Ticker

6/recent/ticker-posts

Janaral Murtala Mazan Jiya

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shimfiɗa

Ga yabo na mazan jiya,

Masu aiki da gaskiya,

Wanda babu ɗigon riya,

Garkuwan Nijeriya,

Ga yabo na mazan jiya

Murtalan Nijeriya.

Janaral namu Murtala,

Allah kyautata kwanciya.

 

Amshi

Shugaban ƙasar Nigeriya janar Murtala shugaban ƙasa,

Allah ya jiƙan Nigeriya da rashin iyaye na gaskiya.

 

Allah Ahadun Allah Samadun,

Wanda anka wa bauta ɗaya.

 

Lam ya lidi Allah Wahidun,

Walam yuladu ƙwalli ɗaya. 

 


Nai riƙo da bautar Majidu,

Ka tsare ni kar na yi bauɗiya-

 

Daraja ta manzo Amadu,

Shugaban halittar duniya.

 

Yau yabon gwanaye ni nake,

Jaruman ƙasar Nijeriya.

 

Na sahun gaba kishin ƙasa,

Ban da masu halin bankiya.

 

Wanda rayuwarsu saddaka,

Suka bai ƙasar Nijeriya.

 

Jiya na kirawo amadu,

Yanzu murtala mai turjiya.

Duka an zubar da jini nasu,

Don tsare mutunci gaskiya.

 

An kisa na gilla kai nasu,

Don tsare ƙasar Nijeriya.

 

Wasu an kashe ahli nasu,

Kwanci tashi za ku ji gaskiya.

 

Za na bayyano su aji-aji,

Ba kamarsu kishin gaskiya.

 

Godiya nake ga Ubangiji,

Da nake yabawa mazan jiya.

 

Godiyar ga na yi aji-aji,

Ga Mamallaki duk duniya.

 

Agaje ni Rabbu da agaji,

Rukunin zalaƙa da dagiya.

 

Kada kan nufe ni da in gaji,

A fagen yabo kan gaskiya.

 

Janar Murtala ɗan Ramatu,

Ɗan Muhammadu sha tambaya.

 

A watan Nuwamba ran takwas,

Aka haifi gagon gaskiya.

 

Shekara ta nantin tati'et,

A milaɗiya lissafiya.

 

Agarin Kano alƙarraya,

Aka haifi gagon duniya.

 

 

A kwaleji yai ilimi nasa,

A Barewa ƙauyen Zariya.

 

Shekara ta nantin fifti nai,

Yai Barewa lardin Zariya.

 

Daga nan ya taffi akadami,

Militiri can Burtaniya.

 

Ya fito muƙamin laftanal,

Nantin sisti wan ba tankiya.

 

Shekara nantin sisti tu,

Majalisar ɗinkin duniya.

 

Ta iza shi Kongo da runduna,

Don a sada zamman lafiya.

 

Shekara ta nantin sisti fo,

Aka ba shi manjo ba riya.

 

Janaral a sanda ya je Iko,

Minista tsaron Nijeriya.

 

Shekara ta nantin sisti sis,

A garin Iko tai mamaya.

 

Lokacin da anka yi ku ƙasa,

Na kisan mazaje naj jiya.

 

Lokacin Agunyi Ironsi ne,

Ya ɗare gadon Nijeriya.

 

Laftanal kanal aka mai da shi,

Shekarar kisan su mazan jiya.

 

 

Yai rawar gani a Biafara,

Masu raba kan Nijeriya.

 

Zamaninsu dum Odumegu ne,

Ojuku ya zo da hatsaniya.

 

Suka shirya tawaye ƙasa,

Don a raba kan Nijeriya.

 

Shugaba janar ɗan Ramatu,

Shi ya tarwatsa su da nakiya.

 

Lokaci na tawayen ƙasa,

Masu son rabon Nijeriya.

 

Sun yi gangami na shirin tsiya,

'Yan Biyafara gonar ƙaya.

 

Odumegu babban jarumi,

Aleɗanda maidubu a jiya.

 

Kun ji rundunar gonar ƙaya,

Da ta so rabon Nijeriya.

 

Rundunar mayaƙa na ƙasa,

Ɓangaren tsaron Nijeriya.

 

Runduna ta farko an ka ba,

Mamman Shuwa mai rawaya.

 

Runduna ta biyu ko janaral

Ɗan Ramatu rumbun ƙaya.

 

Runduna ta ukku Ade Kulle,

Benjamin Adekulle tsiya.

 

 

Yan Biafara sun kai hari,

A garin Iko tun safiya.

 

Suka kai hari da boma-bomai,

Zafi-zafi tun da sakaliya.

 

Daga nan uwa Nijeriya,

Sai ta gane yaƙin kwai tsiya.

 

Mamman Shuwa shi ya kakkaɓo,

Jirgin Ikoja da safiya.

 

Shekara ta nineting siɗty-seɓen,

Goma ga watan Yuli jiya.

 

Aka fara yaƙin cikin gida,

'Yan Biafara Nijeriya.

 

Daga juyin mulki na uku,

Lokacin yana burgediya.

 

An riga da an masa jannaral,

Mai anini huɗɗu mazan jiya.

 

Masu juya mulki kulliya,

Sun ka ba shi kan Nijeriya.

 

Gantamau mazajen duniya,

Sai ya fara shimfiɗa gaskiya.

 

Nan da nan ya shimfiɗa gaskiya,

Daidaita sahun Nijeriya.

 

Haka rukuni na ma'aikata,

Ya zamo suna bisa tarbiya.

 

 

Bisa lokaci bisa ƙa'ida,

Babu maguɗi hauragiya.

 

Jami'an tsaro babu rashawa,

Ya aza su turbar gaskiya.

 

Lokacin janar ɗan Ramatu,

Ɗan Muhammadu mai gaskiya.

 

Babu shugaba mai ƙwarjini,

Da ake wa tsoron da gaskiya.

 

Kafatanta kaf!! Nijeriya,

Da Afurka duk Ifirikiyya.

 

Duk da ƙwarjininsa Muhammadu,

Ba ya shi adala da gaskiya.

 

Na tuno da dakta Ubarogi,

Da ya shirya zancen ƙarya.

 

A cikin jaridar nan Spark,

Afurkan Spark ƙullalliya.

 

Ƙazafin da ya yi wa Murtala,

Ya azurta kansa da dukiya.

 

Ya kwashi kuɗin Nijeriya,

Kan ya zam uban Nijeriya.

 

Dubu mattsayin shugaban ƙasa,

Har dai janaral mai tutiya.

 

Da rashi na ɗar ko fargaba,

Dukkanin ƙasashen duniya.

 

 

Sai ya kai shi ƙara shari’a,

Don ya nemi haƙƙin gaskiya.

 

Shara'ar da bai riske ta ba,

Ya riga mu darul afiya.

 

A cikin mujallar nan ta Funch,

Abiola gagon duniya.

 

Ya yi tambihi kan shugaba,

Murtalan ƙasar Nijeriya.

 

Huɗu ga watan mayu taf fito,

Da yabon gwanin Nijeriya.

 

Mko ya ce janar Murtala,

Ya riƙe amanar gaskiya.

 

Ya mutu ya bar ban dubiya,

Ba shi babu garken saniya.

 

Ba gida guda babu gonaki,

Babu alatun duka dukiya.

 

An ka ce da naira tai bakwai,

A cikin asusun bankiya.

 

Kwabo ashirin da biyu ya ce,

Ku ji shugaban Nijeriya.

 

Matsayin adalar gaskiya,

Murtala mazajen duniya.

 

Shi kaɗai da mai tuƙi nasa,

Babu fargaba ba tutiya.

 

 

Ba shi jera gwanon tafiya,

Ba shi kunna sautin jiniya.

 

Haka zai isa har ofishi,

Kun ji shugaba Nijeriya.

 

Ko ganin gida janaral ya zo,

Daga Ikko jigon nahiya.

 

Shi kaɗai da mai tuƙi nasa,

Babu jera gwanon tutiya.

 

Tun daga Ikko birnin Kano,

Ya taho fa babu makaraya.

 

Gwarzon namiji zakkar maza,

Ba kamarsa wannan nahiya.

 

Shi ya tsara canjin helkwata,

Da Abuja birnin tariya.

 

Ya tsiro jihohi har bakwai,

Da batun siyasar gaskiya.

 

Shekara ta nantin sabinti ne,

Za ya bai wa demokaraɗiya.

 

Ƙudurin ga bai riske shi ba,

Olusegu shi ne ya biya.

 

Nouth west a Sokoto ya cire,

Niger state ba tankiya.

 

Nouth east a Borno ko ya cire,

Gongola Bauchi mazan jiya.

 

 

Ya cire Platour cikin Benin,

Shugaban ƙasar Nijeriya.

 

Ogun state da Imo state,

Ondo state ba tankiya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments