Ticker

6/recent/ticker-posts

4.4 Bunƙasar Waƙoƙin Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.4 Bunƙasar Waƙoƙin Bara

Bayan samuwar waƙoƙin sai suka ci gaba da yaɗuwa daga wannan waje zuwa wancan gwargwadon yaɗuwar mabarata a cikin ƙasar. Ƙaruwar yawan mabarata shi ke ƙara yawan waƙoƙin, domin masu fasaha daga ciki na iya ƙirƙirar waƙa su ƙara cikin waƙoƙin na bara. Misali, mabarata manya kamar Gardawa da makafi da wasu daga cikin mabarata suna amfani da wasu waƙoƙi na addini kamar Ishriniya ko Alburda ko duk wata waƙa ta yabon Annabi da aka wallafa cikin Larabci su yi bara da su. Haka ma suna amfani da wadda aka wallafa a cikin Hausa ake yabon Annabi ko ake wa’azi ko ilmantar da jama’a wani sha’anin addini ko ake addu’a su, su riƙa yin bara da su.

Zuwan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo shi ya ƙara haɓaka rubutattun waƙoƙin Hausa a kan jigogin dabam-daban da suka jiɓinci addini. Wannan ya ƙara wa mabarata yawan waƙoƙin da suke aro su yi bara da su. Haka abin ya ci gaba har zuwa yau, wato da duk wani malami ya rubuta waƙar bege ko ta wa’azi ko ma ta ilmantarwa, sai mabarata su are su yafe su mayar da ita abin yin bara.

Bayan waɗannan rubutattu waƙoƙin da ake samun ƙaruwarsu kullun, sai kuma mabarata suka fara ƙirƙiro wata hanya ta yin bara a cikin taro. A irin wannan baran sai mabarata su riƙa ƙirƙira waƙa suna ƙari, wani na bayarwa saura na amshi. A haka waƙoƙin bara suka bunƙasa kuma suke ci gaba da bunƙasar har zuwa wannan lokaci.


Post a Comment

0 Comments