Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Amshi: Magani wargi ɗan Garba,
Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ɗan Lamiɗo uban Lamiɗo,
Mai gaskiya na difiti gwamna,
Muntari bawan Allah.
Yara: Ko ja da kai sai ka
gyara mai zama,
Ko ja da kai sai ka gyara mai zama.
Jagora: Kwa ja da kai sai ka
gyara mai zama
Yara (Amshi).
Jagora: Shi aiki ya zo ga
jaha tai,
Ba ci da ceto na kawo shi ba,
Balle ya danne abin talakawa,
Yara: Abin nufa tai aikin
gaskiya,
Abin nufa tai aikin gaskiya.
Jagora: Safe duk,
Yara: Abin nufa tai aikin
gaskiya.
Jagora: Maus hwaɗin Ali ba ka gwamna,
Ku ‘yan adawa yaya za ku yi?
Kun ci kare ba wankin hannu.
Yara: Alƙawalin Allah bai
tashi,
Aliyu kai ag gwamnan Sakkwato.
Jagora: Ga wasu sun ci
amanar Allah,
Wane aman ta kama su,
An yi gidaje gandam,gandam,
Ga hwa gida daidai jin daɗi,
Yara: Ba a da dama zamnawa
ciki.
Jagora: Su wane sun ci amana
Allah,
Yanzu amana ta kama su,
Sun yi gidaje gandam-gandam,
Ga hwa gidaje daidai jin daɗi,
Yara: Ba dama zaunawa
ciki.
Jagora: Baƙin ciki ya kai musu
geji,
Yara: An bar su sai dai
yawon ta-zubar.
Jagora: Ni ‘yan PDP ni ka kallo,
Sun shiga zaɓe an kashe su,
Sun sa ƙara kuma su hwaɗi,
Saboda sun san daɗin mulki,
Cikinsu kowa ya ƙi ya dangana,
Yara: Wanda duk a baya da
dangan,
Wanan rabo nai kunya safe du,
Wanda duk a baya da dangana,
Wannan rabo nai kunya safe du.
Jagora: Cikinsu kowa ya ƙi ya hanƙura,
Yara: Wanda duk a baya da
dangana,
Wannan rabo nai kunya safe du.
Jagora: Shi iƙirari ba ya da kyawo,
Du wanda ka ga yana iƙirari,
To ƙyale shi kurum ka yi
kallo,
Yara: Ka bar shi sai ta
gyara mai zama.
Jagora: Wawa,
Yara: Ka bar shi sai ta
gyara mai zama.
Jagora: Saga
Yara: Ka bar shi sai ta
gyara mai zama.
Jagora: Ka zanzame gaba ka
ci da aiki,
Mahasadanka suna da baya.
Yara: Mu je gabansu suna
lalata,
Saboda ka hau dokin gaskiya,
Mu je gabansu suna lalata,
Saboda ka hau dokin gaskiya.
Jagora: Kullum,
Yara: Mu je gabansu suna
lalata,
Saboda ka hau dokin gaskiya.
Jagora: Wane giya mulki ta ɗibai,
Ha ya je gada ya sha wallah,
Ya ce ko hulla tai ya aje ƙasa ga,
Sai tai gwamnan Sakkwato,
Yara: Mai bindiga iskan ga
talotalo,
Bana ya hau dokin rantsuwa.
Jagora: Babba da jika uba ƙuma sheri,
To bana ya yi tciya tai ya gaji,
Da tsahe-tsahe da yanke-yanke,
Da tsahe-tsahe da yanke-yanke
Da tsahe-tsahe da yanke-yanke.
Sai ni ce mishi dori ka dangana,
Yara: Ba ya da ya so Allah
ya yi ba,
Jagora: Babba da jika uban ƙuma sheri,
Ya yi tciya tai ya gaji,
Da tsahe-tsahe da yanke-yanke,
Sai ni ce mishi dori ya hanƙura,
Yara: Ba yada ya so Allah
ya yi ba.
Jagora: Wawa,
Yara: Ba ya da ya so Allah
ya yi ba.
Jagora: Jahili,
Yara: Ba yada ya so Allah
ya yi ba.
Jagora: Ka ga mutum mutumi
da kamar mutum,
Da ka ga nai ka ga tsumma ne kurum,
Bai hana komai bai tare komai,
Ka yi shi don ya tsare ma gona,
Yara: Bai hana tsuntsu ɓata ma ita,
Bai hana tsuntsu ɓata ma ita.
Jagora: Wannan,
Yara: Bai hana tsuntsu ɓata ma ita.
Jagora: Allah wadan gurun
kulu,
Da ɗau bai sa ba kashin kunya ba,
Shi bai saba kashe kunya ba,
Ba ka sani sai ka je gaisai,
In ya yi ma kyauta ka duba,
Ka dubi girma nai ka ga kyautar,
Yara: Abin akwai abin ban
kunya ‘yan uwa.
Jagora: Wannan,
Yara: Abin akwai abin ban
kunya ‘yan uwa.
Jagora: Wannan,
Yara: Abin akwai abin ban
kunya ‘yan uwa.
Jagora: Kwamishinan Idi
kashin Arzika,
Ka yi ciyaman kowa ya yaba,
To har yanzu da sauran aiki,
Yara: Muna da raunin ilmi
Sakkwato.
Jagora: Ka sani,
Yara: Muna da raunin ilimi
Sakkwato.
Jagora: Arzika ka sani,
Yara: Muna da raunin ilmi Sakkwato.
Jagora: Kwamishinan wasani
Ahmed,
Kwamishinan wasani Amadu,
Ɗan Aliyu sadaukin ɗa kake,
Ma’aikata sashen wasanni,
Suk inda kay magana ta zauna,
Yara: Ba su da dama canza
ma ita.
Jagora: Na san,
Yara: Ba su da dama canza
ma ita.
Jagora: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamna Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Yara: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamna Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Sai godiya zabira ka
yi ɗa,
Yara: Abin da yai man ya
kyauta ƙwarai.
Jagora: Gai da Mu’azu Zabira
Sakkwato,
Yara: Abin da yai man ya
kyauta ƙwarai.
Jagora: Gai da mijin
Alhajiya Arziki,
Mai hana ƙarya angon Murja,
Gai da mijin alhajiya Arziki
Mai hana ƙarya angon Murja,
Jikan Umaru kai ɗai gayya,
In sun so imma ba su so ba.
Yara: Aliyu kai a gwamna
Sakkwato.
Jagora: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamna,
Sakkwato ba a kai ma reni ko kusa.
Yara: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamna,
Sakkwato ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Gai da mijin
Alhajiya Arziki,
Mai hana ƙarya angon Murja,
Kai ɗai gayya jikan Umar,
In sun so im ma ba su so a,
Yara: Aliyu kjai ag gwamna
Sakkwato.
Jagora: In sun so im ma ba
su so ba,
Yara: Aliyu kai ag gamnan
Sakkwato.
Jagora: Gai da Mu’azu zabira
ka yi ɗa,
Yara: Abin da yai man ya
kyauta ƙwarai.
Jagora: Ni Baciyawa ka na
gode maka,
Baciyawa ka kyauta maini,
Kuma na san mutumin kirki ne,
Yau du irin harka Ɗanba’u,
Yara: Amadu ya bar watsa
mar ƙasa.
Jagora: Na san,
Yara: Ahmadu ya bar watsa
mar ƙasa.
Jagora: Na gode ma Mustapha
mai gandi,
Abin da yai ya gyauta ƙwarai,
Yara: Ni Mustapha Alhaji
mai gandi,
Abin da yai ya kyauta ƙwarai.
Jagora: Sakataren gwamnatin
jihar Sakkwato,
Sahabi Isa baban baƙo,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai.
Jagora: Ni sabis kwamishina
zan leƙa,
Saboda sarkin noma Bello,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ni sabis kwamishina
zan leƙa,
Saboda sarkin noma Bello,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Kwamishina hilallaki
na Sakkwato,
Aliyu gwamna Acida birni.
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Gaishe ka Ali jikan
Jaji Ali,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Na gode kantoma
Illela,
Abubakar S
Gari ka kyauta,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Abubakar S Gari ka kyauta,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Abubakar S Gari na gode,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Em Haji Kiruwa na
gode ma,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Haji Kiruwa kai
sannu da aiki,
Yara: Abin da yai ya kyauta
ƙwarai,
Jagora: Gai da ciyaman Haji
Sanusi,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ɗanwari ban rena ma
ba,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Alhaji Abu baƙi Ɗanliman Bello,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ciyaman Abu Baƙi Ɗanliman Bello,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ɗan majalisa na Habuja
baba,
Haliru Garba ina gaishe ka,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Na gode Ɗayyabu Kalmanu,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Rai ya daɗe Ɗayyabu na gode,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ni kantoma
Gwadabawa,
Abdu Sidi na gode ma,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ina Ɗan Abubakar Audu
Sidi,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ni Kantoman Gada na
gode,
Yahaya Ummaru Dunƙamaje,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ni kantoman Gada ka
kyauta,
Yahaya Ummaru Dunƙamaje,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Ga kantoman birni Raɓa,
A gai da Hali mutume na ne,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Alhaji Hali kantoman
Raɓa,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai,
Jagora: Alhaji mai akwai na
gode ma,
Yara: Abin da yai ya
kyauta ƙwarai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.