Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo Asirin WaKa na Farfesa Abdullahi Bayero Yahya [01 - Shafukan Farko]

Salo Asirin Waƙa
Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa
 

GODIYA 

Dukkan godiya tabbata ga Allah maɗaukanki. Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammadu (SAW) fiyayyen talikai wanda aka aiko da mafifincin zance domin shiryarwa ga tafarki madaidaici, da alayensa da sahabbansa da masu biyar sa har zuwa ranar sakamakon, amin

Mahaifina da malamaina da kuma ɗalibaina (musamman na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto), duk sun taimaka ainun ga ba ni ƙwarin guiwa wajen fahimta da sha’awar waƙa. Ina godiya gare su ƙwarai. Daga cikin malamaina akwai Farfesa M.K.M Galadanci da Farfesa Abdulkadir Ɗangambo da Farfesa Ɗalhatu Muhammad: biyu na farko a Jami’ar Bayero, Kano, ɗaya kuma na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Waɗannan su ne kan gaba ga zamowa musabbabin samuwar duk wani abin yabo da za a iya gani cikin rubuce-rubucena. Na ‘tir’ ko na ‘ai sha’ani’, kuwa su kam tasiri ne na daƙilata

Kudurin rubuta wannan littafi, Salo Asirin Waƙa, ya zo mini ne a shekarar 1988 bayan na rubuta wata maƙala da ta shafi dangantakar waƙoƙin baka na sarauta da kuma takwarorinsu rubutattu na Hausa ta fuskar ƙananaan jigoginsu. To amma wannan ƙudurin bai ƙarfafa ba sai a shekarar 1998 lokacin da na sake samun damar rubuta wata maƙala mai taken ‘Siffantawa Bazar Mawaƙa: wani Shako A Cikin Nazarin Waƙa’. A lokacin ne ɗalibaina na Jami’ar Usmanu

Ɗanfodiyo suka nemi in rubuta musu wani littafi da ke iya yi musu jagora ga nazarin salon waƙoƙin Hausa. Haka kuma bayan littafin farko da na rubuta, Jigon Nazarin Waƙa, ya fito a 1997 sai magajina mai ƙaunata matuƙa, Yahya Ahmad, ya ce min to saura littafi a kan salo. Nan take na shiga tunani, ina kuma tuntuɓar sa. Shi ne ya tsayar min da sunan Salo Asirin Waƙa. Allah ya saka masa da mafificin alheri, amin.

Bayan ‘yan shekaru da rubuta Salo Asirin Waƙa da kuma ƙarewar yawansa da aka buga, sai kira daga malamai da ɗalibai ya yi ta zuwa na a sake buga Salo Asirin Waƙa. Waɗannan kira-kiraye sun ƙara nuna min muhimmancin littafin. Haka kuma saboda sanin cewa salo wani kandami ne cikin nazarin waƙa sai wani tunani ya zo min na cewa ya kamata in faɗaɗa Salo Asirin Waƙa. Waɗannan dalilai su suka haifar da wannan sabon bugu na littafin. Ina godiya ga dukkan malaman Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. Daga cikinsu akwai musamman Farfesa Ibrahim A. Mukoshy da Farfesa Atiku A. Dunfawa da Dokta Bello Bala Usman da Dokta Ibrahim S S Abdullahi da Dokta Yakubu A. Gobir. Haka nan kuma akwai Dokta A.A. Atuwo da Dokta A. S. Gulbi da Dokta U.A. Bunza da Dokta Yahaya Idris da kuma Malam Dano Balarabe Bunza. A Cibiyar Nazarin Hausa akwai Dokta Hamza A. Ainu da Malami Ƙasarawa.

Mamman Alhaji Mariga, gwanin na’urar komfuta, ya yi rawar da ta shere ni, saboda shi ne duk da ɗalibcin da yake yi, ya yi komi don ya ga cewa na’urar ta fahimci irin Hausata da bukatuna,. Allah ya saka ma da alheri, ya yi ma albarka duniya da Lahira, amin.

Zana sunayen waɗanda suka yi ruwa ko suka yi tsaki don su ga na rubuta Salo Asirin Waƙa, ko bayyana godiyar da ta dace da abin da suka yi, kuma a cikin salon da ya dace da godiyar, aiki ne mai dibilwa ga bamin baharin lugga irina.

 Ina miƙa godiyata mai ɗimbin yawa ga dukkan iyalina saboda fahimta da juriya cuɗe da ƙauna da suka nuna min lokacin da nake cikin ‘gurbin’ Salo Asirin Waƙa.

Alhamdulillahi wa sallallahu ala man la nabiyya ba’adahu, amin.

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto
Maris 2016.

GODIYA TA MUSAMMAN

Ina miƙa miƙa kyakkyawar godiyata ga shugabana, mai ƙauna ta, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Sarkin Yamman Sakkwato, kuma Gwamnan Jihar Sakkwato daga 2007 zuwa 2015.

Sanata Aliyu mutum ne mai sha’awar waƙoƙin Hausa ainun. Haka kuma ya kasance mai nuna sha’awarsa kan rubuce-rubucena da son ya tattauna da ni kan waƙa. A kan haka ne da na faɗa masa cewa ina nan ina ƙoƙarin in faɗaɗa ɗaya daga cikin littattafan da na rubuta, wato Salo Asirin Waƙa, sai ya kada baki nan take ya ce zai ɗauki nauyin bugawa.

Lokacin da na kammala sai ya yi min abin da Musa Ɗanƙwairo ya ce ma Sardaunan Sakkwato kan kyautar da ya yi masa, wato, /Sardauna ya yi min kyauta/wani gari ya hi gaban kunu/. To ni da ko a bugawar farko sai da ni da abokai aka ƙuƙuta sannan aka buga yawan littafin guda ɗari biyar kuma mai bangon takarda, sai ga shi Sanata Aliyu Magatakarda ya ce a buga guda dubu kuma duk da bangon makari, ba takarda ba!!! Lalle na ƙara da abin da magajina Haliru Wurno ya ce saboda kyautar da wani ƙanensa ya sha yi masa, inda ya ce,

14. Babban bajini Bello ƙane ka zama wana
Haskenmu ɗiyan Baba ina son ka ga raina
Na Abbas bahagon Manuga walla maɗi na
Ba don asuli wanga da yah hau bisa kaina
Tabshi nika yo ma na kiɗi za ni kiɗawa

Lalle ni kam sai dai in yi shuru /ina kallo/. Allah Maɗaukakin Sarki ya saka wa wannan bawan Allah da mafificin alheri a duniya da lahira, amin ya Rabbal alamina.

Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto
Mayu 2016.


MUƘADDIMA

SALO, wani daji ne na nazari, mai surƙuƙi, mai duhuwa wanda ya ƙunshi dabaru ko hanyoyi waɗanda a kan bi ta kansu a tsara wani abu. Salo a waƙa ya fuskanci zaɓin da marubuci ya yi amfani da shi wajen shiryawa da tsara waƙarsa daga farakonta zuwa ƙarshenta. Ashe ke nan, salo na iya zama hanyar gudanar da abu, wato furuci ko rubutu. Sannan kuma abubuwan da aka yi amfani da su wajen ƙawata furuci ko rubutu, salo ne, kuma da su ne ake adonta harshen da ake amfani da shi. Hikimomi da hanyoyin kaifafa zance ko ma’ana da bayyana hoton abubuwa da zayyana da kwalliya da amfani da dabarun sarrafa harshe da sauransu, duka abubuwa ne masu tallafa ayyana salo a furuci ko rubutu. Tun a wajejen 1973, manazarta da masana ilimin waƙa suka fara samar da ayyuka don inganta tsarin koyarwa da nazarin waƙa. Cibiyar nazarin Harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero Kano a 1973 ta shirya wani taro inda aka fara samar da wasu kalmomin nazari cikin Hausa. Furofesa Ɗalhatu Muhammad ya tace waɗannan kalmomi a wata takarda wadda aka buga a cikin Mujallar Harsunan Nijeriya III da sunan ‘A Vocabulary of Literary Terms in Hausa’. Har wa yau kuma a shekarar 1982, NERDC ta ɗauki nauyin wani taro don a samar da keɓaɓɓun kalmomi na nazarin harshe da adabi. Furofesa Ɗalhatu Muhammad shi ne ya tace wannan aiki, aka kuma sa masa suna Hausa Metalaugage, ‘Ƙamus Na Keɓaɓɓun Kalmomi’, sannan aka buga shi a 1990. Daga nan kuma an sami daya dayan malamai da manazarta waɗanda suka gabatarda maƙalu da littattafai game da hanyoyin da matakan nazarin waƙa rubutacciya ko ta baka. Alal misali, Ɗangambo (1981) ya gabatar da maƙala mai suna, “Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa”, a tsakanin 1977/1979 CNHN ta yi wani shin wanda sakamakonsa ya zama littafi mai suna Waƙa A Bakin Mai Ita 1x2. Haka kuma Gusau (1983) ya gabatar da littafi mai suna Jagorar Nazarin Waƙar Baka, inda Yahya (1997) shi ma ya fito da wani littafin mai suna ‘Jigon Nazarin Waƙa. Wannan littafi, Salo Asirin Waƙa, shi ne irin sa na farko da aka fara rubutawa, inda a nazarin waƙa za a ɗauki wani fanni ɗaya afaɗaɗa tsokaci a kansa. Wannan littafi ya ƙunshi tsagwaron nazari ne a game da salo da nau’o’insa da sigoginsa kamar yadda yake bayyana a waƙoƙin Hausa rubutattu ko na baka. Marubucin ya yi ƙoƙarin ya bayyana dabarun jawo hankali ta fuskar aiwatar da harshe da kuma yi masa ado tare da yin misalai da kafa hujjoji daga tsakuren baitoci da ɗiya na waƙoƙin Hausa.

Haƙiƙa, an nuna naƙaltar harshe a wajen zaɓo kalmomin da aka yi amfani da su wajen zubin wannan littafi. Tun da farko, dubi kalmomin da aka shirya suka tashi sunan littafin, Salo Asirin Waƙa, wannan ya nuna akwai fahimta da sanin makamar rubutu a wajen mawallafin wannan littafi. Na lura likita Abdullahi Bayero Yahya ya tsara littafin nan nasa bisa manyan babobi guda uku waɗanda suka haɗa da ma’anar salo da wasu muhimman abubuwa guda takwas da

suka shafi tubalan gina salo a waƙa. Sai kuma ya fito da wasu hanyoyi guda goma waɗanda suke tabbatar da muhimmancin salo a waƙa. Har wa yau kuma marubucin ya yi tsokaci a kan wasu salailai da yadda suke ɓullowa a waƙoƙin Hausa. Ya yi magana kan muhimman nau’o’in salo da suka haɗa da salon siffantawa wanda a wajen mawallafin ya ƙunshi kinaya da kamance da jinsarwa da zayyana da kuma alamtarwa. Marubucin kuma ya yi bayani a kan salon gamin bauta da salon kambamawa da gangara da saɓi-zarce da lalurar waƙa da dibilwa da hira da labari da kuma shillo. Wannan ita ce muhimmiyar ƙunshiyar wannan littafi, amma an yi wa littafin mabuɗi da godiya da sadaukarwa, sannan an rufe shi ta kawo jelar wasu kalmomin fannu da kuma manazarta.

Bisa dukkan fahimta, wannan littafi zai yi matuƙar agaza wa masu nazarin waƙa a matakai daban-daban, musamman a manyan fagage na neman ilimin Hausa. ina taya Likita Abdullahi Bayero Yahya murna dangane da wannan damar da ya sake samu ta ƙara wa rumbun nazarin waƙoƙin Hausa yawa. Allah Ya daɗa taimaka masa wajen ƙara samun ƙaimi da himmatawa a cikin bincike-bincike.

Da ma na san gogan nawa ba barci ya dame shi ba, Himma ba ta ga raggo!

Alhamis 22 ga Maris 2001
Dr Sa ‘Idu, Muhammad Gusau
Sashin Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano

 

MUƘADDIMA TA BIYU

Alhamdulillahi! Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da ganin sabon bugu na SALO ASIRIN WAƘA ya fito. Ina ƙara murna da ganin cewa Babban Gogana ya faɗaɗa littafin. Wannan ya ƙara fitowa a fili ya nuna cewa salo ‘wani daji ne na nazari, mai surƙuƙi, mai duhuwa…’, kamar kuma yadda marubucin ya faɗa cewa, ‘ba ya yiwuwa a iya ƙididdige ire-iren salo’.

Na bukaci marubucin da ya sake buga muƙaddimar da na rubuta kan fitowar farko saboda duk abin da ta ƙunsa dangane da muhimmancin littafin yana nan bai kau ba a wannan sabon bugu.

Allah ya sa wannan littafi ya ƙara amfanin jama’a, ya kuma ƙara buɗa basirar marubucin, amin.

 Alhamis 7 ga Mayu 2016
Farfesa Sa ‘Idu, Muhammad Gusau
Sashin Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.

 

ALLAH SAM BARKA

Bismillahir Rahmanir Rahim. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga AnnabinSa, Muhammadu, mafificin talikai, da Sahabbansa da mabiyansa har zuwa Ranar sakamako, amin.

Bayan haka ina farin ciki da ganin littafin ɗan uwana Abdullahi Bayero Yahya ya sake fitowa. Abin ƙarin sha’awa shi ne, ya faɗaɗa shi tare da bayani dalla-dalla kamar yadda ya saba yi. Alhamdulillahi.

Harshen gida gimshiƙi ne wanda da shi ne ake samun a kawo ci gaban ƙasa mai inganci. Da shi ne ƙasashen da suka ci gaba suka tsere wa sauran ƙasashe. Haka kuma bunƙasa rubuce-rubuce kan al’adun al’umma cikin harshensu na gida, shi ke ɗaukaka harshen ya kuma kare al’adunta daga salwanta. Saboda haka ya dace duk mai kishin ƙasa ya ba da gwargwadon tasa gudunmawa ta wannan fuska.

Salo Asirin Waƙa littafi ne da ke ƙoƙarin bayyana wa matasa tarin hikimomin da waƙoƙin Hausa suka ƙumsa, ya kuma taskace al’adummu. Rashin ire-iren wannan aiki tattare da yawaita rubuce-rubuce cikin harsunan baƙi a kan al’adummu kamar waƙoƙin Hausa, ƙoƙari ne na bunƙasa adabin waɗannan baƙi, da kuma dallashe na gida.

 

Allah ya sa mu fahimta, ya ƙara buɗa basirar Bayero da sauran manazarta, ya sa kuma wannan littafi, Salo Asirin Waƙa, ya ci gaba da amfanin ɗalibai da manazarta da al’umma gaba ɗaya, amin.

 


Sanata Aliyu Magatarda Wamakko
Sarkin Yamman Sakkwato
Mayu, 2016.

Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa


Post a Comment

0 Comments