Takarda Wadda Aka Gabatar Domin Tunasarwa Da Ba Da Shawara Ga Makaɗan Baka Na Hausa A Shiryawa Da Tsara Matanonin Waƙoƙinsu Bisa Dacewa Tare Da Zaɓo Ingantattun Kalmomi Kafin Su Rera, Su Kuma Sadar Da Su. Lahadi, Mayu 07,2023/SHAWAL 17,1444
SA’IDU
MUHAMMAD GUSAU,
SASHEN
KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA,
JAMI’AR
BAYERO, KANO.
1.0
Gabatarwa
A wasu
rubuce-rubucen da na aiwatar[1] na
tattaɓa nazari a kan dabarun aiwatarwa da rerawa da sadarwar waƙoƙin baka na
Hausa. Haka kuma na kalli yanayin harshen waƙar baka da furuci a Zubin waƙoƙin
baka da kuma yadda Sarakuna na al’ummar Hausawa suka fara zama masu ɗaukar
nauye-nauye na wasu makaɗan baka. An kuma duba wasu waƙoƙin makaɗan baka da
suka waƙe wasu mabambantan Ubangida a matsayinsu na jagororin al’ummar Hausawa ko
gwarzaye ko masu ilimi ko masu hikimomi ko masu fasahohi ko masana falsafofi.
Har wa yau kuma Makaɗan baka bisa turbobinsu fitattu su ne waɗanda suke shirya
waƙoƙinsu a kan kyawawan al’adun Hausawa da na addinin Musulunci.
Waƙoƙin baka na
Hausa sun jima a tsakanin Hausawa waɗanda aka fara gudanar da su tun ran gini,
ran zane. Waƙoƙi ne da suka danganci zamantakewar Hausawa har zuwa yau da suke
ta bunƙasa, lokaci bayan lokaci.
Su waƙoƙin baka,
waƙoƙi ne waɗanda ake shiryawa da aiwatarwa da rerawa da sadarwa da amo na
murya a haɗe da amo na kiɗa. Hausawa sun soma wanzar da amo na kiɗa a waƙar
baka ta amfani da wasu abubuwa da ba an yi su ne kawai domin a haɗa su da waƙar
baka ba[2].
Daga nan kuma Hausawa suka sami fasaha da azanci na ƙirƙiro kaya na musamman domin
a buga ko a kaɗa su, su ba da amo ko sauti na kiɗa, sannan a haɗa murya da amon
su tayar da rauji na waƙar baka ta Hausa[3]. A
hulɗoɗin Hausawa da baƙin al’ummu sun sami ƙari na wasu kayan kiɗa da ake
ambata kayan kiɗa na baƙin al’ummu[4].
Kamar yadda aka
soma yin bayani a baya, a zangon da Hausawa suka ɓullo da tsari na makaɗan baka
ne aka fara shirya kayan kiɗa da za a iya haɗa amonsu ko sautinsu da furucin baki
(murya) a samar da rauji wanda yake hawa ko sauka ko faɗuwa
a madirar kalmomi na ƙarshen layuka ko saɗaru a ɗa ko ɗiya
na zubin matanoni na waƙar baka Bahaushiya.
Ta fuskar haliyyar
waƙoƙin baka na Hausa, makaɗan Hausa sukan shirya waƙoƙi masu turaku ko saƙonni
manya game da hidimomin da Hausawa suke gudanarwa a zamantakewarsu a bisa doron
ƙasa. Ciki kuwa har gami da halaye da nauye-nauye da suka ɗoru a wuyayen
Sarakuna da sauran manyan rukunoni na masu Sarauta da shugabanci.
Idan aka yi
la’akari da ire-iren waƙoƙin baka na Hausa za a iya rarraba su zuwa:
i)
Waƙoƙin makaɗa a Turke da Sarakuna (Turkakkun
Makaɗan Sarauta): Makaɗan baka turkakku sukan jingina waƙoƙinsu kawai zuwa ga
Sarakuna da sauran masu Sarautu. Daga cikinsu akwai Muhammadu Dodo Maitabshi,
Sakkwato, Gwadabawa da Buda Ɗantanoma, Argungu da Ibrahim Narambaɗa, Tubali,
Isa da Salihu Jankiɗi, Gusau, Sakkwato da Abubakar Akwara, Sabon Birni da Abdu
Kurna, Maradun da Sa’idu Faru, Sakkwato da Sa’idu Maidaji Rambaɗawa, Sabon
Birnin Gobir da Aliyu, Sarkin Kotson Kano[5] da
sauransu da yawa.
ii)
Waƙoƙin Makaɗan Sarakuna a Sake: Su ne waƙoƙi
waɗanda makaɗa suke yi wa kowane Sarki. Misalan makaɗa na wannan kaso su ne
Aliyu Ɗandawo, Shuni, Argungu, Yawuri da ɗansa Sani Aliyu Ɗan’dawo Yawuri da
Hussaini Sarkin Makaɗan Gusau da Makamantansu.
iii)
Waƙoƙin Makaɗan Sarakuna da Game-Gari: Su
ne kamar Musa Ɗanƙwairo Maradun da Musa Ɗanba’u da Dr. Aminu Ladan Abubakar,
Alan Waƙa, Sarkin Ɗiyan Gobir da Imamu Sunusi Ɗanƙwairon Katsina da ire-irensu.
iv)
Waƙoƙin Makaɗan Siyasa a Turke: Ire-iren
Makaɗan siyasa a turke sun haɗa da Tijjani Gandu (NNPP) da Kabiru Muhammad Birnin
Magaji (PDP) da Shamsu Huwarich (PDP) da Musa Ɗanba’u (PDP) da makamantansu.
v)
Makaɗan Siyasa a Sake: kamar Dauda Kahuta
Rarara (PDP, APC, NNPP) da Sanusi Aliyu Gadanga, Gusau da sauransu.
vi)
Waƙoƙi na Makaɗa Game-Gari wato Makaɗa na
Kowa da Komai: Misali Dr. Mamman Shata Katsina da Dr. Adamu Ɗanmaraya Jos da
Aliyu Gadanga, Gusau da Babangida Kakadawa, Gusau, Sakkwato da Naziru Muhammad
Ahmad, Sarkin Waƙa, Kano da Prince Adam A. Zango, Kaduna da S. Fada, Kano da
Muftahu Umar Muhammad, Kano da Aliyu Rijiyar Zaki, Kano (Chairman) da Sarfilu
Sarkin Waƙa da Nazifi Asnanic da ire-irensu.
vii)
Waƙoƙin Makaɗan Bege: Su ne waƙoƙin da
wasu makaɗa suke yi wa Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, da dukkan
ahalinsa da sauran Manzanni da Annabawa da Mujaddadai. Makaɗan nan sun ƙunshi
Hafizu Abdullahi, Kano da Fadar Bege, Kano da Ahmad Muhammad Sabi’u (Shehi)
Kano da Bashir Ɗandago da Sadi Sidi Sharifai, Kano da Rabi’u Usman Baba, Kano
da Bashir Ɗanmusa da Halifa Sanusi Gyaranya da Kawu Dogarai da Rabi’atu da
Shamsu mai Rangaɗaɗau da Kabiru Classic, Gusau da sauransu da yawa.
viii)
Waƙoƙin Makaɗan Soyayya a Turke: Kamar na
Umar M. Sharif, Kano da Hamisu Sa’id Breaker, Kano da Abdul D. I. da Auta
Waziri da Auta M. J. Boy da Sani Ahmed da Sadiƙ Sale da Husaini Danko da Adamu
Hassan Nagudu da sauransu.
A dunƙule, waɗannan
nau’o’in makaɗan baka na Hausa da ma waɗanda ba a jero sunayensu a nan ba, an
daɗa karkasa su zuwa:
-
Makaɗan Bege
-
Makaɗan Sarakuna
-
Makaɗa Game-Gari
(Gusau, S. M.
(2002) sh. 161-162)
Ƙananan batutuwa
su a wannan takarda sun ƙunshi:
º
Ma’ana da Tarihin Shigar Ubangida a Waƙar
Baka Bahaushiya
º
Daidaita Tunani da Tsinkaya a Waƙoƙin Baka
na Hausa
º
Ubangida a Ɗiya ko a Waƙoƙin Makaɗan
Baka na Hausa
º
Zambo da Habaici a Waƙoƙin Ubangida
º
Tsakure a Misalce na Wasu Ɗiya ko Waƙoƙi
da Wasu Makaɗan Baka Suka yi wa Ubangida
2.0
Ma’ana da Tarihin Shigar Ubangida a Waƙar Baka
Bahaushiya
2.1
Ma’anar Kalmar Ubangida
Kalmar Ubangida
tana da tsagi biyu Uba + n gida, an haɗa kalmomin biyu da alamar (-n
) mai nuna wata dangantaka. An kuma ɗauki kalmomin su zama ɗaya a wata ƙa’ida
ta rubutu na daidaitacciyar Hausa (Galadanci, M. K. M. (1976).
Uba
kalma
ce ta suna wato Mahaifi ko Shugaba ko Jagora. -n gida kuwa
wani haɗi ne mai nuna dangantaka (CNHN, 2006, Sh: 461).
Ma’anar Kalmar Ubangida
ta fuskar fannin ilimi ko isɗilahi wato bisa ganowa ko kiyasin Malamai ko
masana ko manazarta ita ce:
Shugaba
ko Sarki ko wani jami’i ko attajiri ko masani ko ma’aikaci ko soja ko ɗansiyasa
ko sauransu, manya, masu kamala, masu matsayi ko wata daraja, waɗanda kuma makaɗin
baka ya yi wa wata waƙar baka ta Hausa bisa daidaitaccen shiri da rauji da
rerawa da sadarwa (Gusau, S. M. 2008, sh. 459).
2.2
Tarihin Shigar Ubangida a Waƙar Baka Bahaushiya
Hausawa sun ɗauki
lokaci mai tsayin gaske suna shiryawa da rerawa bisa rauji mai gamsarwa tare da
isar da wani saƙo dangane da wasu fannonin rayuwa daban-daban.
Wani tsari da ya
shigo cikin waƙoƙin baka na Hausa, shi ne a sami wani makaɗi na baka ya nace wa
wani Sarki ɗaya a yi masa waƙoƙin baka. A haka makaɗin zai turke kansa a da’ira
ta Sarki ɗaya.
Domin haka, tun
daga daidai lokaci ne, wasu makaɗan baka, suka mayar da hankula wajen yi wa
Sarakuna[6] waƙoƙi,
suka kuma ɗauke su a matsayi da muƙami na iyayen gidajensu. Ta wannan wasiɗa
sai Sarakunan suka kasance masu jiɓintar hidimomi da ɗaukar nauye-nauye na
muhimman al’amura na waɗannan makaɗa.
A kwana a tashi,
musamman da tafiyar Hausawa ta tsala a cikin hada-hadar amincewa da sauraron waƙoƙin
baka, sai a wasu zanguna, tun ma na mulkin farar hula wato ‘yansiyasa da mulki
na masu kakin Soja wato Sojoji ba, makaɗan baka sun daɗa buɗa matsayi na Ubangida
har ya ƙunshi:
·
Sarakuna, manya da ƙanana, da iyayen ƙasa
da hakimai da dagatai da masu unguwanni da sauran masu riƙe da muƙaman Sarautu;
·
Jami’an Gwamnati tun daga Shugabannin Ƙasa
da Gwamnoni a Jihohi da Ministoci da Kwamishinoni da Ciyamomi da Sakatarori da
sauran jami’ai madangantansu;
·
Attajirai, masu kuɗi ko tarkoki ko
kamfanoni ko masu gudanar da harkoki madanganta kasuwanci da saye da sayarwa;
·
Manya da hamshaƙan mutane masu tafiyar da
sauran al’amura na sana’o’i;
·
Mashahuran Malamai na addinin Musulunci ko
na sauran fannonin ilimi;
·
Mutane masu darajoji a sauran rukunoni da
kadadu na tarayyar Hausawa da a dukkan al’ummu waɗanda Hausawa suke yin hulɗoɗi
da su a duniya.
3.0
Daidaita Tunani da Tsinkaya a Waƙoƙin Baka na Hausa
Nagarta da
kwarjini na waƙoƙin baka sun ta’allaƙa ne ta fuskar aiwatar da su cikin
jeranta tunani da zaɓo kalmomi a kowane matani na waƙar baka da za a shirya, a
rera, a sadar da shi. Ashe ke nan ya zama wajibi ga masu yin waƙoƙin baka su
zama masu tsinkaya, masu hararowa, masu hango baya da gaba, tare da yin lura da
taka-tsantsan da neman dacewa bisa furuci na waƙar baka da za su dinga farfaɗa.
Har wa yau kuma makaɗan za su dinga tantance yanayi da nauyin daraja na waɗanda
suke yi wa waƙoƙin baka, musamman dangane da lokaci da zanguna mabambanta na
tattakinsu (Gusau, S. M. (2008) Sh: 463).
Makaɗa na waƙoƙin
baka, hakazalika, ya dace su dinga tsayawa kan hauji da haddi dangane da nau’o’in
kalamansu a waƙa, ba tare da shige gona da iri ko zarce iyaka ba[7].
Akwai alfanu matuƙa
makaɗi ya jeranta tunaninsa a waƙa, ya kuma lura Hausawa suna ƙarfafa halaye da
abubuwa kyawawa kuma nagartattu. Kada furuci ko kalamai na waƙoƙin makaɗa ko
mawaƙa su kasance sanadai na haƙa ramin mugunta ko su ba da wata kafa wadda za
ta iya sabbaba ce-ce-ku-ce ko tsagewar bango. Ashe ke nan wajibin makaɗi ne ya
dinga furuci mai kan gado[8].
Sannan mai yin waƙar
baka, ya sani cikin haƙiƙancewa, shi mutum ne mai gyara rayuwar al’ummarsa ta
Hausa da tarsashi na jinsuna madanganta hulɗoɗin Hausawa. Makaɗin baka alƙalami
na al’ummarsa ne, mai sarrafa takobi, mai kaifi, da garkuwa da kiyayewa da
tabbatar da alfarma da muhibba na waɗanda yake yi wa waƙoƙi, ba tare da kuma yana
gaya musu furuci na kowace irin fallasa ba[9].
Haka zalika, shi Ubangida
a ma’anarsa ta fannin ilimi, sananne ne, mai ƙima, wanda kuma za a raga
masa bisa wata maslaha kai ko ma don dole. Ubangida, a tunanin wasu a
yau, ya shiga sahun da Hausawa suke nunawa, ‘Ana jin kunya tasa ko don dole’.
Akan ba shi haƙƙoƙinsa da suka ta’allaƙa da shi. Allahu ne mai shiryarwa![10]
Wata shahararriyar
dabi’a ta makaɗi mai Ubangida, a zamantakewar Hausawa, a da ko a yau,
yakan riƙa Ubangida[11]
da ƙima, ya dinga girmama shi, ya tsare yi masa biyayya, ya dinga zaɓen kalmomi
na jamala yana gaya masa. Shi kuma Ubangida yakan amince da makaɗi, ya zama
sirrinsa, ya dinga kulawa da shi, ya kuma karkatu a yi masa hidimomi gwargwadon
iko domin amana da zaman tare.
4.0
Ubangida a Ɗiya ko a Waƙoƙin
Makaɗan Baka na Hausa
Makaɗan baka sun
ci gaba da shiryawa Ubangida waƙoƙi masu turaku na kansu ko waɗanda suke saka
su a cikin ɗiya na wasu waƙoƙi a matsayin ƙananan saƙonni. Ke nan makaɗi yakan
iya ƙulla babban saƙo wato turke a waƙa sukutum ko ya jefa ƙaramin saƙo a tsari
na tubali a ɗa ko ɗiya na wata waƙa da zai danganta su da Ubangidansa.
Yana daga cikin kulawar
makaɗi, ya aiwatar, tare da sadar da waƙoƙi ga Ubangidansa domin ya bayyana ƙauna
da soyayya da zumunci da hulɗoɗi ƙwarara da suke a tsakaninsa da shi
(Ubangidansa).
Makaɗi zai dinga
gaya wa Ubangidansa kalamai na zubin waƙoƙin baka ta rauji mai garɗi cikin
sadar da zaɓaɓɓun kalmomi masu nagarta, masu fitowa da mutunci da muhibba da
kwarjini da taimako nasa. Ya dace, zubin nan ya zama mai jan hankali, mai
sakawa da samar da nustuwa, a yawancin lokuta ma, zubin ya kasance mai ɗaga
zuciya, mai sa mata farin ciki da kawar mata da kowace irin damuwa. Haka kuma
zubin ya danganci cicciɓawa da kwarzontawa gwargwadon matsayi na Ubangida.
Makaɗi kuma ya
zamana ya kauce wa kowaɗanne irin kalmomi ko ƙananan matanoni na batsa ko
zage-zage ko cin fuska ko sukar muruwa ko faɗar da mutunci ko muhibba ko kuma
kowace hasla wadda take da muni ko take taɓa alfarma da mutuntaka ta maigida ko
Ubangida[12].
Makaɗan baka na
Hausa sukan jingina waƙoƙin da suke yi wa iyayen gidajensu bisa waɗannan turaku
ko tubalai:
·
Bege
·
Yabo
·
Soyayya
·
Karimci
·
Kyauta
·
Baiwa
·
da sauransu da yawa
Haka kuma sukan
zuba wa matanoni na waƙoƙi na mabambantan Ubangida dabaru na adon harshe
da jan hankali da daɗa tabbatar da daraja da ƙima da jamala. Ga wasu daga cikin
dabaru na hikimomi da azance-azancen maganganu:
·
Kamantawa
·
Siffantawa
·
Alamtarwa
·
Kinintawa
·
Alkunyantawa
·
Barkwantawa[13]
·
da sauransu
Wasu turaku ko
tubalai ko dabarun adon harshe cikin zaɓaɓɓun kalmomi da makaɗan baka suke
furta wa Ubangida, wasunsu ne a jadawali kamar haka:
|
A siga ta yi wa Ubangida
ado ko yi masa kwalliya ko yi masa tajmili ko shela ko jan hankulan mutane
a kan halayensa ko ɗabi’unsa ko tallafinsa ko taimakonsa ko nauyi na
tausayinsa, makaɗan baka sukan kwatanta shi da:
·
Dabbobi masu kwarjini, masu buwaya, masu
taƙama masu wobuwa, masu shaja’a ko jaruntaka ko nauyi na iko da mulki a
tsakanin sauran dabbobi a Gandun Daji.
·
Tsuntsaye masu halaye da ɗabi’u na jamala
da kwarjini, ba masu yawan surutu irin suda ba. Duk da yake Makaɗa
Sa’idu Faru ya kwatanta Ubangidansa, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo a
yayin da yake riƙe da Sarautar Sarkin Kudan Sakkwato da Suda wadda ta yi
wani ɗan waƙa ta bayyana muhibba ta Macciɗo da Sa’idu Faru. Haka kuma Abubakar
Imam ya yi amfani da Aku, ya ɗora shi a matsayi na Wazirin Sarki a Magana
Jar ice.
·
Itatuwa da bishiyoyi da ƙwari na tudu da
na ruwa da gulabe da fadama da saiwoyi da tsirrai da makamantan waɗannan
abubuwa ko halittu a duniya.
5.0
Zambo da Habaici a Waƙoƙin Ubangida
Zambo da habaici
da baƙar magana da shaguɓe da ba’a da arashi da gatse da gugar zana da dungu,
kai hatta ma da tumasanci, suna daga cikin maganganun hikima ko azancin magana
da wasu Hausawa suke shiryawa ta furucin baki. Hausawa sukan ƙirƙiri maganganun
hikima a hulɗoɗin rayuwa a zamantakewa ta dare da ta rana domin
hannunka-mai-sanda da yin gargaɗi da jan hankali da tunasarwa da faɗakarwa da
neman a yi taka-tsantsan da sauransu (Gusau, S. M. (2011) sh: 14-15).
Kamar yadda
bincike ya tsinkayo, zambo da habaici da baƙar magana da ba’a da barkwanci,
azance-azance ne na hikima da sukan tusgo ko kutso ko ratso zubi na wasu
matanoni na waƙoƙin baka na Hausa domin hannunka-mai-sanda ko nuni cikin waƙa
ko faɗakar da al’umma ko jan kunne ko madangantan waɗannan halaye.
Alal-Misali, Budan
Zakka, Makaɗa Buda Ɗantanoma, Argungu ya furta wani ɗa na waƙa inda ya
faɗi:
Jagora: Sama ba
yaro ba,
: Ba aboki nai ba,
Y/Amshi: Ba warin yaro barwa,
Jagora: Ba
matsuwa, sa tuba,
Y/Amshi: Ba sake faɗin an yi,
Jagora: Mamman mai
wada yas so,
Y/Amshi: Sarkin ɗibah haushi,
: Gagara Ƙarya
Sadauki,
: Jangwarzon Alƙali.
(Waƙan Buda Ɗantanoma
ta Sarkin Kabin Argungu
Muhammadun Sama (Gusau, S. M. 2008, Sh; 234)
A wannan ɗa na waƙa,
Buda Ɗantanoma, ya baza himma wajen ayyana wasu fitattun halaye na ƙima da
daraja da ƙwato wa jama’a haƙƙoƙinsu da tsayuwa kan gaskiya wofintu daga yin ƙarya
na Ubangidansa, Sarkin Kabin Argungu Muhammadu Sama.
Ƙari a haka kuma,
akwai wasu makaɗan baka da sukan kare ko daɗa bunƙasa mutunci da muruwa na
Ubangida ta fuskar shirya wa wasu zambo ko habaici domin nuni cikin waƙa.
Dubi wata magana
ta hikima cikin ishara da makaɗa Ibrahin Naranbaɗa Isa yake gaya wa Sarkin
Gobir na Isa, Alhaji Amadu Bawa I wani zance da wasu suka yi maras tushe. Ga
kalmomin da ya yi masa nuni da su cikin waƙa:
Jagora: Baban
Maiwurno bar su can su yi zancen banza,
Y/Amshi: Mai ga-noma bai yi ƙwazon mai gona
ba.
Jagora: Ka ji wai
mai roƙo hura ya sha ya shige danga ta,
Y/Amshi: Sai ka ji ya raina mai dame arba don ƙarya,
: Ka san tabbatar
tsiya ga matsaci an nan,
: Gwarzon Shamaki
na Malam toron giwa,
: Baban Doda ba a
tam ma da batun banza.
(Waƙar ‘Gwarzon
Shamaki’ ta Ibrahim Narambaɗa wadda ya yi wa Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa I
(Gusau, S. M. 2008, Sh; 255-256)
A yayin zaman
tare, a wasu lokuta, akan sami gilmayya da faruwa na wasu abubuwa kamar damuwa
da nuna ƙiyayya ko wata jayayya ko cin dudduge ko wasu ayyuka na wuce gona da
iri da ire-irensu. A aukuwar ire-iren waɗannan halaye, makaɗan baka sukan
shirya kalmomi a cikin ƙananan saƙonni domin su kiyaye mutunci da baiwoyi na Ubangida
ko su yi masa garkuwa ta katangar dutsi ko ta kalmomin ƙarfe irin na
kandiri ko kwangiri.
Ga wani misali
daga wani ɗan waƙa ta ‘Gagara Ƙarya, ta Buda Ɗantanoma Argungu shi ne:
Jagora: Kanta
Ubanzagi, Jibo as Sarki,
Y/Amshi: Ba Sarkin ƙaƙe ba,
: Gagara ƙarya sadauki,
: Jangwarzon Alƙali.
A wannan ɗa Buda Ɗantanoma
yana yi wa wasu habaici ne masu yawo da wata ƙaramar magana suna nuna
Ubangidansa, Muhammadun Sama Argungu, wai ba jarumin Sarki ne ba.
A wani ɗan waƙa
kuma makaɗa Buda Ɗantanoma Argungu yana kare kansa da kansa inda yake faɗin:
Jagora: Mai nuƙura
da Buda Sarkin Turu,
Y/Amshi: Bai san Allah na ba,
: Gagara Ƙarya
Sadauki,
: Jangwarzon Alƙali.
(Gusau, S. M.
2008, Sh; 243-247)
Makaɗa Sa’idu Faru
ya mutunta wasu tsuntsaye, suda da burtu, ya mayar da su mutane ko makaɗa, kuma
suna ta rera wa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo[14]
wani ɗan waƙa na kwarzanta shi da bayyana darajojinsa. Hatta Larabawa ma sun
shiga yi wa Sarkin Kudu Macciɗo (Sarkin Musulmi) waƙoƙi masu mutunta shi da
fito da darajojin da Allahu ya yi masa. Ga kalmomi na wannan dogon ɗa na waƙa
kamar haka:
Jagora (Ɗani[15])
: Nic ce suda waƙa akai,
: Tac ce lallai waƙa
nikai,
: Waƙam Muhamman
Sarkin Kudu,
: Waƙan nan da Ɗan’umma
yai mashi,
: Baicin uwat
tsuntsaye nike,
: In da kamam
Mulki na nikai,
: Da nai mai wasiƙa
yai min kiɗi,
: Dannan ni ko sai
niw wuce,
: Can nat taɓa yat
tafiya kaɗan,
: Sai ni ishe burtu
na kiwo,
: Shina ta waƙar
Sarkin Kudu,
: Ala Sabbinani ɗan
Amadu,
: Allah shi ƙara
mai nasara,
: Nic ce burtu waƙa
akai,
: Yac ce lallai waƙa
nikai,
: Waƙam Muhamman
Sarkin Kudu,
: In na yi ta za
ni wurin kiwo,
: In na zo abinci
sai na rage,
: Sai ni ko sai
niw wuce,
: Can na taɓa yat
tafiya kaɗan,
: Nik kai bakin
bahar Maliya,
: Sai ni ishe
Larabawa wurin,
: Suna ta waƙas
Sarkin Kudu,
: Rainai ya daɗe
Sarkin Kudu,
: Ala Sabbinani ɗan
Amadu,
: Allah shi ƙara
ma nasara,
: Ɗan mai daraja
Sarkin Kudu,
: Jikan mai daraja
ɗan Amadu,
: Sannan mai
daraja shi yay yi shi,
: Shina gida zanne
a Sakkwato,
: In ya yi salla
yai tazbaha,
‘Y/Amshi: Hasken nashi han nan kallo mukai,
: Kana shirye Baban
‘Yan’ruwa,
: Na Bello Jikan Ɗanfodiyo.
(Waƙar Sa’idu Faru
ta Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo (Sarkin Kudun Sakkwato a da) Gusau, S. M.
(2009) Sh: 155-156)
Wasu
maganganun hikima da ake tsattsarmawa a wasu waƙoƙin baka na Hausa, musamman na
Ubangida, su zama ƙananan saƙonni, a taƙaice sun haɗa da:
-
Zambo
-
Habaici
-
Gargaɗi
-
Faɗakarwa
-
Tunasarwa
-
Nuni
Cikin Waƙa
-
Taka-Tsantsan
-
Ƙima
-
Muhibba
-
Ayyana
Daraja
-
Ɗaukaka
Daraja
-
Tsaron
Mutunci
-
Bunƙasa
Mutunci
-
Bayyana
Mutunci
-
Inganta
Rayuwa
-
Kyautata
Rayuwa
-
Bunƙasa
Muruwa
-
Girmama
Muruwa
-
Kariya
-
Kangiya
-
Garkuwa
-
Dakushe
Azarɓaɓiya
-
Hana
cin Dudduge
-
Hannunka-mai-Sanda
-
Ingiza
mai Kantu Ruwa
-
da
Sauransu
6.0
Tsakure a Misalce na Wasu Ɗiyan Waƙoƙi da Wasu
Makaɗan
Baka Suka yi wa Ubangida
Kamar yadda aka
kawo bayani a baya, akwai misalai na wasu ɗiyan waƙoƙin Hausa waɗanda makaɗan
baka suka sassaka kalmomi masu fitowa tare da ɗaga darajoji da kwarjini da ɗaukaka
da muhibba da taimako da buwaya da tsayuwa a kan duga-dugi da sauransu waɗanda
suka danganta su da Ubangida daban-daban.
A wannan fage za a
kawo misalai ƙalilan kamar haka:
6.1
Ibrahim Gurso Mafara, yanzu Jihar
Zamfara, ya gaya wa Ubangidansa, Sarkin Musulmi Abubakar III, a yayin da yake
riƙe da Sarautar Uban Ƙasa ta Sardaunan Sakkwato a Talata Mafara a 1938, dab da
zai zama Sarkin Musulmi, ya haye halifa ta Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo a zama na
Sakkwato:
Jagora: Iro ni na
dace,
: In Sarki yas so
ka,
: Ka hi gonat
taki,
: Ka hi hwataucin
Gwanja,
Y/Amshi: Tun da Allah yab ba ka,
: Ƙara godiya mukai,
: Gagarau ɗan
Shaihu,
: Garba Rura
gwarzon Atiku,
: Sa maza ladab.
(Ibrahim Gurso a waƙar
Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar III, dab da zai zama Sarkin Musulmi a 1938
(Gusau, S. M. 1988: Juzu’i na Biyu).
6.2
Alhaji Salihu Jankiɗi, Sarkin Taushin
Sarkin ya shirya wa kansa wasu kalmomi na sanin kima da zalaƙar waƙar taushi ta
Ubangida. Ya furta ɗan ne a cikin da ya yi wa Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar
III (1938-1988). Ga ɗan waƙar kamar haka:
Jagora: Jumurin kwaram
a kwana ana tahiya,
: Sai goga,
jaki bai kai nan ba,
Y/Amshi: ‘Yan yara masu kurin waƙa, ku bar
wargi,
: Ma’ana ba ta
zama ɗai ba,
: Ni ba ni yin kiɗin
iska sai ga Sarkina,
: Ɗibgau bajinin
dole,
: Abubakar na Amadu
ya gyara Masallaci.
(Salihu Jankiɗi a
waƙar Sarkin Musulmi, Abubakar III, ‘Ɗibgau bajinin dole’ (Gusau,. S. M. 2002.
Sh: 95-96).
6.3
A wani ɗan waƙa, Mamman Sanƙira ɗan
Makaɗa Idi Ɗangiwa Zuru ya bayyana ƙaramin saƙo ko tubali na ginin waƙa dangane
da zaman mahaifinsa Sarkin Taushin Zuru, Alhaji Idi Ɗangiwa Zuru a Masarautar
Sarkin Zuru. Ga ɗan waƙar kamar haka:
Jagora: Mamman na
jiya tun hwarko,
: Wannan ya zamo
tarihi,
: Ɗangiwa da yaz
zaka Zuru,
: Mamman Sani yak
kawo shi,
: Sannan Garba
Sami ka iko,
‘Y/Amshi: Shi kau yar riƙe mu da kyawo,
: Yanzu ko Shehu
Danga ka iko,
: Shi kuma ya riƙi
mu da kyawo,
: Alhaji Sa’idu ɗauki
abinka,
: Don kak ka ban
ni ga daji,
G/Waƙa: Koma shirin maza ɗan Mamman,
: Alhaji ba a kai
ma raini.
(Waƙar Mamman Ɗangiwa
Zuru ta Alƙali Sa’idu. Gusau, S. M. 1988: Juzu’i na Biyu).
Jagora: In dai kag
ga matag gado,
: Ita in ta taho
ga mijinta,
Y/Amshi: To, shi ko, shi riƙe ta amana,
: Don dai kas shi
bat ta ga hanya,
: Koma shirin maza
ɗan Mamman,
: Alhaji ba a kai
ma raini.
(Waƙar Mamman Ɗangiwa
Zuru ta Alƙali Sa’idu. Gusau, S. M. 1988: Juzu’i na Ɗaya: 226 & Juzu’i na
Biyu).
6.4
Makaɗa Sa’idu Faru, Makaɗin Sarkin
Kudu Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III, shi kuma ga abin da
yake faɗa:
Jagora: Alhaji
Baba Muhammadu Macciɗo,
Y/Amshi: Baba barka da hayewa Maliya,
Jagora: Waƙag ga
da nim maka Muhammadu,
: Na ji daɗinta
Mamman Sarkin Kudu,
: Tun da Kabi hak
Kano ham Masar,
: Hab birnin Legas
hab Bichi,
Y/Amshi: Kowa ya ji waƙar Sarkin Kudu,
G/Waƙa: Kana shire Baban ‘Yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora (Ɗani/Mu’azu):
Maganag ga da za ni faɗa maka,
: Gagarau ɗan
Aliyu kai man gafara,
: Wada duk aka
gadon ƙasura,
: Wada duk aka
gadon ɗaukaka,
: Wada duk aka
gadon ci gaba,
: Mamman ka gaji
Abubakar,
: Ko da sayen halin
nan a kai,
Y/Amshi: Baba halin da ka kai kuɗɗi shikai,
G/Waƙa: Kana shire Baban ‘Yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora: Ko da ni
makaɗin Ubanzagi,
: Na gaji ka ba mu
dawakuna,
: Na gaji ka ba mu
jukunkuna,
: Na gaji ka ba mu
garuruwa,
Y/Amshi: Muhammadu in Allah yai nuhi,
: Ba mu gari da
mutanenai duka,
Jagora: Na gode riƙon
Baban Zagi,
Y/Amshi: Allah shi yi ma babban rabo,[16]
: Albarkar Shehu
da Bello,
: Had da Atiku
zuwa Sarki Hassan,
G/Waƙa: Kana shire Baban ‘Yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
(Sa’idu Faru a Waƙar
Sarkin Kudu Macciɗo kafin ya zama Sarkin Musulmi. Gusau, S. M. 2009. Sh:
152-154)
6.5
Alhaji Muhammadu Bawa Ɗan’anace a Waƙarsa ta Ɗanduwa
ya kwarzonta shi, yana faɗin:
Jagora: Maza ga giwa
ma sha dahi,
: Zaki mai ƙashi
guda,
Y/Amshi: Gwanki mai kiyon ɓata,
G/Waƙa: Ba tsoro garai ba,
: Ɗandunawa maƙi
gudu.
Jagora: Da in ɗauki
bugunka Duna,
Y/Amshi: Gwamma a halban da bindiga,
Jagora: Bindiga in
kashi takai,
Y/Amshi: Ko hannu kashi yakai,
G/Waƙa: Ba tsoro garai ba,
: Ɗandunawa maƙi
gudu.
(Waƙar Ɗan’anace
ta Ɗandunawa. Gusau, S. M. 2014. Sh: 95-96)
7.0
Kammalawa
Kamar yadda aka
nuna tun a tsakure da gabatarwa, wannan takarda ta yi Nazari ne kan matsayi da
darajar Ubangida a Waƙoƙin Baka na Hausa’.
Muhimman kalaman
da aka kawo su a rubutun nan bisa taƙaitawa, sun fuskanci bayani kan Ubangida
da fasalolin shigar Ubangida a cikin zubi na matanonin waƙoƙin baka na
Hausa. Daga nan kuma aka ɗora nazari a kan wasu yanaye-yanaye da suka cancanta
makaɗan baka su dinga saisaitawa da daidaita tunane-tunanensu da tsinkayoyinsu
a manya da ƙananan saƙonni wato turke da tubalan ginin turke na Zubin waƙoƙinsu.
Haka kuma an kawo
wasu sigogi da matakai waɗanda makaɗan waƙar baka Bahaushiya suke bayyana Ubangida
a kansu, misali ta fito da asalinsa da nasabarsa da zuriyyarsa da
kwarjininsa da ɗaukakokinsa da himmominsa da tallafe-tallafensa da karimcinsa
da baiwoyinsa, musamman da ya samu daga Allah, mai yadda ya so bisa ikonsa da
rahamominsa.
A wasu lokuta,
sukan yi adontawa tare da yi wa Ubangida kwalliya da kwatanta shi da
wasu halittu kyawawa, masu jamala, masu ƙarfi ko shaja’a ko waibuwa ko
siddabaru ko makamantan waɗannan abubuwa.
Makaɗan Ubangida
kuma an nuna sukan tsarma wasu maganganun hikima ko azanci ta yi wa al’umma
hannunka-mai-sanda ko tunasarwa ko faɗakarwa ko taka-tsantsan ko gargaɗi, a
wasu lokuta kuma har da yi musu ingiza-mai-kantu-ruwa, duka a furuci da rauji
na waƙoƙin baka na Hausa.
Takardar nan ta
ayyana, makaɗan baka, sukan jefo zambo ko habaici ko baƙar magana ko ba’a ko
arashi ko gugar zana da sauransu don yin kariya da garkuwa ga Ubangida da
sauran waɗanda suke yi wa waƙoƙi.
Daga nan ne aka
kawo wasu misalai a dunƙule na ɗiya da makaɗan baka suke yi wa Ubangida ko
wani wanda suke yi wa gayaunar waƙa.
Kamar yadda aka yi
bayani a binciken nan, an yi tunasarwa ne da bayar da shawarwari ga makaɗan
baka na Hausa, tun ma na yanzu da kuma masu tasowa ba, kan su dinga tattaunawa
da shirya zaɓaɓɓun kalmomi masu dacewa da matanonin waƙoƙin da suke aiwatarwa
da sadarwa ga al’umma.
Ya kamata kalmomin
da makaɗa suke zaɓowa suna jefawa a cikin waƙoƙinsu su dinga kasancewa suna
kallon shekaru ko muruwa ko tattaki ko ƙima na mutane waɗanda suke yi wa su.
Idan kuma aka daɗa
waiwayar nahiya ta sakamakon wannan bincike, za a nuna, akwai bukatar a yi wa
makaɗan baka tunasarwa da faɗakarwa a kan su dinga yin naciya da mayar da
hankali a wajen zaɓo maganganu ƙanana da manya, masu ma’ana da daidaito, masu kalami
na ƙarfafa kafaɗu na al’ummar Hausawa. Kada su dinga amfani da kalmomi na ɓatanci
ko kalmomi waɗanda za su tarwatsa Hausawa da Ƙasar Hausa da Arewa da Nijeriya
baki ɗaya.
Haƙiƙa, wajibi ne al’umma
ta mayar da hankali ta fuskar ba wa waƙoƙin baka da makaɗan baka matsayai da ƙimominsu
domin suna daga cikin masu riƙe da mutunci da samar da hanyoyi na nagartacciyar
rayuwa. Haka kuma akwai bukatar al’ummar ta dinga kauce wa biyar gwadabu na
masu sakin baki ko surutai barkatai babu na zaɓi. Daɗa makaɗan baka ne ko masu
yaɗa jita-jita.
Musulmi su dinga
tuna akwai sakamako da hukunci a bayan rayuwar nan ta duniya, a yayin da aka
mutu, aka tafi Barzahu da rayuwar ta lahira.
Dukkan waƙoƙin
baka na Hausa, ana son su zama nagartattu ba ballagazazzu ba, masu kwarjini da ƙima
da amfani ga al’ummar da ake yi su da ma sauran al’ummun duniya. Ta haka ne ya
dace cikin armasawa a dinga shiryawa da aiwatarwa da sadarwar waƙoƙin Hausa
bisa suluki da turba miƙaƙƙu. Daga nan kuma a tsare tare da kiyaye mutunci na ɗaiɗaikun
mutane, tun ma ba dattawa da tsofaffi da masu shekaru da auki ba, da kuma jumlatanin
jama’ar Hausawa da dukkan masu hulɗoɗi da su.
Makaɗan baka na
Hausa tun ma ba a yau ba, su lazimci sadar da waƙoƙinsu bisa muhallansu da
munasabobinsu na rukunonin jama’a mabambanta wato yara da matasa da matsakaita
da manya da tsofaffi da dattawa. Sannan da masu muƙamai da darajoji na ilimi da
na mulki da na dukiya ko na attajirci ko na sauransu. Har way au kuma su dinga ɗora
waƙoƙin nasu ta kallon jinsunan maza ko mata tare kuma da tantance nahiyoyi ƙimomi
ko mutuncin kowannensu.
A wata mahanga ta
wannan takarda kuma an lura makaɗan baka na Hausa ba su yi wa Ubangida tsoho
ko sabo, ko wanda suke yi wa waƙa ko da kuwa ta gayauna ce, zambo ko
habaici ko baƙar magana ko shaguɓe, ko arashi ko gugar
zana ko sauransu domin amana da fahimtar juna da mutunci da suke a
tsakaninsu[17].
Ya kamata iyayen
gida, manya da ƙanana, su daɗa fahimtar waɗannan hasloli kyakkyawa, waɗanda
makaɗan baka na dauri a al’ummar Hausawa suke biye da su, sannan su kwaɗaitu da
aiki da su a kowane hali da daɗi ko ba daɗi.
Alhamdu Lillahi
Rabbil-Alamina, was-salatu was-salamu ala Sayyidina Muhammadu, khatimul-ambiya’i
wal-mursalina, allazi ballagar-Risalata wa addal’amanata, sallallahu alaihi wa
sallama.
Muna yin addu’a ga
Allahu, tabaraka wa ta’ala, ya daɗa fahimtar da makaɗan baka na Hausa, su
kasance masu inganta tunaninsu da furucinsu na waƙa.
Muna roƙon Allah
ya fahimtar da mu kyawawan kalami da suke isarwa a gare mu, ya daɗa ɗaukaka
harshen Hausa, ya tsare shi, ya kiyaye shi daga kowane irin ɓata-gari.
Muna kuma ɗaga
hannuwanmu a sama, muna roƙon Allahu ya daidaita zukatanmu a yi masa ibada, ya
kuma daɗa mana ƙauna da so da bege ga Manzon Allah, cikamakin Manzanni da
Annabawa, ya kuma sanya mu a cetonsa a Ranar Mahshar. Ya Nabiyyul-lahi, Khatimil-Mursalina,
Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Alhamdu Lillahi.
MANAZARTA
Adamu,
M. T. (2015) Haihuwa da Suna a Bahaushiyar Al’ada. Kano: Salma-A’aref
Publishers.
Adamu,
M. T. (2018) Aure da Biki a Ƙasar Hausa. Kano: Ɗan Sarkin Kura
Publishers Limited.
Al-Buhari,
A. A. M. I. B. (?) Sahihul-Buhari.
Al-Nawawi,
M. Y. I. S. (1418AH) Hadisai Arba’in da Sharhinsu da Harshen
Hausa(Al-Arba’una Al-Nawawiyah), Riyadh: Al-Hamramaini Islamic Foundation
An-Nawawi,
A. Z. Y. S. (?) Arba’una Hadisan. Cairo: Maɗaba’ar Shu’unil-islamiyya.
Galadanci,
M. K. M. (1972) The Structure and Syntactic Function of Comound Noun in Hausa
in Anthropological Lingiustics no 14.4.
Galadanci,
M. K. M. (1976) An Introduction to Hausa Grammer. Lagos: Longman igeria.
Gora,
Y. C. (1989) Camfi a Al’ummar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu: Kano: Sashen
Koyar da Harsunan NIjeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau,
S. M. (1980/2002) Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Kaduna: Baraka Press and
Publishers Limited.
Gusau,
S. M. (1988) Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanayinsu, Musamman a Ƙasar
Sakkwato: Juzu’i na Ɗaya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero.
Gusau,
S. M. (1993-2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau,
S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau,
S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
Gusau,
S. M. (2011&2013) Adabin Hausa a Sauƙaƙe. Kano: Century Research and
Publishing Limited.
Gusau,
S. M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Biyu. Kano: Century
Research and Publishing Limited.
Gusau,
S. M. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau,
S. M. (2015) Abdu Karen Gusau. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
Gusau,
S. M. (2022) Bugaggun Littattafai da Wasu Maƙalu. Takardar da ya Gabatar. Kano:
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Gusau,
S. M. (2022) Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Shida. Kano: Commercial
Printing and Publishing.
Haɗejia,
M. S. . (2007) Hausawa da Al’adunsu. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Lawan,
U. M. (2021) Tsakure Cikin Al’adun Hausawa da Adabin Gargajiya. Kano:
Gidan Dabino Publishers.
Mu’assasar
Al-Balagh (1993). Haƙƙu Zawil Ƙurba. Iran: Islamic Republic of Iran.
Rufa’i,
M. K. (?) Aƙlul Muslim.
Sha’arawi,
M. M. (?) Manhajar Tarbiyya fil Islam. Masar, Cairo: Al-Ittihad al-Alim
Liɗalibi, Jamhuriyati Misra al-Arabiyya.
Tahir,
R. M. (2012) Ajamin Hausa don Ƙananan Makarantu. Kaduna: Yahaya Ɓentures, General
Printers and Publishers.
Yahya,
A. B., Ainu, H. A., Idris, Y. (2015) Sai Alu: Sharhi kan Waƙoƙin da aka yi
wa Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko (Sarkin Yamman Sakkwato). Kaduna: Ahmadu
Bello University Press Limited.
Yahya,
I. Y. (1971) Tatsuniya da Wasanni, Littafi na Biyar. Ibadan: Oɗford University Press.
Yahya,
I. Y. (1971) Tatsuniya da Wasanni, Littafi na Ɗaya. Ibadan: Oɗford University Press.
Yaro, A. (1994) Waiwaye a Al’adun Hausawa a kan Fulanin Yola. Kundin Digiri na Biyu: Kano: Sashen Koyar da Harsunan NIjeriya, Jami’ar Bayero.
RATAYE
HOTUNA
NA WASU MAKAƊAN HAUSA
NA
DA DA NA YAU
[1] Daga cikin ayyuka na S. M. Gusau,
akwai Gusau, S. M. (2002) da (2013a&b) da (2014) da (2017) da
(2018a&b) da (2021) bisa misalai. Akwai bukatar a sami dama a
nazarci waɗannan ayyuka domin su zama masu yin tuni da tunasarwa dangane da
usuli da bunƙasar waƙoƙin baka na Hausa.
[2] Ire-iren waɗannan abubuwa na samar
da amo ko sauti su ne ake ambata da kaya waɗanda ake yi ba don kiɗa ba, sai dai
akan gwama su da furuci na waƙar baka. Su ne kamar Tafunan Hannuwa ko ɗuwawu da
ake girgizawa su bayar da amo ko ƙirji da ake dokawa ko ƙafa ko ƙwarya ko
shantu ko duma ko tasa ko sauransu.
[3] Su ne ake kira kayan asali na kiɗa
da makaɗa suke rera waƙar baka ta Hausa. Sannan ba a yin wani abu ko wani aiki
da su sai kiɗa kawai. Su ne kamar kalangu ko ganga ko kuwaru ko kurya ko
tambari ko turu ko kanzagi ko sauransu.
[4] Kamar kotsaye na Fulani ko fiyano
da jita da kayan kiɗa na ɗakin sitidiyo da kayan kiɗa na band da sauransu.
Hausawa sun yi wa waɗannan kayan kiɗa halin hankaka mai mayar da ƙwan wani
nata.
[5] Amma duk da haka, wani Sarki ko
Sarakuna sukan nemi izini a wajen aminansu Sarakuna waɗanda wasu makaɗa suke
turke a wajensu domin su yi musu waƙoƙi a matsayi na gayauna.
[6] Zuwa wannan lokaci Hausawa sun
raya Masarautu a garuruwa da birane tare da nannaɗa musu Sarakuna masu
shugabantar gudanar da harkoki na zamantakewarsu.
[7] Daga nan ne kuwa makaɗan za su
waiwayi al’adun al’ummar Hausawa nagartattu, musamman waɗanda suke a cakuɗe da
hukunce-hukuncen addinin Musulunci. Kai tsaye kuma za su kula da matakan
tarbiyya da na kunya da alkunya, ba kuma tare da yaɗa fitsara ko batsa ko
alfasha ba. Su zamana masu faɗar gaskiya, masu kwatance na daidaito ba na kashi
ba domin su cim ma aƙiba kyakkyawa da sauka lafiya.
[8] Ko asaberi ko tabarma ko tsintsiya
ko kuma kitso da mata suke yi wa kawunansu.
[9] Waɗanda ake yi wa waƙa masu
alfarma ne ga makaɗan baka a kowane irin lokaci, kuma su mutunta ne makaɗan ne.
Wani hadisi yana nuna:’Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, kada ya ƙi shi ko ya
hantare shi’. Akwai kuma: ‘Musulmi ya so wa ɗan’uwansa abin da yake so wa
kansa’ (Al-Nawawi, M. Y. I. S. (1418H) Hadisi na 35 da Hadisi na 13).
[10] Abu ne mai matuƙar alfanu, a
kintsa furuci, a ajiye kwaɗayi ko roƙo a gefe. Wani abin waiwaye da ma waɗannan
abubuwa ba su cikin hasloli ko al’adu na Hausawa, kyawawa ko managarta. Sannan
ba su hau turbobi na addinin Musulunci ba.
[11] Ubangidan nan kuwa yana tare da
shi makaɗin alif-da-alif ko kuwa makaɗin ya daɗa samun wani Ubangida sabo dal.
[12] Manzon Rahama, tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi, ya ƙarfafa faɗar: Al-mumin Lil-mumin yashuddu
ba’adhu ba’adhan. Hadisi na 6026. Al-Buhari, A. A. M. I. B. (Sahihul-Buhari)
[13] Dubi wasu matanoni na diya na
barkwanci da yawa a waƙar ‘Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa’ ta Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa.
[14] Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji
Muhammadu Macciɗo wannan waƙa yana a riƙe da Sarautar Sarkin Kudun Sakkwato kafin
ya zama Sarkin Musulmi.
[15] Wato Mu’azu ƙanen Sa’idu Faru kuma
Wazirin Kiɗa, Daudun Kiɗan Kotso na Sa’idu Faru.
[16]Sa’idu Faru yana yi wa Sarkin Kudu
Macciɗo addu’a ya sami Sarautar Sarkin Musulmi, ya zama Amiral-Muminuna
na Nahiyar Nijeriya.
[17] Amma duk da haka, a wasu lokuta
makaɗan baka sukan yi furuci na ingiza-mai-kantu-ruwa, idan sun haƙƙaƙe ko sun
tabbatar Ubangida ba zai kintsu ba. Tare kuma da kyawawan maganganu na tarbiyya
da suke gaya masa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.