Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattalin Zaɓen Rubutattun Waƙoƙin Hausa Domin Yara

Muƙalar  da aka gabatar a Taron Nazari Kan Rubuce-Rubuce Cikin Hausa wanda Hukumar Raya Wallafa Littattafai Ta Nijeriya (Nigerian Book Development Council) ta gudanar a Kaduna (Durbar Hotel) daga 5-8 ga Mayu 1986
Daga

A.B. Yahya
07031961302
bagidadenlema2@gmail.com

Tsakure

Ta nazarin “Waƙar ‘Yan Makaranta” ta Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa, wannan maƙala ta fito da waɗansu abubuwan la’akari da malami ko marubuci ko masu buga littattafai za su yi amfani da su wajen zaɓar wa yara rubutattun waƙoƙin da suka dace da fahimtarsu. Waɗannan abubuwan la’akari su ne lafazi ko harshen waƙa da saƙo da salo da kuma zubi da tsarin waƙar.

Manufa

Manufar wannan maƙala ita ce bayyana wasu muhimman abubuwan la’akari wajen zaɓar wa yara rubutattun waƙoƙin Hausa waɗanda suka dace da tunaninsu da fahimtarsu. Muhimman gimshiƙai ne amma kuma maƙalar ba ta nufin su ke nan. Filin da maƙalar take da shi ba zai ɗauki tattaunawa mai yawa ba ta yadda za a fito da dukkan muhimman abubuwan la’akari wajen zaɓen waƙoƙi domin yara.

Shinfiɗa

Adabin baka na Hausa ba ya ƙamfar waƙoƙi domin yara. Wato cike yake da waƙoƙi waɗanda aka tsara daidai tunani da fahimtar yara kuma domin su yi amfani da su. Ba wuce gona da iri ba ne idan aka ce kusan dukkan wasannin yara na gargajiya akan gudanar da su ne tare da rera waƙoƙi. A cikin tatsuniyoyin Hausa ma akan sami waɗanda suka ƙunshi ko kuma aka gina da waƙa. Haka kuma a wajen bukukuwa ma akwai waƙoƙin da yara sukan rera waɗanda kuma suka dace da tunani da fahimtar yaran1.

To, amma ba haka abin yake ba a rubutaccen adabin Hausa. Yadda adabin baka ya girmi rubutaccen adabi, yadda kuma waƙar baka ta girme wa rubutacciyar waƙa, haka lamarin yake ta fuskar waƙoƙin yara.

A yayin da rubutattun waƙoƙin Hausa suka samu tun aƙalla a karni na 17, nau’insu na yara ko a wannan zamani na karni na 20/21 sun yi ƙaranci. Tabbas an sami aƙalla waƙa guda a ƙarni na 19 wadda take bayyana abubuwan da suka shafi yara. To sai dai wannan waƙa2 ba a rubuta ta ba ne domin yara. Manufarta ita ce manya su fahimci yadda ake yi wa yara tarbiyya. Ko da an rubuta wata waƙa musamman domin fahimta da tunanin yara a ƙarni na 19, binciken da ya haifar da wannan maƙala bai samu kai ga wannan waƙa ba3.

A kan haka ne za a iya cewa babu ka-ce-na-ce idan muka ayyana cewa rubutattun waƙoƙin Hausa musamman domin yara sun fara samuwa ne a cikin ƙarni na 20 bayan da ilmin boko ya kafu a ƙasar Hausa har aka fara samun malamai Hausawa a cikin mukarantun boko, da kuma na Islamiyya masu tsari makamancin na bokon. Malamai kamar Alhaji Shehu Shagari da Alhaji Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu malaman makarantun boko ne waɗanda suka yi amfani da waƙa domin inganta karantarwarsu. Waƙar Nijeriya ta Shehu Shagari fitacciya ce a wannan fage4. Alƙali Alhaji Haliru Wurno da Alhaji Abdulƙadir Macciɗo su ma malamai ne amma na makarantar Islamiyya waɗanda suka yi amfani da waƙa a karantarwar da suka yi.

Gimshiƙan Abubuwan La’akari

A cikin wani littafi nasa E.H. Jones ya ayyana cewa:

Kusan duk mai iya karatu zai iya ‘karanta’

waƙa, to amma fa kafin ya samu nishaɗi

daga waƙa tilas ne sai ya yi tanadin wani

abu (na musamman) zuwa ga yin karatun5

Ko mene ne dai ya kamata wanda zai karanta waƙa ya tanada, a fili take cewa shi ma wanda zai gabatar da waƙa ga yara wajibi ne ya yi tanadin wasu muhimman abubuwa kafin ya gabatar musu da ita. Waƙa wani nau’in adabi ne da ya shafi fasaha mai tasiri kai tsaye a kan zuciya. Haliru Wurno yana cewa.

Waƙe fasaha ne da ya cuɗe ka

Kuma ba karatu na ba in an ba ka

Ilmi dubu sai ka biɗo wani nasa6

Abin nufi a nan shi ne haƙiƙa duk wanda zai rubuta waƙa domin yara, ko zai zaɓo waƙa daga cikin jerin waƙoƙi domin yara, to fa wajibi ne ya yi la’akari da fahimta da tunanin yaran. Malamin Ilmin Mutuntaka da na Haliyyar yara sun fi kowa sani game da gaskiyar wannan magana7.

Ta la’akari da abin da masana suka faɗa ne wannan maƙala take yin kira da cewa tilas ne mai zaɓen waƙoƙi domin yara ya yi la’akari da abubuwa huɗu. Waɗannan kuwa su ne lafazi ko harshen waƙa da saƙo da salo da kuma zubi da tsarinta. Waɗannan suna daga cikin muhimman abubuwan la’akari idan malami yana so ya kauce wa waƙoƙin da ba su dace da yara ba, ko da kuwa an kira su da sunan ‘waƙoƙi domin yara’.

Lafazi Ko Harshen Waƙa

Lafazi ko harshen waƙa a nan yana nufin kalmomi da jumloli ko yankinsu da aka yi amfani da su cikin waƙa. Ta fuskar yara akwai kalmomin da suka dace da su, ko dai ta wajen irin ɗa’ar da suke cusawa ko kuwa ta wajen ma’anoninsu, Akwai kalmomi tsarkaka akwai kuma kalmomin batsa. Saboida haka ta la’akari da al’adun Hausawa bai dacewa a zaɓa wa yara waƙoƙin da suka ƙunshi kalmomin batsa. Wannan a fili yake ba sai an yi wani dogon bayani ba. To amma ta wajen kalmomi dangane da ma’anoninsu akwai matsalar ma’anar da fahimta da tunanin yara sukan iya ɗauka. A nan ne malami zai duba ya gani shin kalmomin da waƙa ta ƙunsa masu sauƙin fahimta ne ga yara. Alal misali, mun san cewa yara ‘yan shekaru uku sun fi amfani da kalmar babbuna bisa ga manya idan suna son su bayyana abubuwa masu girma. Haka kuma yaro ya fi fahimtar kalmar gargaɗi bisa ga nasiha. Wannan kuwa shi ne ya sanya Alhaji Umaru Wazirin Gwandu ya faɗa wa ɗalibansa.

Mallam ka yo muna gargaɗi
Mu tsaya mu ji shi mu ko riƙai

Haka nan kuma ya zaɓi ya yi amfani da kalmomin mai kyau a yayin da yake buƙatar nuni da halin nagarta:

Wa da anka so almajiri
A ishe hali mai kyau garai

Yana daga cikin aiki malami ta wannan fuska ya yi la’akari da kalmomi waɗanda ma’anoninsu a sarari suke ba a ɓoye ba. Abin nufi a nan shi ne yara sun fi fahimtar kalmomin da za a iya ganin ko taɓa abubuwan da suke wakilta, ba wai sai cikin ƙwaƙwalwa ne kurum za su gane manufar ba. Misali a cikin waƙarsa ta ‘yan makaranta Wazirin Gwandu ya ce:

Wanki shikai wanka shikai
Ɗakinsa ko shara garai

Kalmomin wanki da wanka da shara, kyawawan misalan kalmomi ne da suke ayyana manufa ta tsafta ga yara. Dukkansu suna ɗauke da manufofin da yara suke iya gani da ido.

Hausawa sukan ce daidai ruwa daidai ƙurji. Ƙwaƙwalwar yara haka take a wajen fahimtar magana. Abin nufi a nan shi ne amfani da jimloli masu sauƙi ta fuskar tsawo da ma’ana. Wato ke nan malami ya zaɓar wa yaransa waƙoƙin da suka ƙunshi guntattakin maganganu marasa sassarƙiya, marasa kuma tsawo. Kai da ganin wannan baiti na waƙar Garba Gwandu ka san ba na yara ba ne:

Sun ce cimakassu mutuncina sai sun ga ya ƙare
Da shi suka yawatawa cikin ofis da zama cikin zaure

Ni ko nawa gata Halimi Sarki wanda yak kore
Mugu yay yi nesa ga kayana tsoronshi yas sare

Mi wani zai yi min babu mai iya komi sai nufar Allah.

Ko ɗangon Farko muka duba za mu iya ganin sassarƙiyar da za ta gagari ƙwaƙwalwar yara. Muna iya kasa ɗangon zuwa jimloli biyu: sun ce cimakassu mutuncina/sai sun ga ya ƙare. Wato ana buƙatar a fahimci waɗannan manufofi:

(a) Nufarsu ita ce su ci mutuncina

(b) Za su yi ta cin mutuncina har sai na kasance ba ni da sauran mutunci.

To amma a waƙarmu da muke misali da ita, “Waƙar ‘Yan Makaranta” , marubucinta ya yi amfani da gajejjerun maganganu daidai yadda ƙwaƙwalwar yara za ta ɗauka, ta kuma kawo fahimta ga su yaran ba da wahala ba. Dubi waɗannan baitoci.

Da rufin abincinai da kyau
Abada akwai faifai garai

‘Yar ketuwa ga tufa shi ɗun-
Ke tanadin kurɗi garai.

Bai shan sigari gami da taba
Ba yawan roƙo garai

Saƙon Waƙa

Magana kan lafazi ko harshen waƙa wadda ta gabata ita take yin nuni da cewa ya kamata saƙon waƙar da aka yi domin yara ya kasance daidai fahimtar yaran. Nufina a nan shi ne, tilas ne saƙon waƙar yara ya yi la’akari da duniyar yara. Lamurran da suka shafi yara kai tsaye; da saƙo mai jan hankali, wato saƙo mai kwaɗaitarwa; da saƙo mai sauƙin fahimta gare su; sannan kuma da saƙo mai kafa hujjojin bin umurnin da waƙa ta ƙunsa, duk abubuwa ne na yanayin duniyar yara da tunaninsu:

Ta fuskar lamurran da suka shafi yara kai tsaye muna iya kawo misali da cewa babu hikima ga umurtar yaro da ya bi dokokin ƙasa ko kuma ya yi biyayya ga shugaban ƙasa. Dalili kuwa shi ne cewa waɗannan duka ba su shafi yaro kai tsaye ba. To amma idan aka kawo masa maganar malaminsa, zai tsaya tsaf ya saurare ta, ya fahimce ta, ya kuma yi aiki da ita. Saboda haka ne Wazirin Gwandu, marubucin waƙarmu ta ‘yan makaranta ya zaɓi ya umurci almajiransa da waɗannan baitoci:

Mai hankali mai girmamawa
Har a san ladabi garai

Shi tsare umurnin malaminsa
Shi zan tsaron girma garai

Na gabansa ko ba malamai 
Ba shi zan tsaron girma garai 

Haka kuma a gaba kaɗan marubucin ya ce,

Ga tufa da littaffansa har
Ga jiki akwai tsabta garai

Wanki shikai wanka shikai
Ɗakinsa ko shara garai

Marubucin waɗannan baitoci bai nemi yara da su kasance masu tsarkake ƙasarsu ba, amma ya neme su da su tabbata sun tsakake littattafansu da tufafinsu da jikinsu da kuma ɗakin da suke kwanciya a ciki. Duk waɗannan abubuwa ne da suka shafi yara kai tsaye. Ya san cewa waɗannan abubuwa suna da sauƙin fahimta ga yara. To amma mu manya mun kwan da sanin cewa idan yara suka ji wannan umurni na malaminsu, a ƙarshe wannan biyayya za ta kai su ga tsarkake ƙasarsu.

Malamin da zai zaɓar wa yara waƙoƙi na bukatar yin la’akari da waƙoƙin da suka ƙunshi kwaɗaitarwa ta fuskar saƙonnin da suke ɗauke da su. Abin nufi a nan shi ne, yara su sami fahimtar cewa bin umurnin da waƙa ta kawo yana tattare da sakamako mai kyawo gare su. Sanin cewa idan suka aikata abin da waƙa ta nemi su aikata ko rashin aikata abin da waƙar ta hane su, zai kawo musu sakamako mai kyawo, wannan shi zai sa su tashi tsaye su bi wannan umurni. Wato ko bayan nishaɗin da za su samu daga rera waƙar, malamin ya tanadar musu matakin gina kansu zuwa ga rayuwa ingantacciya. Bayan da Wazirin Gwandu ya rattaba wa almajiransa abubuwan da suka kamaci almajiri ya yi, sai ya kammala da cewa duk almajirin da ya kiyaye waɗannan abubuwa, to kuwa shi ne:

To wanga a’ almajiri
Don ko hali mai kyau garai

Samu shikai girma shikai
Don girmamawa ag garai

Kowa yana murna da shi
Don ko halin girma garai

Almajiri duka yaz zamo
Haka arziki na nan garai

A cikin waɗannan baitoci an ambaci abubuwan da yaro yake kwaɗayin su liƙu gare shi. Duk ɗan makaranta yana son a ce idan ana neman ɗan makaranta na sosai to shi ne wannan. Ga shi kuwa Waziri ya faɗa da ƙaƙƙarfar murya. 

To wanga a’ almajiri

Wannan almajiri shi ne mai tabbataccen hali nagari. Shi ne zai sami kowane abu mai kyawo. Haka kuma shi ne zai samu girma kamar Malam da Baba da duk wani mutum wanda yaron yake ganin yana da daraja. Shi ne zai kasance wanda ake murna da shi a duk inda ya tafi. Shi ne kaɗai wanda a cikin taron ‘yan makarantarsu gaba ɗaya zai samu arziki kowane iri.

Haƙiƙa Wazirin Gwandu ya cusa kwaɗaitarwa irin wadda ta dace da yara a cikin waɗannan baitoci. Lura sosai da wata hikima ta ƙarfafa kwaɗaitarwa da marubucin ya cusa a cikin baitocin. Kowane baiti yana ɗauke da sakamako, sannan kuma kowane ɗauke yake da jaddada abin da ake son ɗan makaranta ya yi domin ya sami sakamakon da aka ambata. Baitoci uku farko sun fara kawo sakamako a ɗangogin farko sannan aiki a ɗangogin ƙarshe, a yayin da baiti na ƙarshe ya kawo aiki sannan daga baya ya zo da sakamakon.

Salon Waƙa

Ya kamata mai karatu ya lura tun a bayani kan lafazi ko harshen waƙa, cewa haƙiƙa salo yana da muhimmiyar rawar da zai taka a cikin yunƙurin zaɓar wa yara waƙoƙin da za su dace da su. Kalmomi masu sauƙi da jimloli marasa sassarƙiya ko jimlolin marasa goyo, duk abubuwa ne da kai tsaye suka shafi irin salon waƙar yara. Ƙari kuma a kan waɗannan shi ne akwai kalmomi masu bayyanannun ma’anoni da gajejjerun jimlolin da suke ɗauke da ƙwayoyin tunani ƙalilan. Wato jimla ɗaya, ƙwayar tunani ɗaya. Dubi wannan baiti game da ɗan makaranta marar kirki:

A cikin aji in an shiga
Abada yawan barci garai

Haka nan kuma:

Ai gwamma kwananai zama
Falken yawan yaya garai

Ko kuma:

Almajiri duk yaz zamo
Haka dambala ta zo garai

Wazirin Gwandu bai cika kowane daga baitocin waƙarsa da tarin ƙwayoyin tunani waɗanda ƙwaƙwalwar yaro za ta fuskanci matsalar riƙe su ba. A maimakon haka sai ya kawo ƙwayoyin tunanin daki daki, baiti na bin baiti.

Daga cikin muhimman abubuwan la’akari akwai salon jan hankali wanda ya ƙumshi jan yara a jika da ƙarfafa ko jaddada kalma ko saƙo. Haka kuma akwai salon hira da na labari.

Idan waƙa ta ƙumshi maganganun da suke jefa yara cikin tunanin cewa da su da mai waƙar ne suke cikin wannan waƙa, to kuwa akwai ƙarfafa zaton cewa waƙar za ta karɓu ga yaran. Misalin irin wannan ja a jika ya zo a farkon “Waƙar ‘Yan Makaranta” a inda Wazirin Gwandu yake cewa:

Ku ‘yan uwana duk ku zo
Ku ji gargaɗI in na faɗai

Zancen ga ba ni naf faɗe
Shi ba malamina yaf faɗai

Almajirai muke ni da ku
Gun malami muke tun daɗai

Malam ka yo mana gargaɗI
Mu tsaya mu ji shi mu ko riƙai

Waɗannan baitoci sukan sa yara su ji kamar a matsayi ɗaya suke da su da malamin da ya zaɓo musu wannan waƙa. Wato dukkansu ‘yan makaranta ne, abu guda ne ya shafe su, kuma a jiha ɗaya rayuwarsu take tafiya. Baitocin ba su yi amfani da lafazin dangantakar yaro da babba ba. A’a lafazi ne na dangantakar masu matsayi iri guda.

Irin wannan salon na ja a jika ya fito a baitocin da suke bayani a kan ɗan makaranta marar kirki. A waɗannan baitoci Wazirin Gwandu ya ware wannan ɗan makaranta marar nagarta ya ajiye shi a gefe guda, daban da sauran ‘yan makaranta nagari. Ya nuna cewa ko kusa da shi da ‘yan makarantar ba a matsayi guda suke da wancan marar kirki ba:

Da fita aji ya garzaya
Wajjemmu ba matsaya garai 

In son ganin samnan kakai
Tafi can tashar mota tarai.

Iske shi hotel gun mashaya
Dud da ‘yak kwalba garai

Wato shi wannan ɗan makaranta ba ya cikin su Waziri da ‘yan makarantar da ya kira “yan uwana”. Saboda haka ne ma idan aka tashi daga makaranta wannan ɗan makaranta marar kirki ba ya tunanin ya zo inda “muke” (wajjemmu), a’a sai dai ya garzaya can tashar mota wurin ‘yan iska ko kuma ya tafi mashaya wurin ‘yan giya.

Salon ƙarfafawa ko jaddawa a cikin waƙoƙin yara ya shafi maimaita saƙo ko kalmomin da suke ɗauke da saƙon. Muhimmancin wannan kuwa shi ne taimaka wa yara wajen lura da riƙe saƙon da ke ciki, har su fahimce shi. Kalmar almajiri da waɗanda suke da dangantaka da ita sun sha maimaitawa a cikin “Waƙar ‘Yan Makaranta”. Saƙon da wannan kalma ta ƙunsa a fili yake: marubucin yana son yara su ji cewa wannan waƙa tasu ce kuma duk abin da waƙar ta ce ya shafi rayuwarsu. Haka kuma an maimaita kalmar garai, wato gare shi a kai –a kai cikin wannan waƙa. Dalili shi ne ana so yara su fahimci cewa maganar da ta gabata ta shafi wanda ake magana a kansa, wato almajiri. Ga misali:

Wada anka so almajiri
A ishe hali mai kyau garai

Duk lokacin sallah shina
Tsare, dud da tasbi ag garai

Mai hankali mai girmamawa
Har a san ladabi garai

Shi fake amana malami
Shi tsare umurninai garai

Na gabansa ko ba malamai
Ba shi zan tsaron girma garai

Hasali a cikin baitoci 83 da waƙar ta ƙunsa, 69 ne suke ɗauke da wannan kalma ta garai,

Har ila yau akwai salon hira wanda yake da muhimmanci ga dacewar waƙa ga yara. Yara mutane ne masu son su saurari labari mai daɗi, ko a yi labari da su mai daɗi. Idan baitocin waƙa suka ƙunshi labari tsakanin mutane za mu ce baitocin suna ɗauke da salon hira. Idan kuwa mai waƙar ne ko wani a cikin waƙar yake bayar da labarin shi kaɗai to sai mu ce waƙar tana ɗauke da salon labari.

Salon hira da na labari sukan gurguso da yara kusa da waƙa. Wato salailan sukan sanya tunanin yara masu sauraro ko rera waƙa cikin tunanin mai waƙa ko kuma tunanin da waƙar take ɗauke da shi.

“Waƙar ‘Yan Makaranta” cike take da waɗannan salailai musamman salon labari.Waziri ya nuna tun a baiti na 4 da na 5 cewa labari ne zai ba ‘yan uwansa almajirai:

Ku ‘yan uwana duk ku zo
Ku ji gargaɗI in na faɗai

Zancen ga ba ni naf faɗe
Shi ba, malamina yaf faɗai 

A baiti na 54 zuwa na 56 na wannan waƙa marubucin ya yi kusa da salon hira domin maganarsa kai tsaye ta yi zuwa ga mai sauraren sa: 

In son ganin samnan kakai
Tafi can tashar mota tarai

Iske shi hotel gun mashaya
Dud da ‘yak kwalba garai 

Ɗan bincike shi kaɗan
Cikin taggo akwai wiwi garai

Kalmar tafi da iske da ɗan bincike duk a umurni ne ga mai sauraren waƙar, wato almajirai. Ta amfani da waɗannan kalmomi sai mai saurare ya ji da shi fa ake magana, ba da wani ba.

Zubi Da Tsarin Waƙa

Muhimmin abin la’akari game da zubi da tsarin waƙoƙin da malami zai zaɓa wa yaransa shi ne taƙaitawa. Taƙaitawa ta fuskar yawan kalmomi da taƙaitawa ta fuskar yawan ɗangogin baiti da kuma taƙaitawa ta wajen yawan baitoci.

Mun riga mun lura da cewa waƙa mai ɗangogi masu tsawo suna ƙumshe da kalmomi masu yawa, ko bayan sassarƙiyar da suke da. Saboda haka abin nufi dangane da taƙaitawa ta fuskar kalmomi shi ne, waƙa ta ƙunshi kalmomi marasa yawa a cikin ɗangogin baitocinta. Kalmomi marasa yawan da ake nufi su ne masu mihimmanci a cikin a saƙo. Misali dubi wannan baiti. 

Tsince gare shi da tsegumi
Haka nan yawan ƙarya garai

A nan muhimman kalmomi uku ne rak; tsince da tsegumi da ƙarya. A wasu baitoci ma tserayyar ma’ana tsakanin muhimman kalmomi ba ta da yawa:

Wanki shikai wanka shikai
Ɗakinsa ko shara garai 

Muhimman kalmomi masu makusanciyar ma’ana a wannan baiti su ne wanki da wanka da shara. Kalmar ɗaki muhimmiya ce a cikin baiti wadda kalmar shara ta liƙu gare ta.

Haka kuma abu ne muhimmi ɗangogin waƙa su zamo gajejjeru marasa tsawo. Wannan yakan taimaka wa yara su ji sauƙin fahimta kamar yadda za su ji idan baitocin waƙar suka kasance da ɗangogi kaɗanna. Wato kenan “Waƙar ‘Yan Makaranta” ta dace da wannan bayani. Dangoginta gajejjeru ne sannan baitocinta ‘yan ƙwar biyu ne, kamar dai yadda baitocin da aka kawo don misali a wannan maƙala suke nunawa.

Kammalawa

Ta amfani da “Waƙar ‘Yan Makaranta” ta Wazirin Gwandu, Alhaji Umaru Nasarawa, wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fito da muhimman abubuwan la’akari wajen zaɓen rubutattun waƙoƙin Hausa domin yara.

Waɗannan muhimman abubuwan la’akari, ko gimshiƙan gina waƙoƙi domin yara su ne lafazi ko harshe mai sauƙi ta fuskar ma’ana da kuma dacewa, da saƙo wanda yake la’akari da tunani da duniyar yara, da salo mai jan hankali kuma miƙaƙƙe, kai tsaye zuwa ga manufa, da kuma zubi da tsarin da yake ɗauke da sifar taƙaitawa ta fuskar kalmomi da ɗangogi da kuma baitoci.

Maƙalar ta buɗe da bin diddigin samuwar rubutattun waƙoƙin Hausa domin yara a taƙaice. Daga nan sai ta tsunduma cikin nazarin gimshiƙan da ta ƙuduri ganowa. Ko kusa maƙalar ba ta nufin cewa waɗannan gimshiƙai su ke nan, sai dai cewa suna daga cikin muhimmai8.

Tushen Bayani 

1. Duba A.B. Yahya (1997), Jigon Nazarin Waƙa, FISBAS, Kaduna, Shafi na 49-55.

2. Isa Ɗan Shehu Ɗanfodiyo, “Waƙar Alhakin Mumini Bisa Mumini Da Tarbiyyar Yara.”

3. Kundin Bello Sa’id (1978) “Gudummawar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa”, na digiri na biyu a ABC/ABU, bai kawo irin wannan waƙa ta yara ba. Wannan kundi kuwa bai da na biyu ta fuskar waƙoƙin ƙarni na 19.

4. Tuni aka buga wannan waƙa da sunan Waƙar Nijeriya, NNPC (1973).

5. Duba E. H. Jones Jr. (1968) Outline of Literature Macmillan, (New York), shafi na 89.

6. Alƙali Alhaji Haliru Wurno, (1989) “Ma’anar Waƙa” baiti na 26, (ba a buga ba).

7. Duba M.G. Maitafsir (2001), Child Development and Learning in Psychology, Milestone Information and Publishing House, Sokoto, da A.A. Sheikh da A.B. Yahya (1999) Wannan Yaro!! FISBAS Media Services, Kaduna, duk suna ƙara haske ta wannan fuska.

 8. Wannan magana haka take domin lokacin da aka rubuta wannan maƙala ta asali, kafin a yi bitar gyararraki, ta kasance da siffarta ta yanzu, babu wani aiki mai zurfi a kan wannan jigo. To amma alhamdulillahi, a halin yanzu akwai wani gagarumin aiki mai muhimmancin gaske dangane da zaɓen rubutattun waƙoƙin Hausa domin yara. Wannan aiki shi ne kundin digiri na uku (Ph.D) na Atiku Ahmad Dunfawa wanda ya gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a shekarar 2002. Sunan wannan kundi kuwa shi ne “Waƙa A Tunanin Yara”.

Manazarta

Cohen, B.B. (1973) Writing About Literature, Illinois, U.S.A Dunfawa, A.A. (2002), “Waƙa A Tunanin Yara”, kundi Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.

Hisket, M. (1975), A History of Hausa Islamic Verse, London

Jones, E.H (1968), Outline of Literature, Short stories, Novels & Poems, New York.

Kwantagora (1977), Gama-Gari Ruwan Dare Oxford.

Maitafsir M.G. (2001), Child Development and Learning in Psychology, Sokoto.

Shagari, S. (1973), Waƙar Nigeriya, NNPC, Zariya

Sheikh, A.A. da Yahya A.B. (1999) Wannan Yaro!! FISFBAS, Kaduna.

Umar, M.B. (1979), Waƙoƙi Don Yara, Hudahuda, Zariya

Yahaya I.Y. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, NNPC, Zariya.

Rubutun wakoki

Post a Comment

0 Comments