Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗan Sha’aibu ALU 1 - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

 Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

Kirari: Allah damar Sulɗani,

 Malikal ma mulki,

 Allah ba birni garai ba,

 Ba shi da ƙauye,

 Bawan Allah an duk inda,

 Kai yi bawan Allah

 Tsawa canjin gararinki ya sa

 Dare bare jan kura

 Alhaji ɗan Sha’aibu Tungar Rini,

 Sarki baƙon sarakunan Musulunci

 

Yara: Gwamnan Sakkwato mai Adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci.

 

Jagora: In ka tashi zuwa na tashi,

Yara: In ko ba ka zuwa na fasa.

 

Jagora: In ka tashi zuwa na tashi,

Yara: In ko ba ka zuwa na fasa,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 An ce kana ta rabon motoci,

 An ce kana ta rabon mashukka,

 Ga Ɗan Shaaibu na Tungar Rini,

 Ko ta ya a maƙa min nikan.

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci.

 

Kirari: Don Allah a ba Ɗan Sahaaibu kyautar mota,

 Ni ko a ba ni kyautar Honda.

 

Yara: Yara ku buga min hwata,

 Yarana ku buga min fata,

 Gwamanan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan Barade Alu Wamakko,

Yara: Jikan Barade Alu Wamakko.

 

Jagora: A Ɗan Barade Alu Wamakko,

Yara: Jikan Barade Alu Wamakko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci.

 

Kirari: Wani kiɗi sai mulki,

 Wani iri sai iko.

 

Jagora: Yara karo-da-karo sai rago,

Yara: To kai ɗan akuya kik kai ka?

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Aalu Wamakko.

 

Jagora: Na Yarima kutunkun ɓauna,

 Na san ba a cire ma kaska.

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci.

 

Kirari: Sai ta girma ta faɗi.

 

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Wai mutane suna da labari,

 Mutanen suna fa ta faɗi,

 Matasa suka faɗa man,

 Shi da gaskiya yake aiki

Yara: Don ƙarya maganab banza ta,

 

Jagora: Matasa sun faɗi,

 Da gaskiya yaka aiki,

Yara: Don ƙarya magabab banza ta,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: In ka tashi zuwa na tashi,

Yara: In ko ba ka zuwa na fasa,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan Ama nika so in ga nai,

 Ɗan Ama magana wajjenka,

 Ɗan Ama magana wajjenka,

 Kai ni garai mu ishe mai garkar,

 Gwamnan Sakkwato mai adilci,

 Ni ma na biɗi kyautam mota,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: A miƙa ma mota,

 A ba maroƙanka masussukka.

 

Jagora: Kai ka faɗi a faɗi aƙ ƙarya,

Yara: Mai ja ma wahala ta hau shi,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ko ni ba dai a hika alheri ba,

Yara: Sai dai a gwana ma taska,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko,

 

Jagora: Gwamna ba dai a hi ka Alheri ba.

Yara: Kai sai dai a gwada ma taska,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci.

 

Jagora: Sarkin Yamma Alu Wamakko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: In ka tashi zuwa na tashi,

Yara: In ko ba ka zuwa na fasa.

 

Jagora: Kai ka faɗi a faɗi aƙ ƙarya,

Yara: Mai ja wahala ta hau shi,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: ‘yan adawa sai jin haushi,

 ‘yan adawa sai jin haushi,

 To daɗa sai ku mace ‘yan iska,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: Wada ba su so ba,

 Haka Rabbana Ubangiji yas so,

 Wada ba su so gani ba.

 

Jagora: Ni ban san shi ba,

 Shi bai san ni ba,

 Amma nai mashi kyautar waƙa,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: An laƙa ma ba shi,

 Mun laƙa ma bashi.

 

Jagora: Ni ban san shi ba,

 Shi bai san ni ba,

 Amma nai maka wannan waƙa.

Yara: Gwamanan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan girma sutura yas saba,

Yara: Yanda yai mani ban ram mai ba.

 

Jagora: Sannu Waziri shi nai man hairan,

Yara: Abin da ya kai mani,

 Ban ram mai ba.

 

Jagora: Ni fa manitta na gode mai,

Yara: Abin da yai mani ban ram mai ba.

 

Jagora: Simeta Tureta ban ram mai ba.

Yara: Abin da ya kai mani ban ram mai ba.

 

Jagora: Simeta Tureta ban ram mai ba,

Yara: Abin da ya kai mani ban ram mai ba,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan Barade Alu Wamakko,

Yara: Jikan Barade Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan Barade Alu Wamakko,

Yara: Jikan Barade Alu Wamakko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ni ban san shi ba,

 Shi bai san ni ba,

 Amma nai mashi,

Yara: Kyautar waƙa,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ɗan Ama magana wajjenka,

 Ɗan Ama magana wajjenka,

 Kai ni ga gwamna mu kwana gidan shi,

 Don ɗai dai a maƙa min mota.

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Shi ko wane kutunkun ɓauna,

 Wannan ba ya da yin alheri,

 Kama-kama ni kan nir rena,

 Kamar ya shi bai hairi,

 Kamar ya shi bai hairi,

 Iun kag gane shi kamar zai hairi,

 Ni na san ga buga banza ne,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: Mutumen banza ne.

 

Jagora: Wane kamar ya yi mai alheri,

 Ashe ya zan,

Yara: Mutumen banza na,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 

Jagora: Shi kan wane ba magana,

 Wajje nai kuma ga magana,

 Na samu,

 Zuwa na Sakkwato birnin Shehu,

 Na kumo ma muƙamai nai na,

 Sai mutane suna ta faɗa min,

 Saura ma muƙamai nai na,

 Ɗan Shaaibu ba ya riƙa mai,

 Tunda dai maganam mata ce.

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wmakko.

 

Jagora: Shegen ba ya yi yin kyauta,

 Sai dai in magana mata ta,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: Sai dai in ka iya kalwanci,

 Da kai da shi za ku shiri.

 

Jagora: To ni ba ni iya kalwanci,

 Ni dai ban iya yin kalwanci,

 Ni dai ban iya yin kalwanci,

 Balle ya iza min samu,

 Shege!

Yara: Mai gidanmu Alu Wamakko,

 Gwamnan Skkawato mai adalci.

 

Jagora: Malaman gari ku ba mu,

 Kala tsaye mai ansan magana ‘yan birni,

Yara: Mai amsam magana ‘yan ƙauye.

 

Jagora: Mai amsam magana ‘yan birni,

Yara: Mai amsam magana ‘yan ƙauye.

 

Jagora: Mai amsam magana ta manoma,

Yara: Mai amsam magana ‘yan boko,

 Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Mai amsam magana Hillani,

 Mai amsam maganam mu manoma,

 Mai amsam magana ‘yan boko,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Kirari: Kowa ya taho garai daidai ne,

 Duk yana maraba da kowa.

 

Jagora: Tsantsani kashe mai ganganci,

 Kowaz zo da kiɗi ka ba shi,

Yara: Gwamnan Sakkwato mai adalci,

 Sarkin Yamma Alu Wamakko.

 

Jagora: Ka hi ƙarhinsu wa su nan.

Post a Comment

0 Comments