Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
(Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.8.1 Tsoratarwa
Wa’azi shi ne tsoratar da mutane
da yin kira gare su ta hanyar ambaton azaba ga masu munana aiki da albishir ga
masu kyautatawa. Wa’azi na sa mai saurarensa tuna rayuwar gobe, wato lahira ya
sa zuciyarsa ta yi taushi, ya kuma sa mai suraren rage ganin Æ™imar duniya wanda hakan kan sa rowa. Idan aka yi sa’a
irin wannan saƙo ya shiga
zuciyar mai sauraro, to bayar da sadaka gare shi ba zai wuya ba, domin komawar
da hankalinsa ya yi ga rayuwar Lahira wadda bayar da sadaka na cikin abin da ke
sa kyautata zato samun kyawonta. Wannan babban dalili ne daga cikin dalilan da
ya sa mabarata ke amfani da waƙa wajen bara ta
baka da rubutatta da yake suna ƙunshe da
wannan. Ga misalin wasu É—iya
daga waƙar Laƙada
Raliyallahu anil Muminina.
Jagora: Je ki marowaci ka sake dubara.
Amshi: To.
Jagora: Ranar Lahira kana ci da
kuka.
Amshi: To.
Jagora: Kai kukan jini ka koma na
tilas.
Amshi: To.
Jagora: Ba ka da ɗan ƙane bare ɗan
aboki.
(Laƙada Raliyallahu anil Muminina)
Ɗiyan waƙar da suka gabata suna bayani ne ga irin sakamakon da ke
jiran marowaci wato wanda bai bayar da sadaka ga mabukata. Ɗiyan waƙar sun nuna
irin kuka da da-na-sani da wanda ba ya bayar da sadaka zai yi ta yi a ranar Ƙiyama lokacin da kukan ba ya da amfani kuma ba ya da wani
mataimaki a wannan lokacin. Wannan kamar bayanin wata aya ne da ke cewa:
“Kuma ku ciyar daga abin da muka arzitta ku tun gabani mutuwa ta zayyikke ma É—ayanku sadda zai ce ya ubangiji da ka yi mani jinkiri zuwa wani É—an lokaci makusanci da na yi sadaka kuma in zamo cikin masu kyautatawa”(Qur’an 63:10).
Waɗannan ɗiyan waƙa suna yin gargaɗi da tsoratarwa ga wanda ba ya bayar da sadaka, kuma ga wanda ke da imani
suna iya razana zuciyarsa ya bayar da sadaka ko da daga farko bai yi nufin
bayarwa ba, saboda tunatar da shi da aka yi da Æ™umshiyar baitocin. Wa’azi ba tsoratrwa kawai yake yi ba, yana kuma albishir
ga mai kyautata aiki, ana samun irin haka a cikin waƙoƙin mabarata. Misali:
Jagora: Lansika –
lansika.
Amshi: Kulle.
Jagora: Mata
dangin Fatsima.
Amshi: Kulle.
Jagora: Ku taru ku
ba mu na Annabi.
Amshi: Kulle.
Jagora: Kowab ba
mu na Annabi.
Amshi: Kulle.
Jagora: Allah zai
saka ma shi.
Amshi: Kulle.
Jagora: A ba shi ruwan Alkausara.
Amshi: Kulle.
(Lansika)
Wannan waƙa da ta gabata saɓanin
wadda ta rigaye ta ce mai nuna mummunan sakamako ga marowaci ranar Lahira. Ita
wannan kyakkyawan sakamakon da ke jiran mai bayar da sadaka ne a ranar Lahira
take bayani. Wannan waƙa Almajirai ne
suka fi amfani da ita, su kuwa almajirai a cikin gidaje suka fi yin bara domin
samun abinci. Wannan shi ya sa waƙar ta fi zance
da mata, kasancewarsu uwayen gida.
Haka ma a cikin waƙoƙin da ake bara da su masu ɗauke da gargaɗi da tsoratarwa akwai rubutattu masu nuna gudun duniya domin saka zuciyar mai sauraro ta yi laƙyas, har a wannan lokacin ya ji son duniya da ƙawace-ƙawacenta sun fice daga ransa, ya ji bayar da sadaka daga abin da yake da shi shi ne mafi alfanu. Ga misali:
9. In an swance ran mutum ya ko zama
gawa,
Ba shi batun É—iya da mata balle barwa,
An kai shi can
cikin ƙabri sai kewa,
Ka san tattalin
gidan duniya sai wawa,
Har ranar da anka
kammai bai shiryo ba.
(Liman Alu Isa: Na ƙare lawwali)
Wannan
baiti da ke sama wa’azi yake yi ga mai sauraron waÆ™ar. Baitin na nuna da zarar rai ya fice daga jikin mutum komai ya Æ™are masa. Duk wani abu da yake da shi na ‘ya’ya ko masoya
ko dukiya ya zama aikin banza domin ba ya amfaninsa da komai. Mawallafin na ƙoƙarin nuna
damuwa da duniya da tattalinta aikin banza ne, domin komai daÉ—ewa sai an bar ta kuma ba za a je
da komai ba face aikin ƙwarai da mutum
ya yi, wanda sadaka na ciki. Sauraen wannan baiti na rage ma mutum dogon guri
har ya iya É—iba
daga wani abu nasa ya bayar sadaka. Wato wa’azi wanda shi ne ya Æ™unshi gargaÉ—i da bushara wanda saurarensa ke iya tausasa zuciyar mutum Æ™unshe yake da yawa acikin waÆ™oÆ™in da mabarata ke amfani da su wajen bara da zimmar shawo
kan masu saurare su ba da sadaka.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.