Ticker

6/recent/ticker-posts

2.2.4 Ina Da Cikin Ɗan Fari - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 76)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.2.4 Ina Da Cikin Ɗan Fari

Bayarwa: Ina da cikin ɗan fari,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata ɗaya ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata biyu ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata uku ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata huɗu ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata biyar ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata shida ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata bakwai ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Wata takwas ba wasa ba,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Sai a ran na goma na goma,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na haifi ɗana Mamman,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na je gidanmu da wanka,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na tarad da baba a zaure,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Yana cikin cinikinsa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Yana cinikin goronsa,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce mu ga jikan namu,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Jikan namu har ya girma?

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya tsunkule shi a hanci,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Na ce uhm! Ba komai,

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce ku ji ɗiya ba kunya?

Amshi: To!

 

Bayarwa: Ya ce ku ji ɗiya ‘yar banza!

Amshi: To!

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments