Ticker

6/recent/ticker-posts

4.8.4 Nishaɗantarwa/Raha

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.8.4 Nishaɗantarwa/Raha

Farin ciki da raha ga al’da kan sa ɗan Adam ya yi kyauta ciki har da sadaka. Sanin haka ne ya sa mabarata ke amfani da waƙoƙi wajen domin a wani lokaci su shigar da nishaɗi da raha ga zukatan waɗanda suke yi wa bara da zimmar su zaburar da su sa ba su sadaka. Misali:

 “Ya Allahu Ya Tabaraka ya Rabbana,

 Kura ta ga Ɗan bara ɗan almajiri,

 Bari in bika ɗan bara in shawo gari,

 Tahiyata da taki ba ta zama ɗai da ɗai,

 Ni roƙo ni kai ga mata ‘yan arziki,

 Ke ƙwace ki kai ga mata ba su ba ki ba,

 A ɗebo da kaɗan-kaɗan a ba ɗan almajiri,

 Inna in ba ki ba ni ba inai maki kukan gada,

 ‘Yaaaa meeeee.

Wannan waƙar na nuna irin dangantakar kura da mata don tsoron ta suke yi don haka ne almajirin kan kawo ta ya kuma nuna irin rashin jituwar da ke a tsakaninsa da kurar, duk lokacin da mata suka ji wannan rashin jituwar sukan sami nishaɗi har su yi wa almajirin sadaka.

A wata waƙar kuma almajirai suna raha don su samar da nishaɗi ga jama’a:

To bismilla Rabbana

Zani karatun magani

Ko na ciki ko na haihuwa,

Ko na korar kishiya

Kogon kura na shiga

Ko na damisa na shiga

Sai tat taso man tsaye

Sai nic ce wa zaki ci

Sai tac ce mai magani,

Sai na baɗe ta da magani

Kahin a jima ban gan ta ba

In na baki kar ki sha

In kin sha kin tsimbire.

Babu ruwana na tahi

O! Allah na magani,

Ƙuli-ƙuli na magani,

Kowac ce bai magani,

Ya tambayi ‘yan tafasa ya ji,

To Allah mai magani.

(Karatun Magani)

A wannan waƙar da almajirai ke amfani da ita wajen bara akwai raha domin almajirai ne ke yin waƙar waɗanda ‘yan shekara shida ne zuwa goma sha huɗu, ita ma wannan an nuna kura kamar waƙar da ta gabata da kuma wani babban abu mai saurin jan hankalin mata wato kishiya. Dubi yadda yake bayar da maganin a waƙar tasa, “abin dariya wai yara sun tsinci haƙori”, sai ka ce boka? Wannan rahar tana nishaɗantarwa kuma mafi yawan lokaci sai masu saurare sun ƙyalƙyace da dariya idan sun ji almajiri yana wannan waƙar daga baya sai su ba shi sadaka. Bugu da ƙari a lokacin da waɗannan almajiran suke wannan waƙar da wasu irinta kamar lantika inna lantika suna rangaji tare da marairaicewa ko ɓata fuska ko harara duk dai don su bayar da dariya ga jama’a har sai an ba su sadaka sannan sai su ƙara gaba.


Post a Comment

0 Comments