Ticker

6/recent/ticker-posts

4.8.2 Faranta Rai

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.8.2 Faranta Rai

Mai neman abu daga hannun wani zai yi duba tare da lura da abinda ke faranta ran wanda zai nemi abu daga hannunsa. Mabarata na lura da haka, shi ya sa suke neman waƙoƙi masu ƙunshe da wasu jigogi da suke ganin za su iya faranta wa waɗanda za su yi wa bara su riƙa rera masu su domin samun sadaka daga hannayensu. Misali, kamar begen Annabi, wanda duk Musulmin ƙwarai zai so ya ji ana begensa. Ga misali:

 Jagora: Ya bisimilla Allah,

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: Za ni yabon Muhamman

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: Mai birnin Madina

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: A ba mu domin Allah

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: In da rabo da niyya,

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: Don Shi ba don mu ba,

 Amshi: Ɗan Amina

 Jagora: Mai daraja Muhamman,

 Amshi: Ɗan Amina.

 (Ɗan Amina)

Wannan waƙa da ta gabata yabon Annabi ne ƙunshiyarta. Kamar yadda aka faɗa can baya cewa, ɗaya daga cikin dalilan da suke sa mabarata yin amfani da waƙa a wajen bara shi ne faranta wa waɗanda suke yi wa bara. Yabon Annabi na cikin abubuwan da ke faranta wa Musulmi rai. Wannan ya sa da yawa daga cikin waƙoƙin da mabarata ke rerawa a lokacin bara suna ɗauke da yabon Annabi ne, da zimmar saka farin ciki ga zukatan waɗanda suke yi wa bara har su ba su sadaka. Ga wani misali daga rubutattar waƙa.

1.                     Almiski har kafur ku san duka ba su kai,

 Ƙamshi na al’udin jiki na Muhammada.

2.                     Hakanan ga kyawu ko ga zati ba wa shi,

 Don babu ko dukka Kaman na Muhammada.

3.                     Ba a yo ga tahalikai kama tai nan ɗaiɗai,

 Ba za a yi abadan kama tasa, Ahmada.

4.                     Hakana ga halki masu sha’wa ba wa shi,

 Fara’a da kyawun murmushi na Muhammada.

 (Nana Asma’u: Kirarin Amada)

Waɗannan baitoci da suka gabata yabo ne zuwa ga Annabin rahama Muhammad (SAW). Baitocin suna ambaton daraja da fifiko wanda Annabi yake da shi a kan sauran Annabawa. Haka baitocin sun ƙunshi mu’ujizojin Annabi da Allah ya keɓe shi da su. Ambaton waɗannan na shigar da farin ciki ga Musulmi masoya Annabi. Mabarata suna lura da haka ƙwarai, suna aikata ko rera abin da suka san waɗanda suke wa bara suna so, domin haka na sa su sami sadakar. Umar (2002) ya ba da irin wannan misali na wani kuturu da ke amfani da tutar NEPU da ta NPC wajen bara. Ya ɗaura ta NEPU idan ya je garin da NEPU ta fi yawa, ya kuma ɗaura ta NPC idan ya je inda NPC ta fi yawa. Duk wannan domin faranta wa waɗanda ake yi wa bara ne. Akwai irin wannan a cikin wata waƙar da mabarata ke amfani da ita wajen bara kamar haka

6. Ya Ilahil alamina,

 Taimakan ni in je Madina,

 In ji daɗi in yi murna,

 In ga ƙabarin ɗan Amina,

 Baban Kulsumu ɗan Suwaiba.

 -------------------------------------

46. Ga mu gun jikanka Shehu,

 Don isar Kakanka Nuhu,

 Rungume mu ka ce madihu,

 Wanda ke da uwa a murhu,

 Ba zai ci tuwonsa ba miya ba.

 (Aliyu Namangi: Imfiraji ta Farko)

Waɗannan baitocin waƙar suna faranta ran duk wani Musulmi a cikin al’ummar Hausawa, a cikinsu ne aka ambaci asalin Manzon Allah (SAW) ta hanyar ambaton iyaye da kakanninsa har ma da garinsa wanda jama’ar Musulmi ke burin su je don su kai ziyara. A lokacin da mabaraci ya rera waɗannan baitukan sai masu saurare su ji ransu ya yi daɗi har ya ɗauki wani abu su bayar sadaka zuwa ga mabaracin.


Post a Comment

0 Comments