Ticker

6/recent/ticker-posts

Hangen Dala

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Shurum-shurum ba ci ne ba,

Hangen Dala ba shiga birni ne ba.

 

Allah haɗa mu da alkhairi,

Ka sa idanun mu gano mana alkhairi.

 

Allah haɗa mu da alkhairi,

Ka sa kunnuwan mu ji mana alkhairi.

 

Ka sa mu auren alkhairi,

Mui gamo katar Allah Jabbari.

 

Muna biɗar kai mana tsarri,

Kar san zuciya ya jefa mu a sharri.

 

Fitintinu sun dame ni,

Ga tuntuni kawai sun aure ni.

 

Ɓacin rai ya kama ni,

Ya sauya min kama har ma launi.

 

Zufar gari ta dame ni,

Rana zafi inuwa na ƙuni.

 

Tunani ya ziyarce ni,

Sai kallon ƙuda kamar an jefe ni.

 

Ga shi annai mini guɗa,

Ga sheɗan yana ta busan algaita.

 

Jama’a na gag gaishe ni,

Abin da duk na ce a yi ba mai mita.

 

Komai na sa ya karɓe ni,

Ya bi sahu na masu yayi ba shufta.

 

A hankali a ka rufzani,

In zama ɗan takara dan fifita.

 

Daga ran da na sa ɗan ba,

Ba hutu cikin gida koko garka.

 

Na jimri jele ga yunwa,

Faɗa nan da can ina halin barka.

 

Babu hutu a gare ni,

Ko barci nake furut sai in farka.

 

Buri na kawai in gan ni,

Na yi ɗare-ɗare a mulki san barka.

 

A ɓangare na iyalaina,

Ba ni da lokacinsu ko da ko daƙiƙa.

 

A ɓangare na iyayena,

Ba daman su gan ni na zama mai harƙa.

 

A ɓangare na abokaina,

Sawu na suke ta bi in da na taka.

 

Babu mai sauyan Magana,

Komai in na ce kawai sa a a harka.

 

Kwaramniya kam an shata,

Na hau da ha maza kuma ha mata.

 

Ina zaton ko zan huta,

La haula wala ƙuwatta na furta.

 

Tururuwa da ake guna,

Dan taya murna a yau na fifita.

 

Na saka takalmin ƙarfe,

Kowa in na so in taka shi in huta.

 

Hidindimu su ka dame ni,

Haƙuƙuwana jama’a sun sarƙe ni.

 

Ulla suna ban umarni,

Ga kuma kabinet fa sun azalzale ni.

 

‘Yan kasuwa da mamulkana,

‘Yan gargajiya sunai mana ɗan nuni.

 

Sannan ƙasar da ta raine mu,

Sun ban umarni da tsari ma’auni.

 

Gaban fa kura a gabana,

A baya in na waiwaya ga sayaki.

 

Gami da dukka abokaina,

Kama zuwa abokanai na gun aiki.

 

Kowa fa ya zare kubansa,

Yana ta aiko min ya sanjen aiki.

 

Ga kwansitushin a gabana,

In bibiye shi ya zamar mini jan aiki.

 

Da na shige ɗaka sai kuka,

Da na tuno Ubangiji Sarkin mulki.

 

Da sharaɗɗoɗin mai mulki,

Da tanadin da anka yi wa mai mulki.

 

Da na fito ay yi kirari,

Dubu jiran guda a ɗoran kan jaki.

 

 

Ƙasa guda ke hannuna,

Umarni ake jira ka ga jan aiki.

 

Motar hawana mai tsada,

Ana ta busa jiniya in da na ratsa.

 

Rigar sakawa mai tsada,

Ana ta nuna ni ta duk in da na ratsa.

 

Abinci ma sai an duba,

Kai har kujera ta zama sai an latsa.

 

Gefe sifeshiyal dakta,

Ba wani wanda za ya nuna ni da yatsa.

 

A zahiri ga jin daɗi,

Na yi acan-acan a rigar alfarma.

 

A baɗini babu sukuni,

Ba ni da walwala ta sisi al’umma.

 

Ko da Ummi Momina,

Furar da da take zuma mini ba dama.

 

Ina cikin tsaka mai muni,

Hangen Dala ba shiga birni ne ba.

 

Ga tsoro ya aure ni,

Sannan ga rashi na yarda a gare ni.

 

Ahali sun nuisance ni,

Nai sauyin abokanai dan zamani.

 

Giya ta mulki ta ja ni,

Ba ni da sahibi kacokan duka ƙarni.

 

 

Ana ta doka mini ƙalma,

Ina ta artabu da ‘ya ‘yan zamani.

 

Ba ni sati a ƙasata,

Ƙasa-ƙasa ina ta yawon alhini.

 

Ina ta yawon ragaita,

Giya ta mulki na sha ta ishe ni.

 

Rannan in na nufi ƙasata,

Jirgi ya ringa tangarɗar nuni.

 

Wuta tana cin jelarsa,

Ga mu a sarrarin samaniya ba auni.

 

Failot suna kwaminikeshal,

Wai altanatif a sauka cikin gulbi.

 

A ɗaura rigunan iska,

Ana ta cillo mu kamar ‘ya‘yan zabbi.

 

A nan na nemi sikuritis,

Suna tururuwa ta neman hanyar bi.

 

A ka izzo ƙeyata ƙar,

Sheɗa ta tsaya calak ba ta harbi.

 

Nai yi gwauron numfashi,

Nad dawo a haiyaci na al’umma.

 

Ashe tunanin zuci ne,

Nake mafarki daga zaune fa al’umma.

 

Wahabu na gode Allah,

Allah ka tsare ni mulkin al’umma.

 

 

Allah ka bar ni a mai waƙa,

In riƙa sada faɗɗaka gun al’umma.

 

Wahabu ka horon waƙa,

Ga sigar isar da saƙo ba wahala.

 

Cikin salon jera tunani,

Ana nishaɗuwa da babu tabon illa.

 

Alan Kano na kwanar Gana,

Da ke Tudun Muri da yash sha la haula.

 

Ina yabo a gurin Allah,

Da godiya da babu riya da hila Rabba.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments