoƙin bara kashi biyu ce; gajarta layi da gajarta ɗa.


Post a Comment

0 Comments