Ticker

6/recent/ticker-posts

Manjo Janar Mustafa 1

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Sun buga sun bari manjo janar Mustafa,

Masaba ƙarfen tama ba sa ga ƙarshenka ba.

Ƙarfen tama kwangiri gamji ma sha sassabe,

Manjo janar Mustafa ba sa ga ƙarshenka ba.

 

Sunan abin dogaro Allahu Alƙadiri,

Allahu Alƙadiri mai arzikin haƙƙuri,

Mai sarrafar nan da can cikin dawa ko gari,

Mubaya'ata duka ga annabi shugaba.

 

Allah abin ambato a ɓoye ko sarrari,

Ƙaro aminci duka ga sayyidul bashari

Abin yabon baɗini abin yabon zahiri,

Mai son mijin A’isha ba a ga ƙarshensa ba.

 

Rana idan ta fito sheda ta wayar gari,

Da an fa waye gari sai dabdalar ‘yan gari,

Fiton da kome nata ba mai hanawa gari,

Ranar idan ta fito ba a hana a gan ta ba.

 

Zubar ruwan maddari Buwayi Alƙadiri,

Dukkan sha'an lammari yana kasan Ƙadiri,

Komai nisan zamani yana gurin Ƙadiri.

Abin da ya ƙaddara ba a ƙi a gan shi ba.

 

Ga mai dashen kainuwa ta zam cikin bahari,

In kun biye wa bado kwa sha ruwan bahari.

Cin dudduge sa ƙwafa ba ya hanin zikkiri,

Muna biɗar taimako ba gun wanin Rabbu ba.

 

Allah abin dogaro roƙo yake sha'iri,

Ka san nufin zuciya da ƙuddurin sha'iri,

Allah mafarkin da nai sanya ya zam nagari,

Ka san nufin zuciya ba za mu ɓoye ka ba.

 

Ɗoɗe ganin magauta da dukkanin fajiri,

Allah kai masa kasshafi ya tsallake haɗari,

Tarkon haƙon magauta ya zamma ba tasiri,

Da sun nufin za'ida ba za ta kai gunmu ba.

 

Ka san dukan lamarin ɓoyenmu har zahiri,

Kasan ciki har waje da baɗini zahiri,

Babu abu na ɓoye akauni Alƙadiri,

Sani na al'amari ba za mu ja makka ba.

 

Waɗansu sun ɗau kube suna shirin bidiri,

Gamji yawan sassaƙa ba ya hana ka tsiri,

Jumrau mijin Fatima gwarzo abin fahari,

Takubbunan akwasa ba za mu tsorata ba.

 

Wanda ya kama Allah Buwayi Alƙadiri,

Komai ya taso maka gaya wa Alƙadiri,

Muddin hakan za ka yi ka kewaye haɗari

Kwaron gizago ba zai sanya ka tsoratta ba.

 

Yabo nake Mustafa da gwargwadon hankali,

Ba mai fahimtar abin sai ya zamo akili,

Mai gwargwadon hankali da ya zamo adali,

Shi za ya min uzzurin yabonka ba aibi ba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments