Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //04

iv) Rashin Yarda: Wannan ma na daya daga cikin dalilan da suke janwo kishi, lokacin da mace ta tabbatar cewa maigidanda baida zarafin da zai ƙara mata kishiya ba za ta damu ba ko kadan, ko da kuwa a makarantar mata yake koyarwa inda za a sami kyawawan mata, zarata, farare masu iya magana da takwarkwasa, amma da wahala ka ga ta damu. Daga lokacin da shakku suka fara samun mazauna a zuciyarta nan take za ta fara nunawa a fuskarta ko lafazinta ko a ayyukanta.

Sai kuma saƙar zuci: Inda za ta fara cewa "Zai iya samun wace ta fi ni haske" in mai tunani ce sai ka ga ta fara gyara kanta, irin su dilkannan ba tare da ta furta masa ko kalma ba, ba ma za ta zarge shi ba kar a yi na 'yan uwan annabi Yusuf AS da babansu AS. Ba su san kyarkeci na cin mutum ba, amma tunda ya ce yana tsoron kar kyarkeci ya cinye shi, sai suka ce "Ai kyarkecin ya cinye shi" mace mai kishin gaskiya ba za ta yi masa maganar kishiya ba bare shedan ya rada masa a kunne.

Tunda makaranta yake wurin masu ilimi, in ta ga yana sha'awar mai ilimi nan take za ta fara nemansa kan jiki kan ƙarfi. Amma in aka ce babu yarda to dole kishi ya yi ƙarfi a tsakanin masoya ko kuma ma'aurata. Sai ka ga kowa ya fara shakkun cewa wani abu zai iya faruwa. Me ke sa mace ta fara yi wa maigidanta maƙe don jin maganar da yake yi a waya? Duk mai irin wannan dabi'ar gani take ko maigidanta yana neman wata ne, anan rashin yarda ya ratso tsakiya. Duk da cewa halas ne ya ƙara hana shi ba huruminta ba ne.

Wata macen wayarsa za ta dauka kacokan ta fara duba history dinsa ko zavta ga ya buga wa sunan mata, ko kuma wata macen ta bugo masa. Wata da ƙarfin hali ma za ta dauki lambar ta kira in ta ji budurwa ta amsa ta zazzage ta kuma ta ce ta rabu mata da miji. Akwai aurarrakin da suka mutu da dama a kan daukar wayar miji. Wani ko maigidan ya garƙama wa wayarsa kwado sai ta san yadda ake budewa ta kallo wa kanta hawan jini ko ta yanki tikitin da zai kai ta gidansu.

Idan aka sami rashin yarda shi ne za ka ga mace na saka wa a riƙa bibiyar mijinta me yake yi? In tsayuwa ya yi da wata mace sai an zo an gaya mata, wata kan yi abin kunya ma daga baya ta fara neman yadda za ta gyaro. Kar ki taba yarda ki sa maigidanki a gaba kina bibiyarsa da sunan kishi. ko da wasu ne suka kawo miki gulmar sun gan shi wuri kaza da wance, ki nuna musu kin sani, ko da kuwa za ki bibiyi maganar. Domin a lokacin in suka gaya miki sun wuce kenan, wata ma ba za ta sake tunawa ba, sun barki da zullumi sun wuce.

Akwai wace take bin mijin sau da ƙafa, don ganin ina zai je? Da wa zai yi magana? A ƙarshe ta same shi yana magana da ƙanwarsa da suke dan-mace da 'yar namiji. Ta zaci budurwarsa ce ta yi mata zagin fitar arziƙi. Wannan ya sa ya fara nemanta don dai kawai su baƙanta mata rai, a ƙarshe wasa ta zama gaskiya ya auro ta ma gaba daya.

Kuskure ne namiji ya sanya rashin yarda ya sami wurin zama a zuciyarsa, duk da cewa kishin namiji ibada ne domin shari'a ne, amma rashin yardar da zai kai shi ga zargi zai iya wargaza gidansa cikin dan ƙanƙanin lokaci. An yi wani namijin da in matarsa ta fita unguwa ko bai bi ta a baya ba sai ya je inda ta je don bincikawa: Ta zonan? Yaushe? Me ta yi? Daganan ina ta ce za ta? Ba wai ya taba kamata ne da rashin gaskiya ba a'a tsabar rashin amincewa ne da  abin da za ta iya yi.

Wani ko abu matarsa ta je sayowa sai ya bi diddigi don jin wace magana ta yi da mai shagon? Na ji wani malami da yake cewa "In matarka za ta je awo a asibiti ka bi ta kar a yi maka sakiyar da ba ruwa" ba cewa nake kar ka bi ta ba amma ka dauki lamarin sese-sese yadda ba zai gallabe ka ba. Na san mutumin da in matarsa za ta unguwa sai dai ya kama mashina guda biyu ya goya ta a baya, su kuma direbobin su goyo kawunansu. In ya kai ta inda za ta sauka masu mashina su karbi abinsu. Wannan ba rashin yarda da matarsa ne ba shari'a ce amma Allah ya sa mu dace.

Ka tsare matarka iya iyawarka amma kar ka yarda ta ji cewa akwai rashin yarda a tsakaninku, haka ita ma macen. Babu laifi a tsakaninsu su so juna irin yadda kowa zai ji dadin dan uwansa ya amince cewa yana son sa. Ba kuma yadda mutum zai ji cewa zaman ya ishe shi a rabu kawai ba. Ko hotunan mata mace ta ga mijinta da su ta bi a hankali wajen warware matsalarta, mummunan kishi bai taba zama hanyar nuna soyayya ba.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments