Ticker

6/recent/ticker-posts

Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero

Cite this article as: Lamido, I. & Garba, B. (2023). Makaɗan Hausa A Gombe: Tasirin Makaɗan Fada A Masarautar Buba Yero. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)1, 138-144. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i01.017.

Daga 

Ibrahim Lamido Ph.D

Sashen Koyar Da Harshe Da Harshe da Kimiyyar Harshe

Jami’ar Tarayya Ta KashereJihar Gombe

lamidoibrahim52@gmail.com
lamidoibrahim52@fukashere.edu.ng
07060777144

Da

Bashir Garba

Sashen Koyar da Ilmin Hausa
Kwalejin Ilmi ta Tarayya, PankshinJihar Plateau
sirbash02@gmail.com
08068004477

Tsakure

Hausawa mutane ne da aka san su da shiga lungu-lungu da saƙo-saƙo na yankunan maƙwabtansu na kusa da na nesa. Mutane ne da ke da sha’awar tafiye-tafiye don neman kyakkyawar matsuguni na samun ɗan abin tasarrufi na sa wa a bakin salati. A duk inda suka ya da zango sukan yi wa al’ummar da suka taras tasiri da harshensu da al’adunsu. Wannan takarda ta yi nazarin makaɗa da mawaƙan fada waɗanda suka kwararo jihar Gombe kuma suke rayuwa suna nishaxantar da masarautar ta Fulani da kaɗe-kadensu da waƙoƙinsu na fasaha da bushe-bushensu. An kuma kawo dalilai da suka haifar da zuwan Huasawa ƙasar Gombe da sabubban cuɗanyarsu da Fulani a Gombe. Takardar ta yi amfani da hanyar hira da masu ba da bayanai da kuma ajiyayyun takardu don tattara bayanai da suka taimaka wajen taskace nau’o’in makaɗa da mawaƙan Hausa da suke masarautar. Daga ciki, an kawo makaɗan taushi da na turu da na kotso da na ganga da na ruwa da kuma masu bushe-bushe. An yi bayanin waɗanda suka assasa kowane kiɗa a masarautar da inda suka fito da waɗanda suka gaje su, da kuma lokutan da suka fi gabatar da waƙoƙin nasu. Binciken ya gano akwai makaɗan Hausa maza da mata a fadar masarautar da suka shafi dukkan rukuni na mawaƙan da aka gabatar a nan sama. An kuma kawo ‘yan misalai na wasu ɗiyan waƙoƙin makaɗan. Binciken ya nuna yadda ‘ya’ya da jikoki da aka haifa a masarautar suka taimaka wajen gina al’ummar nan da aka fi sani da Hausa/Fulani wato narkewar al’adun al’ummu guda biyu waje ɗaya.

Kalmomin Fannu: Makaɗa, Mawaƙa, Tasiri, Gombe, Fada

1.0 Gabatarwa

Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da ake aiwatarwa don ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gudunmawa ta musamman. Kiɗa ta yi ruwa ta yi tsaki, ta durmuya sosai a cikin rayuwar Bahaushe ta fuskokin zamantakewa da sana’o’i da bukukuwa da lokacin shaƙatawa. Kaɗe-kaɗe da waƙoƙi suna nan cike fal da wasu ayyanannun mutane waɗanda aka fi sani da suna ‘Makaɗan Baka’. Wannan rukuni na jama’a sun bambanta da juna dangane da asalinsu da yanayin waƙoƙin da suke aiwatarwa da kayan kiɗan da suke amfani da su (Gusau 2005 p. vii). Makaɗan baka na Hausa mutane da aka san su da sana’ar yawace-yawace zuwa yankunan maƙwabta na nesa da na kusa suna taɓa sana’arsu ta kiɗa da waƙa (Lamido 2012 p. 14). Wannan bincike ya duba yadda ɗaya daga cikin nau’o’in makaɗan baka na Hausa suka yi tasiri a masarautar Fulani na Gombe wato makaɗan fada, waɗanda aka san su da shirya wa sarakuna da sarautun gargajiya kiɗa da waƙa suna yabon su da kakanninsu da ƙwarzanta su (Gusau 2003 p. 22). Wannan bincike yana da muhimmanci domin ya daɗa ƙarin haske a kan irin shaƙuwar Hausawa da Fulani musamman na Gombe da binciken ya shafa. Hakanan ya nuna yadda makaɗan Hausa suka zama kanwa uwar gami a al’adu da shagulgula na masarautar Bubayero a Gombe.

2.0 Taƙaitaccen tarihin masarautar Gombe

Masarautar Gombe ta samo asali ne daga jihadin jaddada musulunci da kafa shi da Shehu Usman Ɗanfodiyo ya ƙaddamar a ƙasar Hausa da maƙwabta ciki har da Gombe. Bubayero ɗan Usman ɗan Arxo Aliyu ɗan Arɗo Mamuda shi ya jagoranci jihadin a ƙasar Gombe da Jalingo Muri. Shi ne kuma ya kafa masarautar Gombe bayan jihadi. Jihadin wanda Bubayero ya ƙaddamar ya faro ne a shekara 1806 kuma ya ƙare ne a shekara ta 1841. Kodayake ‘yayansa biyu da suka gaje shi sun ci gaba da jihadin a yankin kudancin Gombe. Bubayero ya zauna a wurare da dama a lokacin jihadi kafin ya zarce zuwa yamma da Dukku da ke ƙaramar hukumar Dukku ta yanzu ya kafa cibiyar masarautarsa a wani wuri da ya raɗa wa suna Gombe kuma aka dawo ana kiran sa da suna Gombe Abba[1] bayan rasuwarsa (Abba 2004 p. 7-9). Bincike ya nuna tun a wannan cibiya ta masarautar wato Gombe Abba aka soma samun makaɗan Huasa daga Kano waɗanda suka soma kwararowa zuwa wannan sabuwar masarauta (Tukur 2003 p. 14).

A shekara ta 1913 zamanin Sarki Umaru, Turawan mulkin mallaka suka ɗage cibiyar daga Gombe Abba zuwa Nafaɗa a arewa maso gabas da Gombe Abba. Shekara shida bayan nan Turawa suka sake bai wa sarki Umaru Kwairanga umurnin sake ƙaura zuwa Gombe Doma cibiyar masarautr ta yanzu kenan. A nan ne aka gina wa sarki gida da masallaci da kotu da kurkuku da ofishin Mulki. Aka samar da kasuwa da makaranta. Wannan wuri da aka gyara asalinsa jejin al’ummar Fulanin Akko da Gona. Wannan wuri shi ya zama cibiyar masarautar Gombe a yau (Abubakar 2009 p. 14). Masarautar Gombe masarauta ce ta Fulani kasancewar Bubayero Bafulatani kuma masu riƙe da muƙaman sarauta galibinsu Fulani ne waɗanda tun a lokacin jihadi suka taho Gombe ƙungiya-ƙungiya suka taimaki Bubayero jihadi. Masarautar ta ƙunshi Fulanin Kiri Mbororo’en waɗanda suka fito daga yankin Borno don su taimaki Bubayero. Sai Fulani Janafula waɗanda ke zaune a duwatsun Lala da Hona da Ga’anda da Bira a ƙasar ta Gombe suna kiwo. Daga tsatsonsu ne Bubayero ya fito. Da akwai Fulanin Jada waɗanda ake kira da Fulɓe Kitaku waɗanda suka ƙaurato daga kudu maso yammacin Borni zuwa Gombe. Sai Fulani Tera waɗanda ake musu inkiya saboda zama da Terawa asalinsu daga Tarangara ce ta Marwa a ƙasar Kamaru daga can suka yiwo ƙaura zuwa Gombe ƙarƙashin jagoransu Arɗo Kaigama Buba Yele wanda Bubayero ya naɗa madakin Gombe (Tukur, 2003 p. 25). Saura sun haɗa da Fulanin Jera ƙarƙashin jagorancin Arɗo Aliyu daga Jaragol da Kubegasi. Shi ne Bubayero ya naɗa sarkin yaƙin Gombe. Sai Fulani Maga waɗanda suka fito daga Gulani a yammacin Biu ƙarƙashin jagorancin Arɗo Magi Buba Kari Banto wanda aka naɗa Kadin Gombe kuma tun daga lokacin zuriyarsa take riƙe da sarautar sarkin Magin Gombe. Saura sun haɗa da Fulani Walama waɗanda suka fito daga Shelleng bayan an kammala jihadi suka zauna tare da Bubayero a Gombe. Sai Fulani Daɓe waɗanda suka fito daga Dabema kusa da Shelleng tun a farkon jihadi suka taho Gombe. Sai Fulanin Gona waɗanda suke riƙe da sarautar Galadiman Gombe. Waɗannan bincike ya nuna suna zaune a Sumbe da Kalshingi tun kafin jihadi (Tukur 2003 p. 8).

Waɗannan su ne suka haɗu suka zama asalin Gombe kuma waɗanda suka kafa sarautu daban-daban a masarautar ta Gombe.

3.0 Cuɗanyar Hausawa da Fulanin Gombe

Lamido (2021 p. 151) ya bayyana cewa ƙaurace-ƙaurace da aka san al’ummar Hausawa da su zuwa yankunan maƙwabta na nesa da na kusa su ne silar cuɗanyar Hausawa da Fulanin Gombe. Hausawa mutane ne da aka san su da tasiri da harshensu da adabinsu da al’adunsu a kan duk al’ummun da suka tarar a duk inda suka ya da zango. Bisa ga wannan ɗabi’a Hausawa daga yankunan Kano da Zariya da Sakkwato da Zamfara da Haɗeja sun daɗe suna mu’amala da yankuna da dama na arewa maso gabashin Nijeriya waɗanda suka haɗa da Bauci da Gombe da Maiduguri da Yola da Jalingo Muri.

A Gombe Hausawa sun daɗe suna mu’amala da ƙabilu mazauna ƙasar Gombe tun a wajajen tsakiyar ƙarni na sha tara lokacin jihadin Bubayero da ‘ya’yansa. Dalilai da dama sun haifar da zuwan Hausawa da cuɗanyarsu da Fulani a masarautar. Daga ciki da akwai Hausawa waɗanda kasuwanci da sana’o’in gargajiya suka kawo su ƙasar. Da Hausawa masu yawon malanta tare da almajiransu suna zama suna ba da karatun Alƙur’ani. Da akwai masu dalilai na sha’awar sauya matsuguni da auratayya. Sai kuma masu yawon kiɗa da waƙa da masu roƙon baka waɗanda su ne suka shafi wannan bincike.

4.0 Dabarun gudanar da bincike

An yi amfani da hanyar hira da masu ba da bayanai waɗanda suka haɗa da masu riƙe da muƙaman gargajiya da makaɗa. A ciki an yi amfani da mutum 6 wajen tattaro muhimman bayanai. Baya ga haka an yi amfani da ajiyayyun bayanai a kundayen bincike da litattafai da kuma faya-fayen sauti da na bidiyo da aka taskace waƙoƙi don samun bayanai da za su taimaka wajen warware matsalar wannan bincike.

5.0 Kaɗe-Kaɗe da waƙoƙin Hausa a bukukuwan sarautar Gombe

A ƙarƙashin wannan an duba kaɗe-kaɗe da waƙoƙi da bushe-bushe na Hausawa da suka yi naso a shagulgula daban-daban na masarautar Gombe.

5.1 Kaɗe-Kaɗen Hausawa a bukukuwan fada na masarautar Gombe

Hausawa suna da kayan kiɗa da dama da nau’o’in makaɗa suke amfani da su a sana’arsu ta kiɗa da waƙa. Da akwai da dama daga cikin waɗannan nau’o’i na makaɗan Hausa a masarautar Gombe. Ga fitattu daga ciki:

5.1.1 Kiɗan ganga

Bincike ya nuna da ga cikin fitattun makaɗa da ake da su, da akwai makaɗan ganga waɗanda suke kiɗan ganga. A kiɗan ganga bayanai sun nuna sarkin kiɗa Barau Sani shi ya fara kiɗan ganga da waƙa tun a zamanin sarki Haruna Umaru Kwairanga. Daga bisani ɗansa Adamu Barau ya gaje shi. Tare da su a ƙungiyar tasu da akwai Muhammadu Masi Bateri wanda ke kaɗa gangar guiwa ya dawo kiɗan ganga. Waɗannan makaɗa suna kida da waƙa a lokacin hirar sarki jaance lamorde da ake yi a duk daren alhamis. Hakazalika suna kiɗa da waƙa a lokacin shagulgula na salla kumtal julde da na naɗin sarauta lamminki. Ga misalin taken da gangar ke kaɗawa:

“Ga bajimin dole ya ƙi garaje,

Jan damisa bai karɓi wasa ba”.

 5.1.2 Kiɗan turu

Kiɗan a turu a masarautar Gombe ya samo asali ne daga Ango da ɗan’uwansa waɗanda suka taho Gombe a zamanin sarki Abba wato Abubakar Umaru. Daga bisani ɗansa mai suna Muhammadu Ɗanbawa ya gaje shi da kiɗan kotso har ya zama Ɗanƙwairon Gombe. Makaɗan turu da kotso a ranar lahdi da kuma lokacin shagulgula na fada suke tasu nishaɗantarwar (Muhammad 2004 p. 24).

Ga tsakure daga waƙoƙin da suke yi wa Sarki Abba:

“Sai mu yi Gombe mu zo mu gano sarki,

In mun gan shi sa’a ta yi,

Ya ɗau zuriya duka har da bayi,

Ya ɗauke makafi da guragu,

Bai bar su da sha’awar komi ba.

 

Amshi: “Abba uban Sule mai sulken daga ɗan Umaru,

Bana mun yi zama mun sha daɗi,

Mun sami fura mai nono,

Mun ɗebi tuwo mai nama,

Sai ga fa hatsina na zaman birni,

Goron da ake kai wa maroƙa,

Ɗan Umaru Habu yab bayar,

Tilas ake gode wa sarki,

Bai bar mu da sha’awar komi ba….”

(Hira da Makaɗa Ahmadu).

5.1.3 Kiɗan kotso

Fitaccen makaɗin kotso shi ne Muhammadu Mai Lili da jama’arsa waɗanda suka fito daga wani ƙauye mai suna Dole a ƙasar Zamfara. Bayanai sun nuna dalilin zuwansa ziyara ce ya kawo dutsen Bima wanda ke da tarihi matuƙa. A wannan ziyara tasa ce ya yi wa sarki Abba waƙa. Daga nan ne mai martaba sarki ya ba shi masauki tsawon wata shida bai sallame shi ba. A lokacin ne ya yi wata waƙa da ya yi wa laƙabi ‘baƙo raɓa’ waƙar da ta ba shi damar komawa garinsu bayan sun yi yarjejeniya da sarki a kan zai dawo Gombe. Bayan ya koma gida ne ya sake shiri tsaf ya dawo Gombe shi da iyalansa inda ya zauna ƙarƙashin sarki yana kiɗa da waƙa. Ga misalan waƙoƙinsa:

Jagora: “Halin Umaru na nan ba mu san magani ba,

Amshi: Yana gaba da maza ko can Habu gobe shiri nai yai.

 

Jagora: Yana gaba da maza ko can, Habu goma shiri nai yai,

Halin Umaru na na nan gurin Abba bai ya da sakewa ba.

Audu kyauta ikon Allah.

Amshi: Alhaji kyauta sai jabbaru, Allah kyauta sai Garba,

Sa mutum yai magana shi ɗai.

 

Jagora: mu ɗau kunkuru mu ba shi horo,

Amshi: Mutum in ya datta sai dai ka ji wai wai.”

Ban da sarki Abba Mailili ya yi wa Sarki Shehu waƙoƙi. Ga misali:

“Sarki Shehu kasuwa tai ta cika,

Runhuna suna hushin banza,

Yau zai ba ka gobe zai ba ka.

Rakiya/Amshi: kai wanga mai hushin ba ka yin komai,

Kai wanga mai hushi ba ka yin komai,

In ka tuna amshi dai ya fi”.

(Waƙoƙin Mailili a Faifan CD).

Daga bisani Makaɗa Mailili ya ƙaura ya koma fadar Yariman Gombe hakimin Funakaye bisa umurnin sarki Abba inda ya ci gaba da kiɗa da waƙa. Ga misali daga wata waƙarsa ga Yarima:

Jagora: “Dogon munafuki da gajere,

Ba su aikata alheri sai sharri,

Ga su zamne ga fili,

Sai ko ukkunsu ga shi bahili,

Tun ga duniya Allah ya nuna ba ya tare da kowa.

Amshi: Ya gyara duniya ɗan Mamman

Ɗan Abba maza jiran wasu maza”

(Hira da Ndotti Yayari).

5.1.4 Kiɗan taushi

Wanda ya fara kiɗan taushi a masarautar Gombe shi ne Ɗandabu mai taushi. Yana kiɗa tare da yaransa yana yi wa sarki kiɗa da waƙa a duk daren Lahdi da kuma lokacin biki da shagulgula na fada. Ga misali daga waƙoƙinsa:

Jagora: “Idan sarki yai ɗamara haka kowa sai ya yi tunziri.

Amshi: saboda ƙarfin Allah aka zama mai gayyar doki,

Na Umaru ba ka taruwa mai gayyar doki.

 

Jagora: ga can sarki ya fito.

Amshi: Abba hauni nai ba ka taruwa mai gayyar doki na Umaru gurin daga ba ka taruwa.

 

Jagora: Abba ba a yi ma reni.

Amshi: Ga ka mutum na san ba shi yiwa mai gayyar doki.

(Waƙoƙin Ɗandabu a Faifan Audio CD)

A fadar Yariman Gombe da ke Bajoga Gundumar Funakaye kuwa, da akwai Mai Damma mai taushi wanda ke yi wa Yariman Gombe kiɗa da waƙa a duk daren jumma’a. Ga misali daga waƙoƙinsa:

Jagora: “Mamman ka wuce hasada,

Ba yalwa jikan kasaƙi,

Ingarma ya fi ƙuru ga komai,

In ga karaga a ɗauke gado,

In ga taliya ba ya cin wake,

In ga sulei, ahu ba ta kar na yi ba…”

(Hira da Jaɓɓo Dawaki)

5.1.5 Kiɗan jauje

Kiɗan Jauje ya samo asali ne tun a lokacin jihadin Bubayero. Wanda ya fara kawo kiɗan jauje masarautar Gombe shi ne sarkin jauje Bawa. Daga shi sai sarkin jauje Adamu wanda ya taho Gombe zamanin sarki Haruna Umaru, ɗansa Muhammadu ya gaje shi ynna da masu masa amshi kamar Tijani Garba da Bala Isa da sauransu. Makaɗan jauje suna kiɗansu a duk daren Jumma’a a fada. Ban da waɗannan da akwai makaɗa Adamu wanda masarautar ke tare da shi tun a Gombe Abba. Da shi aka yi ƙaura zuwa Nafaɗa zuwa Gombe Doma. Ɗansa Ibrahim shi ne ya gaje shi a yanzu a matsayin Tamburan sarrkin Gombe yana da masu masa amshi mutum tara waɗanda suka haɗa da: Alkalin Tambari da sanƙiran tambari da wazirin tambari da Muhammadu madakin marafan tambari. Su ma suna tasu hirar sarki duk daren alhamis suna kiɗa da waƙa suna yabon sarki.

Shi ma Sarkin Jauje Salihu yana yi wa Yariman Gombe Muhammadu Mazadu kiɗa da waƙa yana yabon sa. Ga misali:

“Mamman a kau da kara, a kau da kararuwa,

Guma-gumai sun kama wuta,

Yarima kai ne ba su ne ba,

A gidan na Abdu ke duniya,

Kowa ya zo ya sha”

(Hira da Ndotti Yayari)

5.1.6 Kiɗan tambari a fadar Mai Martaba Sarkin Gombe

Kiɗan tambari kiɗa ne wanda ake yi tun daga jajiberin sallah ƙarama. Zuwa washegari ranar salla. Akwai makaɗan tambura waɗanda suke kaɗe-kaɗe tun daren salla har a washegari a je idi a dawo da kuma lokacin karɓar gaisuwar salla da sarki yake a fadarsa. Al’adar masarautar Gombe ce da washegarin salla, hakimai da masu riƙe da muƙaman fada da zuriya-zuriya na masarautar sukan zo su yi wa sarki gaisuwar salla. To, a wannan lokaci fada takan cika da makaɗa irir-iri daban-daban waɗanda suke gocewa da kiɗa da waƙa. Masu tambura ma wannnn shi ne lokacinsu. Sukan yi ta kaɗe-kaɗe suna yabon sarki da kaknninsa da irin bajintar da suka yi a tarihin masarautar. Daga cikin fitattun makaɗan tambura da akwai: Tambari Kawu na Sani wanda shi ne makaɗi na farko da ya yi zamani da Sarki Umaru Kwairanga da ‘ya’yansa Sarki Haruna da sarki Abba. Sai Tambari Babagana wanda ya yi zamani da Sarki Abubakar. ‘ya’yansa daga baya suka ɗauka suna kaɗa tambarin musamman lokacin shagulgulan salla babba da ƙarama. Kiɗan tambari ya fantsama har a fadar mai martaba Yeriman Gombe hakimin Funakaye[2]. Makaɗa Audu Tambari shi ya fara kaɗa tambari a fadar Yerima da ke Bajoga daga baya ‘yan’yan ‘yan’uwansa suka karɓa suka ci gaba da yi. Ga kaɗan daga cikin waƙar Sarki Shehu da Ibrahim tamburan sarki ya masa:

“Dole a bi ka

Gombawa Shehu mai raba kaya

Shehu uban sarakuna dodo

Babban barde shehu mai raba kaya

Giwa duk naka ne mahe

Gabasawa naka ne dodo.”

(Hira da Ardo Chindo Abubakar)

5.1.7 Makaɗan Ruwa

Waɗannan su ne makaɗa masu amfani da ƙwarya da ruwa a matsayin kayan kiɗa da shi suke gamawa su samar da kiɗa a waƙoƙinsu. Daga ciki da akwai Hajiya Fatsuma zabiyar sarki ‘yar Alin Kano. Iyayenta suna kiɗan kotso, amma ita garwa take amfani da shi da kiɗan ruwa. Tana da ‘yan amshi kuma masu mata kiɗa da suka haɗa da Fanta da Yarima da Mama da Gambo da Lami da Iya Falmata. Ga kaɗan daga cikin waƙoƙin da take yi wa sarki Shehu a lokacin bikin salla:

“Ya yi halin girma ya bi da maza ɗan Garba,

Gagarau ka daɗe makayen gidan Kwairanga,

Ya yi halin girma ya buwayi maza ɗan Garba,

Ɗan Garba mai rabo da yawa makayen gidan Kwairanga,

Giwa lafiya ka wanye da lafiya raba kaya,

Giwa ɗan Hassan na Haruna ka wanye lafiya uban Baraya,

Komi girman barewa watarana a hannun mai dawa za ta kwana”

(GLGIU, Video Cassette Record).

Ban da Hajiya Fatsuma, da akwai Hajiya Amina Yebe Bafulatana wadda ta fara waƙa kimanin shekara talatin da suka wuce. Tana da ‘yan amshi da makaɗa da suka haxa da: ‘Yar Kwando da Jummai da Kaltume. Ga kaɗan daga cikin waƙoƙinta:

“Ya fi tantama raba musu sa maza ladaf Baba,

Mai sulke da bindiga ka gama lafiya da Turawa,

Ai ba don kuwaraba bana sai mun gama da Turawa

Baba uban aku, uban jimin har da dawaki ba gaba.”

(GLGIU, Video Cassette Record).

Akwai Hajiya Intabe wada ta taho Gombe ta hannun Garkuwa. Tana yi wasa sarki kiɗa da waƙa tare da ‘yan amshinta a lokacin bukukuwan salla da wasu shagulgula na fada. Ga kaɗan daga cikin waƙoƙinta da take yi wa Yeriman Gombe Abdulƙadir Abubakar:

“Damo sarkin haƙuri,

Hankaka mai da ɗan wani naka,

Abdulƙadir mai Gombawa,

Na Shehu mai Gombawa,

Ɗan Abubakar da Haruna,

Hadari malafar duniya,

Zauna gari na Shehu,

Zamaninka ban ga talauci ba,

Allah ya ja kwana……

(Hira da Ɗantima).

5.2 Bushe-Bushen Hausawa a masarautar Gombe

Ban da kaɗe-kaɗe da akwai bushe-bushe waɗanda ke amfani da kayan busa na Hausawa a fadar mai martaba sarki. Daga ciki da akwai:

5.2.1 Masu busa kakaki

Masu kakaki su ne waɗanda suke nishaxantar da sarki a duk daren Jumma’a da busar kakaki. Malam Abubakar Adamu shi ne ya fara busa kakaki a masarautar a shekara ta 1930 zamanin sarki Haruna. Yana busa kakaki da shi da ‘ya’yansa. Ga kaɗan daga cikin taken da yake busawa:

“Allah babban sarki,

Sarki magajin sarki,

Kakanka ma sarki

Ina maka fata ka daɗe a duniya

Cikin sarari babban baƙo

Ga bajimin sarki

Wasa da dariya ta fi dukiya

Don dukiya takan ƙare

Zakin sarakuna

Kada ka sake da duniya

Kada ka sake da lahira

Daɗa haƙuri kan haƙuri

Mai haƙuri yana tare da Allah”

(GLGIU, Video Cassette Record).

5.2.2 Masu busa algaita

Waxanda suke a sahun farko cikin masu busa algaita shi ne Adamu sarkiin algaita. Bayanai sun nuna shi ne ya fara zuwa da algaita a zamanin Sarki Haruna. ‘Ya’yansa Haruna Baƙoji da Sule suka gaje shi suna busa algaita a fada a ranar jumma’a. Busar tana tafiya da kiɗa, in busa ta canja, sai kiƙa ma ta canja. Ga misali daga taken da suke busawa:

“Ga bajimin dole,

Amma ya ƙi garaje

Ga shi a sarari,

Hattara cigarin raba kaya”.

(Hira da Arɗo Chindo Abubakar).

6.0 Sakamakon bincike

Wannan bincike ya nuna yadda aka samu malalar makaɗan Hausa a ƙasar Gombe musamman ma makaɗan sarauta. Bincike ya nuna yadda aka samu nau’i na makaɗan Hausa da suka haɗa da makaɗan ganga da na kotso da na tabshi da na turu da na ruwa. Ban da waɗannan an ga masu bushe-bushe waɗanda suka darara a masarautar da nasu kayan bushe-bushen da suka haɗa da kakaki da algaita. Akwai alamu da ke nuna Fulani ba su san waɗannan nau’o’in kaɗe-kaɗe ba sai da suka haɗu da makaɗan Hausa. Kafin zamanin Muhammadu Kwairanga, masarautar Gombe ba ta san waɗannan kaɗe-kaɗe ba, sai a lokacin da su makaɗan suka riƙa kwararowa daga yankunan ƙasar Hausa zuwa Gombe. Binciken ya nuna yawancin waɗannan makaɗa Huasawa sun fito ne daga ƙasar Kano Zamfara da Katsina. Hakazalika makaɗa ne da suka ƙunshi maza da mata waɗanda suka taho Gombe a mabambantan lokuta. Wasu ma daga cikinsu a nan iyaye suka haife su suka tashi suka gaji kiɗa da waƙa a hannun iyayen nasu. Su waɗannan ba su san ko’ina ba ban da Gombe. Wannan na nuna yadda makaɗan Hausa suka malala a ƙasar Gombe kuma suka yi shuhura da sana’arsu ta kiɗa da waƙa. A yau da makaɗa da dama da ke ganin Gombe gida ne saboda nan suka tashi kuma suke ci gaba da raya gadon gidajensu da suka samu daga iyaye da kakanninsu. Kuma da su ne ake daɗa samun yalwar al’ummar nan da aka fi sani da suna Hausa/Fulani.

7.0 Kammalawa

Wannan bincike ya yi nazarin makaɗa da mawaƙa da suke warwatse a ƙasar Gombe msuamman makaɗan fada. An kawo nau’o’in makaɗa da aka yi bayaninsu dangane da irin kayan kiɗan da suke amfani da su a waƙoƙinsu. Daga ciki, an yi bayanin makaɗa da masu bushe-bushe. An kuma kawo ‘yan misalai waɗanda suka ƙunshi tsakure daga waƙoƙin nasu. Binciken har wa yau ya yi bayani a taƙaice wuraren da suka fito da silar zuwansu Gombe da yadda suka tare suna kiɗa da waƙa a Gombe. Hakazalika an ga yadda wasu daga cikin makaɗan ‘ya’ya ne da jikoki na makaɗan farko da suka taho waɗanda Gombe ta zama musu gida kuma suke rayuwa suna kiɗa da waƙa. Waɗannan makaɗa saboda auratayya da Fulani da suka yi yanzu sun narke sun zama al’ummar na da ake kira da Hausa/Fulani.

Manazarta

1.       Abdullahi, A. (2019). “Nazarin Waƙoƙin Malam Muhammadu Mailili na Marigayi Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usman Abubakar”. Kundin Digiri na Ɗaya Wanda Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsuna, Jami’ar Tarayya ta Kashere, Jihar Gombe.

2.       Gombe Local Government Information Unit. Gombe Eid El Fitr Celebration Record (1990). VHS Cassette.

3.       Gombe Local Government Information Unit. Gombe Eid El Fitr Celebration Record. (1994). VHS Cassette.

4.       Gombe Local Government Information Unit. Gombe Eid El Fitr Celebration Record. (1996). VHS Cassette.

5.       Lamido, I. (2012). “Tasirin Adabin Hausa a Al’adun Fulanin Gombe”. Kundin Digiri na Biyu Wanda Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

6.       Muhammad, Y.J. (2004). “Nazarin Waƙoƙin Ɗanbawa Ɗanqwairon Gombe”. Kundin Digiri na Ɗaya Wanda Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

7.       Tukur, A. (2003). “History of Gombe”. Unpublished History of Gombe Emirate. Waƙoƙin Wasu Makaɗan Fada a faya-fayen Audio CD.



[1] Bubayero ya raɗa wa wannan wuri suna Gombe daga sunan wata bishiya da Bolawa mazauna ƙauyukan kewaye suke kira da yarensu ‘Gombe Memosiri’. Amma wasu sun ce suna Gombe daga sunan asalin garin da kakanninsa suka taso a ƙasar Mali ne, wato Dagombe. An ci gaba da kiran wurin da suna Gombe Abba bayan rasuwarsa wato Gomben Abba. Abba taƙaitaccen suna ne da ke nufin Abubakar wanda shi ne cikakken sunan Bubayero. Wato Gomben da Abba ya kafa.

[2] Yeriman Gombe Muhammadu Kwairanga ya zama sarkin yanka bayan da aka xaga gundumar Funakaye ta koma masarauta a shekara ta 2001.

Post a Comment

0 Comments