MATSALOLIN KISHI
Kusan wannan babin shi ya fi kowanne muni a wannan littafin, domin mummunan kishi na da cutarwa sosan gaske, wanda yakan kai mace cikin matsaloli ita da kanta kafin ma ya shafi wani, yakan jefa ta cin damuwa da zullumi a kowani lokaci, da ma zai bar ta haka to da da sauƙi, amma yakan bi ta cikin gidanta ya ba ta alaƙarta da kowa ba ma maigidan da zai riƙa kallonta a matsayin mai son kai ba hatta 'ya'yanta wani lokaci za su riƙa magana a gefe cewa mama kaza-kaza. Wani sa'in ya kamata a ce da ita za a yi wani abin, ko da ita za a tafi wani wurin, amma dole a boye mata sabida sanin halinta.
Don da a ce
mace mai mummunan kishi ta san matsalolin da cutarta ke haifar mata da ita da
kanta za ta fara neman magani kafin wasu su ba ta shawarar hakan. ko da yake
wasu lokutan takan sani, kuma da kanta ma takan ce "Ni fa mace ce mai
zafin kishi" kuma takan ga wasu matan ba haka suke ba me ya sa ta zama
daban? Da kanta ta ga yadda kishin kan sa ta yi asarar abubuwa da dama, ciki
har da abin da take kishin a dalilinsa
to meye amfanin badi ba rai, misali kwanannan wata ta kusa kashe dan kishiya a ƙarshe
mijin ya kasa haƙurin zama da ita, tana ji tana gani ta bar nata 'ya'yan a hannun
wancan maigaida ya kore ta.
1) KUSAKURAI:
A dalilin abin da mata ke kira kuskure
wata kan yi abin da zai yi ta damunta
har ƙarshen rayuwarta. Don mace mai kishi ba ta girma, ayyukanta na yara ne har
ƙarshen rayuwarta, amfanin girma aiki da hankali ko ilimi, ko tana aiki da su a
wasu abubuwan indai za a dawo maganar kishi an gama. Mai ilimi kan manta da
karatun gefe guda, babbar kuma kan koma daidai da yaranta ta yi duk abin da ta ga dama a gabansu har su yi fatar
da ma ba ta a wurin, tunda hankali bai aiki a wurin ba bare ilimi.
Mai mummunan
kishi ko mafarki take wai mijinta ya yi aure sai ta farka cikin salati, in wata
ƙawarta da kuskure ta shiga gonanta tana iya mantawa da komai ta sauke mata
fushinta gaba daya. Na sha ganin mai batawa da ƙawayenta da suka fi kowa kusa a
kan abin da ba ta ma da tabbas, alabashi
daga baya ta ba da haƙuri ko a zo a yi musu sulhu, wata har abada ba ta yin
nadama kan abin da ta yi, matuƙar yana
da alaƙa da abin da take wa kishi. Tun
muna yara nake ganin ƙawaye na dambe a kan namiji, kuma kishin ne dalili, a ƙarshe
ka taras bai ma san suna yi ba.
Akan sami lokacin
da mace za ta sha kuka a yi ta ba ta baki ta ƙi, don dai kawai ta kai ga cimma
burinta, kuma a shirye take ta yi zage-zage da cin mutunci a gaban kowa da kuma
kowaye, ciki har da mahaifanta bare surukanta, ba ta damu da abin da za a ce a kanta ba matuƙar za ta kai
ga cimma burinta. Wata kuwa zargin mijin za ta yi da wasu ƙarairayi marasa
kan-gado, ko kwanannan da wata ta baro gidan mijin ta ce yana neme-nemen mata
ne, alhali an san shi da kamun kai kuma malami ne ma, ko ta ina ta sami labaran
oho.
Akwai wace in
ta tashi haukan kishinta gani take kowa a kan kuskure yake, ita ce kadai a kan
gaskiya, don haka take daga murya a lokacin da za ta yi magana don kowa ya ji
tunda da shi take, ta riƙa fadin an yi mata kaza-kaza da kaza don an ga ba
wanda zai taimake ta, kullum a ce ita ce ba ta da gaskiya. WaÉ—anda suka so
shiga maganar sukan yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen gano masabbabin rigimar amma
ba sa iyawa, asalin matsalar kishi ne kawai na banza ba a kan abin da take magana ne ba.
Abinda zai ba
ka haushi ko mamaki shi ne wace za ta yi kishi, kuma a zahiri tana cutar da
maigidan ne wai hakan wata alama ce da za ta nuna tsabar ƙaunar da take masa,
har ka ji tana cewa "Ai duk macen da take kishinka wallahi ƙaunarka
take!" A lissafinta duk wace ba ta goyi bayanta a kan abin da take kai ba to munafuka ce, in
budurwa ce to akwai alamar zargi tare da ita, ƙila tana da wata alaƙar
tsakaninta da maigidanta. Kenan mummunan kishi ya zama ma'auni da za a iya auna
ƙaunar mace ga maigidanta.
A duk abubuwan
da mace ke yi ita ba za ta taba sanin cewa tana rushe ginin soyayyarta ne da
mijinta ba, ba za ta san ko 'ya'yanta na yi mata kallon maras gaskiya ne ba
kuma a ƙarshe abin da ba ta so din shi
yake faruwa. I mana, an yi wace ta kwana da wuƙa ita da mijin a hannu kuma sai
da ya yi aurensa. Wata ta je gidan wata yarinya sun sha dambe duk da haka sai
da yarintar ta shigo. Akwai wace ta zagi uban surukinta, maigidan ya sallame ta
kuma ya yi aurensa, nan gaba ba za ta auri wanda bai taba aure ba to ita ya za
a yi kenan ta auri mai mata?
Da haka za ka
ga wata da mijinta malami ne mai kamun kai, tana zuba wa wata zagi wai ta yi
shigar banza, ko ba ta yarda da kwalliyar da take yi ba ai maigidanta na aiki a
wurin in ya ganta fa? Ko ta fara zargin cewa wallahi duk kwalliyar da take yi
don maigidanta take yi, ko ka dauka da wasa a ƙarshe za ka ga ne tabbas da
gaske take yi ba wata alama dake nuna wasa ne, ba kuma za ta saka a zuciyarta
cewa ya kamata ta kwaikwayi abin da take
ganin maigidanta zai yi sha'awa ba.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban
Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.