Ticker

6/recent/ticker-posts

3.2.1 Masu Mulki

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

3.2.1 Masu Mulki

Masu mulki a nan na nufin masu shugabancin al’umma. Daɗaɗɗiyar al’adar Bahaushe ce a sami shugaba ga duk wata ƙungiyar jama’a da ta wanzu a cikin al’umma, kamar yadda Alhassan (1982) ke cewa:

Idan gari ko tunga ko ƙauye ya kafu sai a sa shugaba wato Sarki ko Hakimi ko Mai unguwa da sauransu. Alhasan (1982:54).

Akwai irnin wannan shugabanci daban-daban a cikin al’umma. Misali, akwai sarakuna da uwayen ƙasa da hakimai da masu unguwanni. Haka kuma, a zamanance akwai manyan ma’aikatan gwamnati da kuma shugabannin siyasa da suke mulkin al’umma. Irin waɗannan shugabanni mafi yawa sukan kasance masu wadata. Haka ma ko bayan wadatar da suke da ita, suna da hannu ga wasu abubuwa na tallafi da kan shigo zuwa ga mabuƙata ta wasu hanyoyi kamar tallafin gwamnati ko na wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin ƙasa da na waje.

Mabarata na yi wa waɗannan shugabanni da aka ambata bara, saboda wadatar da suke da ita da kuma hannu da suke da shi a kan abin da ke shigo ma tallakawa daga wasu kafafe. Koyaushe gidajensu da ofisoshinsu maƙil suke da mabarata iri-iri domin neman taimako daga wajensu. Haka kuma, wannan ba zai hana a tare su ga hanya a yi masu bara a nemi sadaka daga hannunsu ba, saboda ko a waje suka fita suna cikin alama mai nuna mawadata ne, wanda kan ƙara jawo hankalin mabaraci zuwa gare su.


Post a Comment

0 Comments