Ticker

6/recent/ticker-posts

4.6 Waƙoƙin Bukin Haihuwa (Suna) - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 118)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.6 Waƙoƙin Bukin Haihuwa (Suna)

Bayan bukin aure, akwai waƙoƙin da akan rera a gidajen bukin suna. Haihuwa aba ce ta farin ciki da ake yin biki dominta. Kusan burin kowaɗanne ma’aurata shi ne su ga ƙwansu. Auren da ya jima ba tare da an haihu ba, na jawo cece-kuce a tsakanin al’umma. Wani lokaci har abin ya kai ga zunɗe da nuna har ma da habaici da ba’a. Gusau, (2012) ya bayyana bukin haihuwa da cewa:

Al’adun bikin haihuwa ko zanen suna al’adu ne, da Hausawa ke gudanarwa a lokacin da mace ta haihu, har zuwa ranar da aka raɗa wa abin da aka haifa suna (Gusau, 2012: 36).

Ranar da mace ta haihu, akwai al’adu daban-daban da ake aiwatarwa, har dai ta kai ga ranar sanya wa jariri suna. Irin waɗannan al’adun bayan haihuwa sun haɗa da: Lugude, da guɗa da shan magani da karɓar biƙi, da wankan biƙi da kuma barkar haihuwa da makamantansu. A ranar suna ne ake yin asalin bikin haihuwa. Tun safe akan raba goro a masallaci, sannan a sanar da sunan da aka raɗa wa jariri, tare da yin addu’ar Allah Ya raya.

A cikin gida kuwa, mata za su fara girke-girke iri-iri. Maƙwabta da ‘yan uwa na kusa da na nesa za su riƙa tuɗaɗowa zuwa gidan domin wunin suna. A nan za a ci a sha. Yara mata kuwa za su kama raye-raye da waƙe-waƙen wasanninsu na yara. Wasu lokuta har manyan mata ma na rera waƙoƙi daban-daban, duk dai saboda nuna farin ciki da samar da annashuwa. An ɗauko biyu daga cikin misalan waƙoƙin bukin suna daga aikin Ibrahim (Mrs.) (2002: 92-93). Ga waƙoƙin kamar haka:

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments