Ticker

6/recent/ticker-posts

4.6.1 Waƙar Hafsatu - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 119)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

4.6.1 Waƙar Hafsatu 

Wannan waƙa ana rera ta kamar haka:

Hafsaty Baɗɗo ‘yar mama,

Hafsatu Baɗɗo ‘yar Sarki.

Hassi Baturiyar mata.

Wadda maza ka lallashi.

Har yau ba su ba ta kashi ba.

Sai dai ba ta kuɗɗinsu.

Da alama wannan waƙa an rera ta ne a lokacin sunan ɗiyar da aka raɗa wa suna Hafsatu. Idan haka ne kuwa, dole ne a samu sauye-sauye cikin waƙar daga wuri zuwa wuri, musamman ta fuskar sunan da za a riƙa ambato ciki. Yayin da aka nazarci waƙar, za a tarar tana da zubi da tsari na waƙoƙin reno. Domin kuwa ana koɗa wannan ɗiya (Hafsatu) da kalamai irin su boɗɗo da ‘yar sarki da kuma ‘yar gata.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments