Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Taimaka mana Magaba,
Yara: Ka taimake mu Allah,
Waƙa Ali zam fara,
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Mai halin ƙwarai Wamako uban
Hindu.
Jagora: Yara zan yi tambaya,
Kai don Allah ku ban amsa,
Was sa mu yi mai waƙa?
Yara: Ummaru Ɗan Amma yas sa mui
mai waƙa,
To gata nan muna yi,
Waƙa Ali mun hwara,
Ka yi mun gani,
Dun mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini,
Wamako Uban Hindu.
Jagora: Yara zan yi tambaya,
Kai don Allah ku ban amsa,
Was sa mu yi mai waƙa?
Yara: Ummaru Ɗan Amma yas sa mui
mai waƙa,
To gata nan muna yi,
Waƙa Ali mun hwara,
Ka yi mun gani,
Dun mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini,
Wamako Uban Hindu.
Jagora: Kai tahiya sama sai
jirgi.
Yara: Tahiya ƙasa sai mota.
Jagora: Kai tahiya sama sai
jirgi.
Yara: Tahiya ƙasa sai mota.
Jagora: Ko gobe a ja daga,
Yara: Maƙi gudu ya shirya.
Jagora: Kai ko gobe a ja
daga,
Yara: Maƙi gudu ya shirya.
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Giwa ma sha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Yara: Giwa ma sha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Jagora: An so a ja ka yaƙi,
Sai an ka ga ka gagara.
Yara: Dud da ‘yan adawa,
Sun dangana sun bi ka.
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Ko gobe a ja daga,
Yara: Maƙi gudu ya shirya.
Jagora: Kai ko gobe a ja
daga,
Yara: Maƙi gudu ya shirya.
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Daular Usmaniyya,
Sun sa maka albarka,
Sun ce ga lokaci nai,
An ƙara masa girma.
Yara: Ba a rage masa girma
ba,
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora:’Yan kasuwaj jahas
Sakkwato,
Sun wani labari,
Sun sa maka albarka,
Sun ce ga lokaci nai,
An ƙara masu girma.
Yara: Ba a rage masu girma
ba,
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Manoman Sakkwato,
Su ma sun sa maka albarka,
Sun ce ga lokaci nai,
An ƙara masu girma.
Yara: Ba a rage masu girma
ba,
Sun yarda ka dai ƙara,
Mai farin jini,
Ali Wamako uban Hindu.
Jagora: ‘Yan kasuwaj jahas
Sakkwato,
Sun wani labari,
Sun sa maka albarka,
Sun ce ga lokaci nai,
An ƙara masu girma,
Yara: Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Edukeshin ɗin Sakwato,
Sun sa maka albarka,
Sun ce ga lokaci nai,
An ƙara masu girma.
Yara: Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Ku gwada min ɗan Ama
A sau mini tau mota,
Wagga gajiyak kah a yi,
Yara: Babu uban wasa,
Shi Ummaru waba ne,
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai farin jini,
Ali Wamako uban Hindu.
Jagora: Kai ku gwada mini ɗan Ama,
A sawo mini tau mota.
Yara: Wagga gajiya kak a
yi babu uban waƙa,
Shi Umaru waba
ne,
Ka yi mun gani,
Dum muyn yarda ka dai ƙara.
Jagora: Dange Shuni suna cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Mun yarda ka dai ƙara.
Jagora: Dange Shuni suna
cea,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘yan Tureta suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘yan Tureta suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Boɗinga suna cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Boɗinga suna cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Shagari suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Shagari suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Tambuwal su ma sun
bi,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Tambuwal su ma sun
ce,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Kuma ‘yan Yabo su
ma,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda Yabo suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Kuma ‘yan Kebbi sun
ce mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini,
Ali Wamako uban Hindu,
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: ‘Yan Wamakko suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Wammakko suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Kuma ‘yan Kware sun
ce muna,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Kuma ‘yan Gwadabawa
ma,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda ‘yan Gwada
bawa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Ilela suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Ilela suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hada ‘yan Gada sun
ce mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda ‘yan Gada na
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Gwaranyo suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Gwaranyo suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda Wurno suna ce
mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda Wurno suna
cewa,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Ka yi mun gani,
Don Allah ka dai ƙara,
Mai hwarin jini Wamako uban Hindu,
Jagora: Hadda ‘yan Gubi sun
ce muna,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Hadda ‘yan Gubi sun
ce mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Tangaza sun ce
mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: ‘Yan Tangaza sun ce
mana,
Yara: Mulkinka akwai daɗi,
Don Allah ka dai ƙara.
Jagora: Giwa masha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Yara: Giwa ma sha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Jagora: Walin Gagi a gaishe
ka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Walin Gagi da ranak
ka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Fam sek Aminu ka
kyauta,
Ummaru na goede.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Fam sek Aminu ka
kyauta,
Ummaru ya gode,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Waziri Aminu godiya,
Ummaru ya gode,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Waziri Aminu sannu,
Ummaru ya gode maka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Ummaru Ɗahiru na gode,
Na Tambuwal a gai sai,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ummaru ya Ɗahiru ka kyauta,
Na Tambuwal shirarre,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Ummaru na Gwari shi
ma,
A’a Ummaru na gode maka.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Na gwari godiya,
Edukashin kai komi,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Sannu Bello a gaishe
ka,
Na guiwa da ranak ka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Sannu fam sek na
gode,
Bello Guiwa a gaishe ka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Kalambaina mu gaishe
shi,
Ahamad na gaishe ka.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Kalambaina mu gaishe
shi,
Ahmad yai mani komai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Sita Silaimanu kai
komai
Sita Silaimanu kai komai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Mamman Tureta na
gode,
Ummaru ya kyauta min.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Muhamman Tureta,
Ummaru shi ma ya yaba girma nai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Jaɗɗi Kilgoro shirarre,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Aminu godiya kantoma
na Boɗai giwa,
Ciyaman na Dange Shuni,
Ciyaman na Dange Shuni,
Ummaru ya gode.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Walin Sifawa na
hantci,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Walin Sifawa na
hantci,
Tsoho baban gwamna.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Amadu Shantali can
Dange,
Amadu Shantali can Dange,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Kabiru Maraaa,
Ummaru ya yaba girma nai,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Kabiru Maraaa,
Ummaru na yaba girma nai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ahmed ɗan Ali na gode ma,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ahmed Ɗan Ali ka kyauta min,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Mai gwandu sifikan
nan,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Mai
Gwandu sifikan nan,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Faruƙu can ƙarar Yabo,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Sannu Bello Koc uban
ku gai sai
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Sannu Bello Koc uban
ku gai sai
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: P.L. Abu dugo yai muna ko,
Jagora: Abu dogo shi ma,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: ‘Yar Kangiwa a
gaishe ki,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Kulu ‘yar Kangiwa a
gaishe ki,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Ho Kulu Modi ‘yaƙ ƙasar Yabo,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ho Kulu Modi ‘yaƙ ƙasar Yabo,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Fati Ilu gaishe ki,
Ke Fatiu Ilu na gode,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Bala Talle a gaishe
ka,
Barista ka kyauta,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Bala Talle a gaishe
ka,
Barista na mawaƙa,
Amma a gidan gwamna.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Dodo Oroji mu
gaisai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Dodo Oriji mu
gaisai.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ciyaman Ɗahe na Shuni can fat,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Tasalla kire mun
dai,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Indo Ɗan Tasalla ku gaishe
shi.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ɗan Ado na Wahabi
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ɗan Ado na Wahabi
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Garzali gaishe ka,
Mai waƙa ka kyauta.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Sakataren mawaƙa,
Amma na gidan gwamna,
Barade Ali ka kyauta.
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Ko Alhaji mai gura
na Dange,
Ka biya can,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Alhaji mai guru na
Dange,
Ka yi
komi,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Isah Koko a gaishe
ka,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Ƙarnin Basiru Isah,
Yara: Na yi godiya,
Domin Ali na Wamako.
Jagora: Gowa masha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Yara: Gowa masha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Jagora: Ga giwa ma sha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Yara: Gowa masha dayi,
Yau Ali ka yi wuyay yaƙi.
Jagora: An so a ja ka yaƙi,
Sai an ka ga ka gagara.
Yara: Dud da ‘yan adawa,
sun dangana sun bi ka,
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Mugun madambaci,
Ali dambenka akwai shawa,
Ka sari kundumi,
Ka sari kini Sanyinna,
Su Ɗan Tagaye.
Yara: Rannan sun ce mana
sun wahala.
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
Jagora: Mugun madambaci,
Ali dambenka akwai shawa,
Ka sari kundumi,
Ka sari kini Sanyinna,
Su Ɗan Tagaye.
Yara: Su ɗan Tagaye rannan,
Sun ce mana sun daina,
Ka yi mun gani,
Dum mun yarda ka dai ƙara,
Mai hwarin jini wamako uban Hindu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.