Ticker

6/recent/ticker-posts

4.3.1 Samuwar Waƙoƙin Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.3.1 Samuwar Waƙoƙin Bara

Bara roƙo ne, saboda haka dole a sami wasu dabaru da za a yi amfani da su lokacin aiwatar da shi domin jawo hankalin mutane su bayar da sadaka. Daga cikin hanyoyin akwai shirya waƙoƙi masu ɗauke da fatar alheri domin daɗaɗa zuciyar waɗanda ake rera wa su a zaburar da su wajen bayar da taimako, wato sadaka. Daga cikin waƙoƙin akwai na baka akwai kuma rubutattu. Na baka suna da dogon tarihi da ma ba za a iya ƙayyade lokacin fara su ba[1]. Su kuwa rubutattun waƙoƙin Hausa sun zo daga baya ne sakamakon shigowar addinin Musulunci wanda ya kawo fasahar iya karatu da rubutu a ƙasar ta Hausa[2].

Ga dukan alama, waƙoƙin baka na bara waɗanda Almajirai ke amfani da su tsara masu su ake ko kuma ƙila su tsara da kansu, domin da ma su waƙoƙin yara tsara masu ake yi ko ƙila su tsara wa kansu[3]. Wato ke nan waƙoƙin bara na baka su ne waƙoƙin bara na farko da aka fara samu a ƙasar Hausa, kuma su ne aka fara samu a ƙasar Hausa. Su kuwa rubutattun waƙoƙin sun samu ne a ƙasar Hausa bayan Hausawa sun iya karatu da rubutu kamar yadda aka bayyana can baya, wanda ake hasashen faruwar haka a ƙarni na sha huɗu (Ƙ14).



[1]  Sai dai a ce an fara su tun a lokacin da Hausawa suka fara zaman tare a waje ɗaya, lokacin da ba a iya ƙayyade shi ta amfani da kwanan wata ko shekara, domin tun wancan lokacin ne taimakekeniya da neman taimako yake a tsakanin Hausawa.

[2]  Ana hasashen shigowars Musulunci a ƙasar Hausa cikin ƙarni na 14 (Yahaya,1988).

[3]  A duba Dunfawa 2002.


Post a Comment

0 Comments