Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗan Abai ALU (b) - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

 

Jagora: Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu.

Yara: Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade,

Yara: Bangon Tama na Amadu,

 Baban Fodiyo jagoran,

 Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sa he duk,

 Sadauki sarkin Ymman,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade,

Yara: Bangon Tama na Amadu,

 Baban Fodiyo jagoran,

 Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sa he duk,

 Sadauki sarkin Ymman,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ba su iyawa da kai,

 Su bi ka kawai shi am magana,

 Gwamnan Sakkwato,

Yara: Mai ja maka ya san,

 Wahala ɗai ta yash shigo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ba su iyawa da kai,

 Su bi ka kawai shi am magana,

 Gwamnan Sakkwato,

Yara: Mai ja maka ya san,

 Wahala ɗai ta yash shigo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Allah shi ka son mutum,

 Yakin nan mala’iku,

 Sannan ‘yan Adam su bi,

 Don haka mun bi ka,

 Alu gwamnan Sakkwato.

Yara: Mai ja maka zai ɗau wahala,

 Koko ɗan wuta na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Allah shi ka son mutum,

 Yakin nan mala’iku,

 Sannan ‘yan Adam su bi,

 Don haka mun bi ka,

 Alu gwamnan Sakkwato.

Yara: Mai ja maka zai ɗau wahala,

 Koko ɗan wuta na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Suri Tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade mai turawa.

Yara: Alu sadauki kake birni da,

 Dawa daji ko gida na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Suri Tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade mai turawa.

Yara: Alu sadauki kake birni da,

 Dawa daji ko gida na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ya yi cif sikiriti na jaha,

 Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,

Yara: Sarkin Yamma na Saluhu,

 Mai aikin gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi sahe duk.

 

Jagora: Kai an yi cif sikiriti na jaha,

 Kmuma doke a ce gwamnan Sakkwato,

Yara: Sarkin Yamma na Shehu,

 Mai aikin gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kamarka ne jahag ga kane ma,

 Uban Mahadi,

Yara: Kwas same ka ba hi yash sheƙa,

 Ya ɗau wata wahala,

 Kowwa ac ciki na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kamarka ne jahag ga kane ma,

 Uban Mahadi,

Yara: Kwas same ka ba hi yash sheƙa,

 Ya ɗau wata wahala,

 Kowwa ac ciki na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: In babu hassada,

 An san gwamnatinka tai aiki,

 Sakkwato,

 Sa’annan kuma ko da hassada,

 An san gwamnatinka tai aiki,

 Sakkwato.

Yara: Zama an san ta raya,

 Birane kuma ta raya mutan,

 Ƙauyen Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: In babu hassada,

 An san gwamnatinka tai aiki,

 Sakkwato,

 Sa’annan kuma ko da hassada,

 An san gwamnatinka tai aiki,

 Sakkwato.

Yara: Zama an san ta raya,

 Birane kuma ta raya mutan,

 Ƙauyen Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Arzikin ka ya fasa Dutse,

 Gwamna mijin Azziki,

 Bangon Tama mijin Murja,

Yara: Lokacinka na ka matsa,

 Wadda duk aka tsammani,

 Ka hi nan na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Arzikin ka ya fasa Dutse,

 Gwamna mijin Azziki,

 Bangon Tama mijin Murja,

Yara: Lokacinka na ka matsa,

 Wadda duk aka tsammani,

 Ka hi nan na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kowa ad da tsohuwa mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura,

 Mai ita na Amadu.

 

Jagora: Kowa ad da tsohuwa mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura,

 Mai ita na Amadu.

 

Jagora: Kowa ad da tsohuwar mota,

Yara: Saio ya biɗi mai tura mai ita na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: A ko makaho bai san,

 Dare ba ya san rana tsaka.

Yara: Idan rana ta kai wani,

 Ba ya faɗa mai,

 Ga jiki nai yaka ji,

 Kowa ash shiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sa he duk,

 Sadauki sarkin Yamma

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ali ka yi godiya ga Allah,

 Don baiwad da a kai,

 Allah ya yi ma,

 Jahar Sakkwato kai ad da,

 Mutane baki ɗaya na Amadu,

Yara: Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali ka yi godiya ga Allah,

 Duk baiwad da a kai,

 Allah ya yi ma,

Yara: Jahar Sakkwato kai ad da,

 Muane baki ɗayan na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jaogra: Zmanin ka an ga ci gaba,

 Sosai jahar Sakkwato,

 An samu ci gaban ilimi,

 Raya karkara da ruwan sha,

 Da titunan mota kuma inda,

 Ka son NEPA an yi mai,

Yara: Jahar Sakkwato duk inda,

 Ka son titi an yi mai na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jaogra: Zmanin ka an ga ci gaba,

 Sosai jahar Sakkwato,

 An samu ci gaban ilimi,

 Raya karkara da ruwan sha,

 Da titunan mota kuma inda,

 Ka son NEPA an yi mai,

Yara: Jahar Sakkwato duk inda,

 Ka son titi an yi mai na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗace,

 In da duk a kai gefe,

 Mu ba mu da wannan,

 Nan jahar Sakkwato,

 Mun yarda da junanmu,

 Muna hulɗa sahe duk,

 Duk jahar Sakkwato kowa,

 Ka nufin gina yai gida,

Yara: Jahar Sakkwato kowa,

 Ka nufin mota ya sawo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗace,

 In da duk a kai gefe,

 Mu ba mu da wannan,

 Nan jahar Sakkwato,

 Mun yarda da junanmu,

 Muna hulɗa sahe duk,

 Duk jahar Sakkwato kowa,

 Ka nufin gina yai gida,

Yara: Jahar Sakkwato kowa,

 Ka nufin mota ya sawo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Fodiyo jagoran Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ba su iyawa da kai,

 Su bi ka kawai shi am magana,

 Gwamnan Sakkwato.

Yara: Mai ja maka ya san wahala,

 Ɗzai ta yab biɗo na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato

 

Jagora: Ba su iyawa da kai,

 Su bi ka kawai shi am magana,

 Gwamnan Sakkwato.

Yara: Mai ja maka ya san wahala,

 Ɗzai ta yab biɗo na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 

Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade mai turawa.

Yara: Alu sadauki kake birni,

 Da dawa daji ko gida na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: A suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Mamman Ɗan Barade mai turawa,

Yara: Alu sadauki kakr birni da dawa,

 Daji ko gida na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kai an yi cif sikuritin na jaha,

 Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato.

Yara: Sarkin Yamma na Salihu,

 Mai aikin gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kai an yi cif sikuriti na jaha,

 Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,

Yara: Sarkin Yamma na Saluhu,

 Mai aikin gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,,

 Sahe duk,

 Sadauki sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kamar ka ne jahar ga ka nema,

 Uban Mahadi,

Yara: Kwas same ka ba hi yash sheka,

 Ya ɗau wata wahala,

 Kowwa ac cikin na Amadu,

 Mai kwana sa shirin yaƙi.

 

Jagora: Kamar ka ne jahar ga ka nema,

 Uban Mahadi,

Yara: Kwas same ka ba shi yash she ka,

 Ya ɗau wata wahala,

 Kowwa ac ciki na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ali in babu hassada,

 An san gwamnatin ka tai aiki,

 Sakkwato sa’an nan kuma,

 Ko da hassada,

 An san gwamnatinka tai aiki,

 Sakkwato,

Yara: Zama an san ta raya birana,

 Kuma ta raya mutan ƙauyen Sakkwato,

 Na Amadu mai kwana da shirin yaƙi.

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Kowa adda tsohuwar mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,

 Na Amadu.

 

Jagora: Kowa ad da tsohuwar mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali ka yi godiya ga Allah,

 Duk baiwad da akai,

 Allah ya yi ma,

 Jahar Sakkwato kai adda,

 Mutane,

Yara: Baki ɗaya,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Gagarabadau,

 Abin ruhe ƙohohi gwamna,

 Uban ɗan Ama,

Yara: Gudurmutsun dutsi kallon ka a kai,

 Sai heshin ruwa na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Gagarabadau abin ruƙin ƙohohi,

 Gwamna uban ɗan Ama,

Yara: Gudurmutsun dutsi,

 Kallonka a kai,

 Sai heshin ruwa na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: A ko makaho bai san dare ba,

 Ya san rana tsaka,

Yara: Idan ta kai wani ba ya faɗa mai,

 Ga jiki nai yaka ji kowa ash shiya,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk.

 

Jagora: A ko makaho bai san dare ba,

 Ya san rana tsaka,

Yara: Idan ta kai wani ba ya faɗa mai,

 Ga jiki nai yaka ji,

 Kowa ash shiya,

 Na Amadu.

 

Jagora: Zamaninka an a ci gaba,

 Sosai jahar Sakkwato,

 An samu ci gaban ilimi,

 Raya karkara da ruwan sha,

 Da titunan mota,

 Kuma inda ka san NEPA an yi mat,

Yara: Jahar Sakkwato,

 Duk inda ka son titi an yi mai,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Zmaninka an ga ci gaba sosai,

 Jihar Sakkwato,

 An samu ci gaban ilimi,

 Raya karakara da ruwan sha,

 Da titunan mota,

 Kuma inda ka son titi an yi mai,

Yara: Jahar Sakkwato,

 Duk inda ka son tutu,

 An yi mai,

 Yanzu jahar Sakkwato,

 Duk inda ka son titi an yi mai,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Tashin hankali da faɗace-faɗace,

 Da duk akwai gehe,

 Mu ba mu da wannan Sakkwato,

 Mun yarda da junanmu,

 Muna hulɗa sahe dut,

 Jahar Sakkwato duk wanda,

 Ka son gina yai gida,

Yara: Jahar Sakkwato,

 Duk wanda ka son mota ya sawo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Tashin hankali faɗace-faɗacen,

 Da duk a kai gehe,

 Mu ba mu da wannan,

 Nan Sakkwato,

 Mun yarda da junanmu,

 Muna hulɗa sahe dut,

 Jahar Sakkwato,

 Duk wanda ka son gina yai gida,

Yara: Jahar Sakkwato,

 Duk wanda ka son mota ya sawo,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mammam,

 Ɗan Barade mai Turawa,

Yara: Alu sadauki kake,

 Birni da dawa daji ko gida,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Suro tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade mai Turawa,

Yara: Alu sadauki kake,

 Birni da dawa daji ko gida,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

 Baban Foɗiyo,

 Jagoran Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Fodiyo,

 Jagoran Sakkwato na Amadu.

 

Jagora: Ali ɗan Barde Wamakko,

 Gwamnatinka tai aiki,

 In ba a faɗi ijjiya ta gani,

Yara: Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali jikan Barade Um,aru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Fodiyo,

 Jagoran Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kamar ka ne jahayag ga ke nema,

 Umaba Mahadi,

Yara: Lwas sameka ba shi yash she ka,

 Shi ɗau wata wahala,

 Kowa ac ciki na Amadu,

 Mai wakan da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kamak ka ne jahag ga ka nema,

 Uban Mahadi,

 Kwas same ka ba shi yash she ka,

 Ya ɗau wata wahala,

 Kowwa ac ciki na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk.

 

Jagora: Miƙe tunaninka tahi,

 Ja ɗamaram mulki,

 Yau da wanda yas so ka,

 Yau da wanda yaƙ ƙi ka,

 Kama ka riƙe gwamna,

 Tun da yanzu nauyin,

Yara: Kowa na bisa kanka jahas Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk.

 

Jagora: Miƙe tunaninka,

 Tahi ja ɗamaram mulki,

 Yau da wanda yas so ka,

 Yau da wanda yaƙ ƙi ka,

 Kama ka riƙe gwamna,

 Tunda a yanzu nauyin,

Yara: Kowa na bisa kanka,

 Jahar Sakkwato,

 Tun da yanzu nauyin kowa,

 Na bisa kanka jahar Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk.

 

Jagora: Muna ganin gwamnati,

 Ba dai da irin ta ka ba,

 Sakkwato musakai ma,

 Sun san da,

Yara: Kana mulkin Skkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Foɗiyo,

 Jagoran Sakkwato na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kai an yi cif sikiriti na jaha,

 Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,

Yara: Sarkin Yamma na Saluhu,

 Mai aikin gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kai an yi cif sikuriti na jaha,

 Kuma dole a ce gwamnan Sakkwato,

Yara: Sarkin Yamma na Saluhu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Gajiyayyu da nakasassu,

 Kjowane ka yi mishi albashi,

 Jahar Sakkwato a daina bara,

Yara: Kowa ka bara,

 Bai son gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Gajiyyyu da naƙasassu,

 Kowane ka yi mishi albashi Sakkwato,

Yara: A daina bara,

 Kowa ka bara bai son gaskiya,

 Yac ce a daina bara,

 Kowa ka bara,

 Bai son gaskiya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: In ba ka nan maza suka ƙarya,

 Sun faɗi suna ai maza,

 Da duk ka taho ba wani mai motsawa,

 Sai su dangana yau dukba zakara,

 Sai kai sai su dangana,

Yara: Yau ba zakara ya zuwa,

 Sai kaya na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kai in ba ka nan maza suke kuri,

 Har su faɗi su ne wai maza,

 Idan har ka zo ba wani mai motsawa,

 Sai su dangana.

 

Yara: Yau duk ba zakara ya zuwa sai kai.

 

Jagora: Sai su dangana yau duk ba,

Yara: Zakara ya zuwa sai kaya,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Toron giwa,

 Kai ka kiyo daji kaikaɗai,

 Don namu kowa ya laɓe,

 Manya sun taho na Amadu,

Yara: Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Toron giwa kai ka kiyo daji,

 Kai kaɗai,

Yara: Don namu kowa ya laɓe,

 Manya sun taho na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: Abin yai farko,

 Na shaida yana kai ƙarshe,

 Kare da kura,

 Gaban da su kai tai ƙarshe,

 Yawan ilimi ya fara haɗasu,

Yara: Suna gaisuwa,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu.

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Foɗiyo jagoran Sakkwato,

 Na Amadu.

 

Jagora: A suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade toron giwa,

Yara: Alu sadauki kake,

 Birni da dawa,

 Daji ko gida,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Suri tozon ƙasa ƙanen Mamman,

 Ɗan Barade mai turawa,

Yara: Alu sadauki kake,

 Birni da dawa,

 Daji ko gida,

 Na Amadu.

 

Jagora: Gajiyayyu da naƙasassu,

 Kowane kai mishi albashi,

 Sakkwato,

Yara: A daina bara,

 Kowa ka bara bai son gaskiya,

 Na Amadu.

 

Jagora: Yac ce a daina bara,

Yara: Kowa ka bara bai son gaskiya,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Kowa adda tsohuwam mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita.

 

Jagora: Kowa ad da tsohuwam mota,

Yara: Sai ya biɗi mai tura mai ita,

 Na Amadu.

 

Jagora: Icce mai kama da ɓota,

 Sakkarawa ka faɗin maganan nan na ji,

 Icce mai kama da ɓota,

 Sakkarawa ke faɗin maganan nan na ji,

 In dai gaskiya a kai malam,

 Mai kamaz zuwa aka aiki,

 Wa ka shiga harkar sakare,

 Na Amadu,

Yara: Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sar\dauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 

Jagora: Ali jikan Barade Umaru,

 Kuma ɗan Barade Jaɓɓi,

Yara: Bangon tama na Amadu,

 Baban Fodiyo jagoran Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi.

 

Jagora: Dutsen tsakar ruwa kake,

 Ba rana kake ji ba,

 Kana nan ciki,

Yara: Gabanka da baya cikin ni’ima,

 Allah yai yo na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk,

 Sadauki Sarkin Yamma,

 Alu gwamnan Sakkwato,

 Na Amadu,

 Mai kwana da shirin yaƙi,

 Sahe duk.

 

Jagora: Aliyu magatakarda,

 Uban Lamiɗo ture haushe,

 Yara: Ba wani mai tare ka,

 Banda ikon Allah ture haushen maza,

 Aliyu magatakarda,

 Uban Lamiɗo ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda,

 Uban Lamiɗo ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,

 Toron giwa mai kiyo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Banda ikon Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda,

 Uban Lamiɗo ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,

 Toron giwa mai kiyo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Banda sarauta Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda,

 Uban Lamiɗo.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe su,

 Ba su tantance ba,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe su,

 Ba su tantance ba,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.

 

Jagora: Ko da ma ina ta cewa,

 Gwamna ti za ka yi Alu,

Yara: Da ikon Allah.

 

Jagora: Ko da ma ina tunanin,

Yara: Gwamnati za ka yi Aliyu,

 Da ikon Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ga mu mun taho ma,

 Alhaji ɗan Barade,

Yara: Ka ɗau kayanka,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ga ni na taho ma,

Yara: Alhaji ɗan Barade,

 Sai ka ɗau kayanka,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda,

 Uban Lamiɗo.

 

Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,

 Toron giwa mai kiyo wurinda ya so kiwo,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarauta Allah.

 

Jagora: Alhaji ɗan Barade,

 Toron Giwa mai kiwo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarauta Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu ɗan Barade,

 Toron giwa mai kiyo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarauta Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗan Barade toron giwa,

 Mai kiwo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarauta Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.

 

Jagora: In ka ga mutane suna ta dibi,

Yara: Jirgi ya ɗaga sama da ikon Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu magatakarda uban Lamiɗo.

 

Jagora: In ka ga mutane suna ta dubin jirgi,

Yara: Ya ɗaga sama da ikon Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza,

 Aliyu magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗan Barade toron giwa,

 Mai kiyo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Banda sarauta Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo.

 

Jagora: Ni Mamman ina tunanin,

 Ali kana sama hakan ga,

 Shi,

Yara: Ba shakka ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗan Barade toron giwa,

 Mai kiyo inda ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarauta Allah,

 Ture haushin maza,

 Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

Post a Comment

0 Comments