Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗan Ba’u 6 - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

 

Amshi: Aliyu Magatakarda uban Lamiɗo,

 Tura Haushin maza.

 

Jagora: Ɗanbarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka ban da ikon Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗanbarade toron gira,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Ɗanbarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka ban da sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe su ba su tattance ba,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe su ba su tattance ba,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ko da ma ina ta cewa,

 Gwamnati za ka yi,

 Alu ikon Allah,

Yara: Da ikon Allah,

 Ture haushin mata.

 

Jagora: Ko da ma ina ta tunanin,

 Gwamnati za ka yi,

 Alu ikon Allah,

Yara: Da ikon Allah,

 Ture haushin maza

 

Jagora: Ko da ma ina tunanin,

Yara: Gwamnati za ka yi,

 Alu da ikon Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ga mu mun taho ma,

 Alhaji Ɗambarade,

 Sai ka ɗau kayanka,

Yara: Sai ka ɗau kayanka,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ga ni na taho ma,

Yara: Alhaji Ɗambarade,

 Sai ka ɗau kayanka,

 Ture haushin maza,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagoara: In ka ga mutane suna ta dibi jirgi,

Yara: Ya ɗaga sama da ikon Allah,

 Tura haushin maza.

 

Jagoara: In ka ga mutane suna ta dibi jirgi,

Yara: Ya ɗaga sama da ikon Allah,

 Tura haushin maza.

 

Jagora: Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare mai,

 Banda sarauta Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ni Mamman ina tunani9 Ali,

 Kana zama hakan ga,

 Shi ba shakka,

Yara: Shi ba shakka,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Aluyu Ɗanbarade uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

Yara: Aliyu Ɗanbarade uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Aluyu Ɗanbarade uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

Yara: Aliyu Ɗanbarade uban Lamiɗo,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka ban da ikon Allah,

 Ture haushi,

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da ya so,

Yara: Ba wani mai tare ka sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe,

 Su ba su tattance ba,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Maza na ta hassada tai,

Yara: Gulbi ya haɗe,

 Su ba su tattance ba,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ko da ma ina cewa,

 Gwamnati za ka yi,

 Alu da ikon Allah,

Yara: da ikon Allah,

 Ture haushen maza.

 

Jagora: Ko da ma ina cewa,

 Gwamnati za ka yi,

 Alu da ikon Allah,

Yara: da ikon Allah,

 Ture haushen maza.

 

Jagora: Ga mu mun taho ma,

 Alhaji Ɗambarade,

 Sai ka ɗau kayanka,

Yara: Sai ka ɗau kayanka,

 Ture haushen maza.

 

Jagora: Gani na taho ma,

Yara: Alhaji Ɗambarade,

 sai ka ɗau kayanka,

 ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade,

 Toron giwa mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade,

 Toron giwa mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Alhaji Aliyu Ɗambarade,

 Toron giwa mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare ka,

 Sai sarautar Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: In ka ga mutane,

 Suna ta dibin jirgi,

Yara: Ya ɗaga da ikon Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: In ka ga mutane,

 Suna ta dubi jirgi,

Yara: Ya ɗaga da ikon Allah,

 Ture haushin maza.

 

Jagora: Ɗambarade toron giwa,

 Mai kiyo wurin da yas so,

Yara: Ba wani mai tare mai,

 Sai sarautar Allah,

 Tura haushin maza.

 

Jagora: Ni Mmman ina ta tunanin,

 Ali kana zama hakan ga,

 Shi ba shakka.

Yara: Shi ba shakka tura haushin maza

 

Jagora: Ni Mmman ina ta tunanin,

 Ali kana zama hakan ga,

 Shi ba shakka.

Yara: Shi ba shakka tura haushin maza

 

Jagora: Ni Mmman ina ta tunanin,

 Ali kana zama hakan ga,

 Shi ba shakka.

Yara: Shi ba shakka tura haushin maza.

Post a Comment

0 Comments