Ticker

6/recent/ticker-posts

2.5.6 Ɗan Yaro Fari Tas - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 95)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.5.6 Ɗan Yaro Fari Tas

Ɗan yaro fari tas,

Kamar daga Ingila ya taso.

 

Ɗan hanci surat rat,

Kamar daga maina ya karyo.

2.5 Kammalwa

Wannan babi ya bi da mu cikin wasu daga cikin misalan waƙoƙin gargajiya da suka shafi wasanni. An kawo misalai daga wasannin dandali na yara maza da mata, da kuma wasannin tashe na yara maza da mata. Yana da kyau a fito da waɗannan waƙoƙi fili sannan a daddage su filla-filla domin bankaɗo falsafar da kowacce waƙa ta ƙunsa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments