Ticker

6/recent/ticker-posts

Mutuwa

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi:

Dangi mu yi ɗamarar ko-ta-kwana,

Mutuwa ba ta sallama ko bankwana.

 

Allah na sani kana jin zancena,

Domin kai ka zam mafi kusa a wurina,

In nai kuskure ka yafen zunubaina,

Don haka na saka ka farkon zancena.

 

Sallu alaika ya Rasulu uban Nana,

Mai tsarki da tsarkakar asali guna,

Wanda ya zam sila ta riskar saƙona,

Ko kuma sanadi na samun haskena.

 

Allah kai ka ƙagi ruhi a jikina,

Kai mani rayuwa da ƙaidin kwanana,        

Ka ɗauke ubanmu Ladan a gabana,

Yau fa gare ni gobe sai ga maƙwabtana.

 

Allah kai ka yi ni ba mai tsoro ba,

Ba mai fargabar abin da ka ƙaga ba,

Amma ka sakan tunani mai jazaba,

Mutuwa ta hanan sakata tunanina.

 

Mutuwa na ji na gani da idanuna,

Na san ai babu makawa wata rana,

Zan zamto abin kwatance dangina,

Allah ya sa na ribatu alkhairaina.

 

Na zamto kamar farar kura Allah,

Na gaza in sake in wala ni Allah,

Allah kai yi min gamo da katar Allah,

In cikata da kyau a ƙarshen kwanana.

 

 

Duniya ba madauwamar ɗorewa ba,

Ba bigire na miƙe sawaye ne ba,

Mai bacci ka wartsake tun ba ta zo ba,

Mai raba gardama da yayyanke ƙauna.

 

Mutuwa ta bi nan jiki tun bai zo ba,

Ta ɗauko jirajirai tun ba su zo ba,

Kai har mai cikin da ɗan ba ta ƙyale ba,

Balle kai da ke ɗagawa ikwana.

 

Kai ba a maka albishir ɗorewa ba,

Mai cirani ba ka samu makwanci ba,

Balle ka yi gyangyaɗi har kai kwana,

Wataran za ka wartsake ba gun kwana.

 

Mai tafiya ka duba salkarka ta fata,

Kai guzirin ruwa da kyakkyawar fata,

Ka yi wa kanka tanadi tarkon fata,

Tafiya ta zamo fa dole a hangena.

 

Kai ba a maka albishir ɗorewa ba,

Ka ga da mutuwa baku yi amana ba,

Ba ka da hanzarin da ya fi ka bar murna,

Ka yi kicin-kicin da aikin sarkina.

 

Mai zuba jari ka sa hannun jari,

Mai fa asusu ka zo neman jari,

Mai yin dashi ka zo kai saurari,

Sirrin duk yana ga bautar Sarkina.

 

Wataran in na kalli tarin ‘ya‘yana,

Ga su suna dara suna shauƙin ƙauna,

In na tuno ta sai na kau da idanuna,

Sai ka ga ɓulɓular hawaye a idona.

 

 

 

Na san babu makawa sai ta bi su,

Ɗaya da ɗaya za ta tsin-tsince min su,

Fatana Ubangiji ka tsare min su,

Su yi gamon katar a ƙarshen bankwana.

 

Ita Aljanna ba shiga otel ne na,

Balle in biya kuɗi in wuce gaba,

Sannan ba shiga da ƙarfin ƙwanji ba,

Kai mai bindiga ka gane zancena.

 

Ita Aljanna ba shigar ta da alfarma,

Balle mai naɗi da siffar bangirma,

Mai girma ga Wahidun Sarkin girma,

Mai aiki akan tafarkin manzona.

 

Ba a shigar ta da siyasar ɓaɓatu,

Yanzu gareku ‘yan siyasar ɓaɓatu,

In kun yarda zantukan da nake batu,

Mutuwa za ta gincire ku kuna kwana.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments