Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.1.2 Ma’anar Waƙa Daga Wasu Al’ummomi
Haka kuma
masana lamarin waƙa da ba Hausawa
ba sun bayar da ma’anar waƙa rubutatta
kamar haka:
Wordsworth,
cewa ya yi:
“Spontenious overflow of powerful feelings” (Google: Poetry.com)
Fassara:
“ Ra’ayi wanda ke rufe mutum kai tsaye”
A wannan ma’anar marubucin ya nuna cewa ita waƙa tamkar wani Ra’ayi wanda ke rufe mutum kai tsaye, wato dai irin tunanin da kan shigi mutum a lokacin da yake tsara waƙa tunani ne wanda kan mammaye zuciyarsa.
Dylan Thomas ya bayyana ra’ayinsa kamar haka:
“Poetry is what
makes me laugh or cry or yawn, what makes my toenails twinkle what makes me
want to do this or that or nothing” (Google: Poetry.com)
Fassara:
“Waƙe[1] abu ne wanda ke sani dariya, kuka ko kuma hamma, abinda ke sa farce ƙafafu na motsi ko abinda ke sa ni yin wannan ko wancan ko kuma in ƙi yin komai”
Shi Dylon yana ganin waƙa ne a matsayin wani abu mai haifar da faruwar wani abu wanda mutum kan yi ko bai shirya ba, yana cewa: waƙe abu ne wanda ke sani dariya, kuka ko kuma hamma, abinda ke sa farcen ƙafafuna motsi ko abinda ke sa ni yin wannan ko wancan ko kuma in ƙi yin komai”. Wannan ya nuna cewa waƙa na iya sa mutum yin dariya ko kuka da dai sauran abubuwan da gangar jiki ke yi ba tare da mai jikin ya shirya yinsa ba.
Marriam Webster inc. 2014 an kawo cewa:
“Writing that formulats a concentrated imaginative awareness of experience in language, chosen and arrenged to create a specific emotional response through meaning, sound and rhythm” (Google: Poetry.com)
Fassara:
“Rubutu ne wanda ke tattaro ƙololuwar zurfin tunani a kan al’amuran rayuwa a cikin harshe, wannan tunani wanda aka zaɓa ne kuma aka tsara shi ta hanyar da zai iya haifar da wata halayyar kiɗimewa ta hanyar ma’ana ko amo da kuma karin sauti”.
Wannan ma’anar cewa take yi rubutun waƙa rubutu ne wanda ke tattaro ƙololuwar zurfin tunani a kan al’amuran rayuwa a cikin harshe, wannan tunani wanda aka zaɓa ne kuma aka tsara shi ta hanyar da zai iya haifar da wata halayyar kiɗimewa[2] ta hanyar ma’ana ko amo da kuma rauji.
The new Grove
Dictionary of music and Musicians an bayyana ma’anar waƙar baka kamar haka:
“A piece of music for voice or voices whether accompanied or unaccompanied or the act or art of singing” (Google: Song.com)
Fassara:
“Wani guntun kiɗa don murya ko muryoyi ko tare da abinkiɗa ko ba tare da abin kiɗawa ba, ko kuma fasahar waƙa”
Wannan ƙamusun ya dubi waƙa a matsayin wani guntun kiɗa don murya ko muryoyi ko tare da abinkiɗa ko ba tare da abin kiɗawa ba, ko kuma fasahar waƙa. a nan marubucin yana nufin wasu muryoyi da akan jera su wani lokaci a haɗa da kiɗa wani lokaci kuma ko ba a haɗa da kiɗan ba su ake kira waƙa.
The
Harvard Dictionary yana cewa:,
“Mordern song is characterised by expressing personal feelings that encompass the whole range of human emotion[3].
Fassara:
“A zahiri ko
wani sashe na kiɗa ya
adabin waƙa ba tare da ambaton halayyar waƙar al’ummar ba. Waƙar zamani tana ƙunshe da bayyanara’ayi na kai wanda ya ƙunshi dukkan halayyar kiɗimewar Ɗan’adam”.
Shi kuma ƙamusun Harvard ganin yake waƙar zamani tana ƙunshe da bayyana ra’ayi na kai wanda ya ƙunshi dukkan halayyar kiɗimewar Ɗan’adam. Wato dai waƙa kan iya canza halayyar rayuwar mutane domin hikimomin da ke tattare a cikinta.
Glenco
(2000) yana cewa:
“By making us stop for a moment, poetry gives us an oppotunity to think about ourselves as human beings – and what we mean to each other”[4]
Fassara:
“Sawar da take yi mu ɗan dakata na ɗan lokaci, waƙe na bamu damar tunanin kawunanmu a matsayin mutane da kuma yadda muke ga yan’uwanmu”.
Wannan masanin ya bayyana waƙa da cewa tana sa duk lokacin da mutum ya ji ta ya ɗan dakata don ya saurare ta ya kuma fahimce ta. wato irin sawar da take yi mu ɗan dakata na ɗan lokaci, waƙe na bamu damar tunanin kawunanmu a matsayin mutane da kuma yadda muke ga yan’uwanmu.
La’akari da waɗannan ma’anonin da masana da
manazarta suka samar muna iya cewa: Waƙa wata
magana ce da ake zaɓo
kalmomi a tsara su cikin hikima bisa wasu ƙa’idoji na musamman domin daɗaɗa zukatan masu
saurare da kuma isar da wani saƙo gare su, a
kuma yi amfani da wata murya ta musamman domin rerawa wadda ke fizgar hankalin
jama’a ya zuwa bin diddigin[5] ma’anoni da manufofin da
ke cikin kalmomin.
[1] Masana sun bambanta waƙe da waƙa, suna ganin
waƙe
a matsayin rubutacciyar waƙa ya addini. Ita kuma waƙa ta shafi
kowace irin waƙa.
[2] Halayyar kiɗimewar a nan tana nufin ta mantawa da komai in banda
wannan rubutun waƙar.
[3] An samo wannan daga Google: Song. Com.
[4] A nemo wannan
ta hanyar Google: Poetry.com.
[5] Wasu suna cewa diddiƙin, ma’ana dai bin abu sau da ƙafa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.