Ticker

6/recent/ticker-posts

5.1.1.1.1 Gajarta Yawan Layuka A Cikin Ɗa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.1.1.1.1 Gajarta Yawan Layuka A Cikin Ɗa

Ɗa a waƙar baka yakan ƙunshi layi ɗaya ko biyu ko ma fiye gwargwadon wurin da mawaƙi yake tsayawa ya numfasa.

Ɗa shi ne jerin kalmomin da ake shiryawa cikin layuka. Shi ne kuma wanda jagora yakan yi ko ya soma rera wani layi daga cikinsa, sannan Amshi su karɓa”. (Gusau, 2003:57).

Ɗiyan da ake samu a cikin waƙoƙin bara gajeru ne amma ɗauke da saƙo cikakke. Da yawa za ka taras ɗiyan waƙoƙin bara layi ɗaya ne wani lokaci biyu.Amma rubutattun waƙoƙin da ake bara da su ba dole su kasance da wanna sigar ba. Misali, waƙar “Mata Dangin Fatsima”

 Jagora: Lansika, Inna lansika.

 Amshi: Kulle.

Jagora: Mata dangin Fatima.

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Ku taru ku bamu na Annabi.

 Amshi: Kulle.

Jagora: Kowab ba mu na Annabi.

 Amshi: Kulle.

 Jagora: Allah na gode mashi.

 Amshi: Kulle.

 (Mata Dangin Fatsima)

Wannan waƙar da ta gabata duka ɗa takwas ne take da shi, kuma kowane ɗa layi ɗaya ne. Wato ke nan ɗiyan waƙoƙin bara da yawansu ba su ƙumsar layuka da yawa kamar sauran wasu waƙoƙin baka da ba na bara ba.


Post a Comment

0 Comments