Ticker

6/recent/ticker-posts

Daukaka Abar Gudu Abar Nema

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi: Shahara abar gudu abar nema,

Ɗaukaka abar gudu abar nema.

 

Na gode Maɗaukaki mafi girma,

Mai rabo na ɗaukaka san girma,

Yanzu in ya so ka zamo ba dama,

Sai ka ji ana Aminu ba dama.

 

Gaisuwar yabo ga Abdu mai girma,

Tambarin yabo mai busha nema,

Wanda duk maɗaukaka suke nema,

Duniya da lahira abun nema.

 

Hajiya da alhaji suna nema,

Yau zamantakewa gashi ta girma,

Harda haihuwa da ɗa abin nema,

Addu’a ake ɗan a ga ya girma.

 

Ɗa na goye yau zama yake nema,

Daga zaune rarrafe yake nema,

Sai dabo da tatata abar nema,

Sannu-sannu tarbiya ake nema.

 

Kwanci tashi tarbiya fa an sama,

Har da illimin shiga fagen fama,

Daɗa yanzu inna ɗanki ya girma,

Har da ɗaukaka wacce ake nema.

 

Duniya a yau ɗanki ake nema,

Tambarinsa wa a yanzu sha nema,

Yanzu ɗanki addu’a yake nema,

Kar ya hau sama ya fara ɓamɓarma.

 

So yake ya burge dukka mai nema,

Wassu ko rabo nasa suke nema,

Ya gaza rabe fari da baƙƙi ma,

Ya gaza rabe abokanen nema.

 

Ba shi ko rabe dare da rana ma,

Ko dare fa ba ya iya bacci ma,

Wata ran da rana bai iya nema ma,

Ɗanɗano a baki babu ba dama.

 

Ga shi da kamar yana da alfarma,

Sai ya hau gadar zare da ya nema,

Kan ka ce kwabo yana cikin ɓurma,

Ya shiganga ya bonu na ɗan nema.

 

 

 

Babu lokaci ya samu hutu ma,

Babu lokaci na cin abinci ma,

Babu lokaci ya samu barci ma,

Ba a masa uzzuri na mai nema.

 

Ba shi sakata ya wataya shi ma,

Dole yai kaɗan gare su ‘yan nema,

Ba shi sirri ba priɓacy kuma ma,

Masu sharri sharrinsa suke nema.

 

In ka yi abin yabo a ƙyale ma,

Da ka yi abin faɗi a yaɗa ma,

Masu talla har daɗi suke yi ma,

Sai Buwayi wanda ra ka saka ma.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments