Ticker

6/recent/ticker-posts

Amina

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Rabbi kai ni gidansu Amina in sha ruwa,

Aminar Mama,     

Rabbi kai ni gidansu Amina in sha ruwa,

Ruwa ɗan randa.

 

Saboda zumunci sai da gamon jini,

Baba ba ni in ba ka sai da farin jini,

Shimfiɗar fuska sai dai haɗuwar jini,

Shi adashen kyauta sai da farin jini.

 

Duniya mai yayi daina ƙuna-ƙuni,

Yau da mu taka juyi gobe gidan wani,

Godiya mukke Allah da farin jini,

Ba mu yin katsalandan kan sha’anin wani.

 

Takwara na taso dan na rabe aya,

Takwara ki rabe tsakuwa tsakin haya,

Ya ɗiyan Hausawa sun gaza taciya,

Sun gaza da rabe tsakuwa tsakin aya.

 

Alfijir mai kau da duhu na shigar dare,

Da ruwa da wuta ba sa zamani tare,

Yau ga ni a ɓarina na ruwan dare,

Kafin a fahimta ai tsayuwar dare.

 

Kan batu na zumunci an yi karan tsaye,

A bayanin ƙauna an yi fashin tsaye,

Ƙauna da zumunci an masu gauraye,

An haɗa su da soyayya a karan tsaye.

 

Lamarin soyayya akwai rabuwa ciki,

Lamarin ƙauna ko ba rabuwa ciki,

Ƙauna da zumunci sani da ni ciki,

Harƙar rabuwa ku cire ni in bar ciki.

 

Ɗan uwa na haƙiƙa nake a gunku ni,

Ɗan uwa na shaƙiƙi nake a gunku ni,

Sahibin da alaƙa ba ku rabo da ni,

Ni da ku fa alaƙa ba ta da ƙa’ida.

 

Rabbi kai ni gidansu Amina in kwana can,

Rabbi kai ni gidansu Amina in saura can,

A gidan su Farida Amina in ƙoshi can,

Mui raha da zumunta mui yo dariya.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments