Ticker

6/recent/ticker-posts

Yarenmu Abin Alfaharinmu

Daga Alƙalamin Abu Isah Aminu Sani Uba Asshankidy

08162293321
aminusaniuba229@gmail.com

1. Zunzurutun Saƙa Harshe,

Wanda In nai babu kushe,

Babu saɓo gun Bahaushe.

 

2. Zanyi waƙen dan ku gane,

Ni Bahaushen Assaline,

Ga fa saƙon nan a ƙunshe.

 

3. Ko dare kodai da  Rana,

Babu hutu ko na zauna,

So nake zancen  ku amshe.

 

4. Ni fa yaren assalina,

Shi ya zamto fahharina,

Ba ni so na gane shi ƙarshe.

 

5. Al'adunmu mu rungume su,

Koda wasa kar mu bar su,

Kaji ko malam Bahaushe.

 

6. Ga shigar mu abar a koya,

Kar mu barta mu kama yaya,

Ko shigar wasu can mu amshe.

 

7. Kar ku manta ‘Yan uwa na,

Tun a can mu Bamu ɓarna,

Bamu yin aiki na kushe.

 

8. Ga ɗabi'un girmamawa,

Tarbiyarmu abar kulawa,

Babu mai kalla ya kushe.

 

9. Ya kamata mu rungumesu,

Kar mu barsu mu ƙanƙamesu,

Yin hakan mun yaɗa Harshen.

 

10. Don uwa malam Bahaushe,

Na gida kowanne sashe,

Kar ka yo wasa Da Harshe.

 

11. Hausa kwai hikima cikinta,

Gashi wai haushi gareta,

Shi ya sa takwabi na lashe._

 

12. Nai Shiri na sanya silke,

Kana har ɗamara na tamke,

Don dukan ƙofa na toshe.

 

13. Kuma duk ɓarna na share,

Kana duk jifa na kare,

Don kwa Turai nata rushe.

 

14. Gashi rushen ya yi nisa,

Ɗan kaɗan ya rage ta isa,

Dan ta kai yaren mu ƙarshe.

 

15. Gashi mu ko munyi kwance,

Munƙi tashi don mu ƙauce,

Ba ruwanmu da namu Harshe.

 

16. Mun sa kai mun kama nasu,

 Munyi wauta munbi nasu,

 Nasu na gaba namu bushe.

 

17. Ni abin na ban takaici,

 Har ya kan ma sani qunci,

 In na hangi waɗansu sashe.

 

18. Gasu dai asalinsu Hausa,

 Ga uwa tai ma Bahausa,

 Da gani nai sak Bahaushe.

 

19. Amma fa idan ka bashi,

 Alƙalami kat-tittsiye shi,

 Yai rubutun nashi Harshe.

 

20. Koda wasa bai iyawa,

 Na shi Yaren yai gazawa,

 Baya koyan nashi Harshe.

 

21. Shi wuri nai baida ƙima,

 Bai zaton zaiyo nadama,

 Ka yi wauta kai Bahaushe.

 

22. Kai zato naka ya yi muni,

 Shi ya sa ni na ɗanyi nuni,

 Don mu bar mugun Hasashe.

 

23. Ni Aminu abin nufi na,

 Wanga shashanci mu dena,

 Duk mu dawo namu Harshe.

 

24. Zan tsaya nan don na huta,

 Zaku ji Ni da ƙarashenta,

 Dan ku san waye Bahaushe.

 

25. Zan rufe ta da yin salati,

 Gun nabiyyu da ali baiti

 Shugaban farko da ƙarshe.

ALHAMDULILLAH

May 21, 2023 

Daga Alƙalamin Abu Isah Aminu Sani Uba Asshankidy

Daga Alƙalamin Abu Isah Aminu Sani Uba Asshankidy

Post a Comment

0 Comments