Ticker

6/recent/ticker-posts

4.2 Ma’anar Waƙar Bara

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

4.2 Ma’anar Waƙar Bara

Waƙar bara ita ce waƙar da mabaraci/mabarata ke amfani da ita yayin da yake/suke aiwatar da baransa/su. An kira su waƙoƙin bara domin amfani da ake yi da su wajen aiwatar da bara. Waƙoƙin da ake bara da su sukan kasance na baka da rubutattu. Na bakan su ne waɗanda tun a wajen samar da su an ƙudurci tsara su ne saboda a yi bara da su, mafi yawa domin Almajirai. Akan kuma sami wasu waɗanda ba domin almajirai ba ne sai dai domin sauran mabarata manya, amma haka bai hana su ma wasu Almajirai su yi amfani da su wajen bara ba. Daga cikin irin waɗannan waƙoƙin da mafi yawa manya suka fi amfani da su, akwai rubutattun waƙoƙi. Ke nan a nan waƙar bara ita ce waƙar da mabarata ke amfani da ita wajen aiwatar da bara ko da kuwa wanda ya wallafa waƙar ba domin a yi bara ya wallafa ta ba, tunda dai su mabarata sun mayar da ita abar yin bara ga jama’a, to an ɗauki irin waɗannan waƙoƙin a matsayin waƙoƙin bara. Waƙoƙin da ake amfani da su wajen bara suna da yawa kuma iri-iri ne, akwai waɗanda suka keɓanta da Almajirai kamar waƙar “Kwalho, Inna Kwalho” da “Lantika” da “A tumbulo” da sauransu. Akwai kuma waɗanda kowane mabaraci ke iya amfani da su, amma manya sun fi yawaita amfani da su, kamar rubutattun waƙoƙin wa’azi irin “Gangar Wa’azu” da na madahu kamar “Imfiraji” da sauran irinsu da aka wallafa domin addu’a ko ilmantarwa, da kuma wasu na baka da ake rera su cikin taro irin su “Madogara Annabi” da “Jirgi Ɗan Amina” da wasunsu.


Post a Comment

0 Comments