Amshi
Yau gareka gobe waninka ba a kanka aka tsira ba,
Yau gudun hijira muke yi gobe an tashi alkiyama.
Shimfiɗa
Rayukanmu a yau da gobe sun zamo jari na waɗansu,
Muttuwarmu a yau da gobe ta zamo noma na waɗansu,
Yau yawanmu a yau da gobe ya zamo nema na waɗansu,
Kurri'unmu a yau da gobe sun zamo mulki na waɗansu,
Yau hakinmu na yau da gobe ya zamo gado na waɗansu,
Ba makwanci zama mu huta don muna goyo na waɗansu,
Babu ‘yanci mu a garemu babu zaɓi kawai mu bi su.
Za a wayi gari a gobe alkiyama za mu mu kwana
Marabar tallaka da bawa ni ka so yau a warwarewa,
Yaushe ne yaudara a kanmu yaushe ne za ta warwarewa?
Yaushe ne za mu kauce ƙunci sasarin nan ya warwarewa?
Yaushe ne za mu sami dama tarnaƙin nan ya zam kwaɓewa?
Yaushe ne za mu sami 'yanci wai adala ta zagayawa?
Yaushe ne za mu daina kuka don hawaye su bar zubowa?
Yaushe wai bugu na zukata za su bar bubbuga dakawa?
Yaushe ne za mu sami 'yanci da mukan ji ana sanarwa?
Yaushe za mu ɗanɗani romo na adala da kan faɗowa?
Yaushe ne za mu sami barci da saleba tana fitowa?
Yaushe ne za a daina dukan talaka a hana shi kuka?
Yaushe ne za mu gane doka na gare ni ta na gare ka?
Yaushe ne za a sanya doka sama da ƙasa a bi doka?
Yaushe ne masu yin hukunci za su zartar ƙasanta doka?
Yaushe ne jami'an tsaronmu za su bar warwara da tufka?
Yaushe ne yaudarar talakka za ta sam ƙarshe gudana?
Yaushe ne yaudarar siyasa za ta zo ƙarshe a daina?
Yaushe ne talakan ƙasata za ya san kansa ganina?
Yaushe ne za a juya halin baragurbi ya daina ɓarna?
Yaushe juyin juya hali na nagarta zai gudana?
Yaushe ne za mu sam salama da sa'ida ko 'yan uwana?
Yaushe ne za mu sam sawaba da sa'ada ko 'yan uwana?
Yaushe ne dangi zukata za su sam sanyin lumana?
Yaushe ne wai yaushe ne wai yaushe ne ranar nufina?
Yaushe ne ranar tsayawa ta hawayen da ke gudana?
Yan uwanmu na nahiyarmu sun zamo 'yan gudu a ɓuya,
An rugurguza nahiyarmu wacce tuntuni ke a baya,
An kisan gilla a gare mu ga marayu da ba gidaya,
Tattalin arzikinmu babu ba sukuni na kassa kaya,
Tallafi 'yan gudun hijira yau da shi wasu ke abaya.
Haƙuri dai ai haƙuri dai haƙuri dai Nijeriyawa,
Dandalin nasara yana nan kar ku sare Nijeriyawa,
Ran da aski ya zo a goshi alami ne na ƙarƙarewa,
Rahama na biye daga tsauri wata ran za mu sha alawa,
'Yan gudun hijira riƙe su 'yan uwa na jini riƙewa.
Garuruwanmu a yau kufayi ungulaye kaɗai ka jewa,
Kasuwanninmu yau kusheyi karnuka ne kaɗai ka jewa,
Ga ɗiyanninmu nan marayu babu ilmin zamantakewa,
Mataikunmu kau zawarawa ba wadata da mai kulawa.
Duk wadata ta mawadata na ƙasarmu ba su ganowa.
Dubi ‘ya’yanmu nan marayu ba su san me aka nufa ba,
‘Yan ƙanana 'yan ba ni babu 'yan dagwaigwai da ba kula ba,
Ba tufafi babu abinci ba mahalli na kwanciya ba,
Ga ƙasussan haƙurƙuransu ba su zarci ƙididdiga ba,
Mu muna nan muna ta barci sai ka ce ba bani Adam ba.
War against terrorist muke yi masu sanho da masu adda,
Za a kau da dabar ta'adda 'yan kisan kai da al'amuda,
Masu ta da ƙaya ta baya yau gareku nake ƙasida,
Ittakillaha aina kunta mafitar masu son sa'ida,
Bindiga gariyo da sanda tattara su mu sam sa'ida.
Ga gamayyar bishe ta'adda sai da jinƙai ake isarwa,
Kar mu bar ‘ya’yanmu marayu a aƙubar rashin nutsuwa,
Da saraku da ma'azurta da mutanen garinmu kowa,
Mu kiyaye bara ta yara don da su ne ake fakewa,
In ba sui ilimi ba yara babu mai kwanciya a inuwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.