Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.8.3 Ƙimar Ilmi/
Ilmantarwa.
Ilmi abu
ne mai ƙima ga idon mutane bale ma a ce ilmin addini. Sau da yawa mabarata kan yi
amfani da waƙa wani lokaci ma ta Larabci ba tare su kansu sun san
ma’anar da ke ƙunshe cikinta ba, haka su ma masu saurare. Da yake
masu sauraren sun san waƙar ta ilmi ce sai su riƙa ganin ƙimar mai rera ta. Ganin wannan ƙimar da mabarata suka san mutane na da ita ga ilmi, shi ya sa wani lokaci
suke amfani da waƙa wajen bara, domin a dube su da ƙimar ilmi a kuma ba su sadaka. Misali :
1. Ya arhamar rahamani bani abin
nufi,
Zancen da zan yi kas shi faɗi ga banza.
2. Kai mai kiran sallah ka san
wada zaka yi,
Ka yi hattara don ba a yi nai
banza.
-----------------------------------------------------
6. Don na ga ƙattan ƙauye wasa ɗai su kai,
Sai sun gaza suka fasa kuwwar
banza.
------------------------------------------------------
16. Allahu akbar in kiran sallah
ka kai,
Don kak ka ce Ala ka faɗi ga banza.
17.Wanna alihin ɗamre kablasan shikai,
Kak ka ce akabar a bar ka ga
banza.
18. Akubar da akabar wanga dud
dulginku na,
Juhala’u kau da ka buɗe baki banza.
(Maharazu Barmo Kwasare: Waƙar Kiran sallah)
Wannan
waƙa mabarata suna amfani da ita wajen
bara tana koyar da ilmin kiran sallah ne, duk wanda ya saurari wannan waƙar yakan ba ta wata ƙima saboda ilmantarwar da take ɗauke da shi. Har saboda
hakan sai su riƙa samun sadaka
daga masu sauraren baran nasu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.