“Na rubuta wannan maƙala domin tunawa da Alƙali Alhaji Haliru Wurno, ɗan uwa kuma masoyi. Allah ya yi masa gafara ya sa shi cikin aljannarsa Firdausi cikin rahamarsa da jinƙansa, amin.” (Prof. A.B. Yahya)
Daga
Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Email: bagidadenlema2@gmail.com
Phone: 07031961302
Tsakure
Raha haliyyar ɗan Adam ce. Ita kuwa haliyya
takan yi tasiri a kan rayuwar ɗan Adam. Ana iya ganin tasirin wannan
haliyya cikin waƙoƙin da Alƙali Alhaji Haliru Wurno ya rubuta. Waɗannan waƙoƙi kuwa sun ƙunshi jigogi mabambanta,
kama daga waɗanda suke sakayau kuma maɗauka raha, zuwa ga masu nauyi waɗanda bisa ga al’ada, manisanta ne da
raha. Saboda haka ne wannan maƙala take kallon wannan tsattsafi na
raha a matsayin salon marubuci na gaba ɗaya cikin waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno. A
taƙaice tsattsafin raha shi ne salon waƙoƙinsa na gaba ɗaya, da shi ne za a iya a ce wannan waƙar Haliru Wurno ce ko kuma ba ita ce ba.
A ƙoƙarin tabbatar da haka maƙalar ta fara da gabatarwa wadda ta ƙunshi bayani a kan kalmomin fannu, da kalmomin ƙumshiyoyin tunani masu nasaba da haliyyar raha, da kuma taƙaitaccen tarihin Alƙali Alhaji Haliru Wurno.
Daga nan sai maƙalar ta shiga yin nazari a kan wuraren
da haliyyar raha ta samu tsattsafi cikin waƙoƙin mawaƙin. Ta kuwa haɗa wannan tare da misalai domin kafa
hujja.
Gabatarwa
Babban ƙudurin wannan maƙala shi ne tabbatar da
cewa tsattsafi, wato barbaɗi ko yayyafin haliyar raha shi ne salon waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno.
Salo ne wanda ya zo a ƙarƙashin abin da Abdulƙadir Ɗangambo ya kira Salon marubuci
na gaba ɗaya1
To amma kafin maƙalar ta nuna gaskiyar
wannan hasashe zai dace ta fayyace wasu kalmomin fannu da ƙamshiyoyin tunani. Sanin haka ne madafa ga fahimtar
gundarin saƙon da maƙalar take ɗauke da shi.
Kalmomin
Fannu Da Ƙumshiyoyin Tunani
Muhimman kalmomin fannu a wannan nazari su ne tsattsafi da haliyya. Su kuwa ƙumshiyoyin tunani masu nasaba da raha su ne fara’a da nishaɗi da ban-dariya da shammata da ba’a da bananci da kuma barkwanci
Tsattsafi yana nufin salon kawo wata
magana (wato, saƙo ko jigo) ko cusa wata haliyya ko
kuma amfani da wani salo a kai a kai (wato, a yayyafa ko a barbaɗa) cikin waƙa ko kuma mafi yawan waƙoƙin marubuci. Idan muka ƙaddara waƙa a matsayin wani fili mai faɗi, sannan muka ɗauko wani abu kamar gari muka barbaɗa shi a wannan fili, garin zai kasance
wanda ake iya gani a nan da can a cikin filin. Saboda haka an samu tsattsafin
gari cikin wannan fili. Kiran wannan salo da sunan tsattsafi ba
barbaɗi ko yayyafi ba, waɗanda duk masu dacewa ne, ya zo ne
domin yin ishara da ‘daɗi’ ko ‘zaƙin’ da salon yake ba waƙa. Wato wannan salon,
tsattsafa ce, tsattafa kuwa da zuma akan yi ta.
Haliyya tana nufin
yanayin ko ‘labarin’ zuciya wanda waƙa take
tattare da shi. Yanayi ne da kalmomi da yadda suka zo cikin waƙa suke cusa wa mai karatu ko sauraren waƙa. Haliyya
tana iya zama ita ce wadda zuciyar marubuci take ciki a lokacin da yake rubuta
waƙarsa, ko kuma haliyyar da ya cusa wa kansa da gangan domin
waƙar da yake a kan rubutawa ta ƙunshe ta.2 Ga alama haliyya za ta fi jigo
ko salo jawo muhawara a tsakankanin manazarta waƙoƙi saboda nasabarta da zuciya.
Kalmomin raha da fara’a da nishaɗi dukansu haliyyoyi ne masu ma’anonin da suka yi kusa
da juna. Dukansu nau’o’i ne na farin ciki. A yayin da farin ciki ya wanzu a
matsayin kalmomi biyu na tsagwaron harshen Hausa, su kuwa kalmomin nan uku ga
alama su ne suka maye gurabun takwarorinsu na harshen. Masana harshen Larabci
su ne da ilmin fayyace yadda suke. A harshen Hausa dai raha tana nufin
sakankancewar zuciya cikin walwala da rashin damuwa. Ita kuwa fara’a tana nufin
jin daɗin rai(zuciya) mai haskaka
fuska. Nishaɗi yanayin zuciya ne
makamancin raha kuma mai saurin ingiza mai shi ne ga yin abubuwa na walwala.
Abin da wuya ( ba da kamar wuya ba), har dai ga wanda ba masanin Ilmin
Mutuntaka ba.
Ban dariya shi ne abu ko aikin da yake
sa a yi dariya ko murmushi. Su kuwa waɗannan ayyuka dukansu masu bayyana
haliyar raha da dangoginta ne. Shammata cikin magana tana nufin a faɗi wani abu game da mutum, na jikinsa
ko halinsa, domin muzantawa wadda za ta kawo a dare shi. Ba’a tana kusa ga
shammata wajen ma’ana fiye da bananci. Wato faɗar magana ga wani domin ta ba shi
haushi a yi dariya, ga ta nan dai kamar wani ƙaramin zambo. Shi kuwa barkwanci magana ce mai kawo dariya
gaya ko da kuwa ga lamarin da ya riga ya ɓaci ne.
To duk waɗannan abubuwa, tun daga ban-dariya har
zuwa barkwanci, ayyuka ne waɗanda suke bayyana samuwar raha tattare da mai aiwatar da
su. A. wannan maƙala abubuwa ne da ke bayyana raha
cikin waƙa musamman a baitoci ko ɗangogin da suke. Abubuwa ne da
watakila suke yin ishara ga halin marubucin waƙa na kasancewa mutum wanda
raha ta rinjayi fushi da damuwa da baƙin ciki, da dai dangogin
waɗannan, a cikin rayuwarsa
gaba ɗaya. Abin nufi a nan shi
ne marubucin da ake iya siffanta salon waƙoƙinsa na gaba ɗaya da cewa salon raha ne, to ana
kyautata zaton cewa mutum ne mai fara’a, mai dariya kuma wanda ba ya barin
damuwa ko baƙin ciki ko ɓacin rai, ɗayansu ko dukansu, su nauyaya
rayuwarsa. Mutum ne mai tarbon abin da ya zo masa a yadda ya zo masa. Idan
na ɓacin rai ne, ya nuna ɓacin ransa, amma kuma ba zai bari ya
faifaye ba, domin rayuwa ba ta kasance ɓacin rai duka ba. Haka ne zai yi da
sauran faɗi-tashin rayuwa. Hasali ma
yakan yi ƙoƙarin sassauta su.
Da wannan bayani ne maƙalar za ta juya zuwa ga taƙaitaccen tarihin rayuwar
Alƙali Alhaji Haliru Wurno.
Alƙali
Alhaji Haliru Wurno
A wannan ɓangare za a fi mayar da hanakali a kan
halayen Haliru Wurno kamar yadda marubucin wannan maƙala ya san shi.3
An haifi Haliru Wurno cikin shekarar 1925 a ƙauyen Ƙwargaba na ƙasar Wurno ta Jihar Sakkwato. Abin lura a nan shi ne Haliru
Basakkwace ne kuma Bagiɗaɗe. Sarauta ce ta kai kakansa a Wurno
inda ya yi Sarkin Rima. A wata waƙar madahu wadda ya kira ‘Ƙorama’ Haliru ya ce:
Waƙar yabon Manzo ga raina
nif fake
Ƙarin bayanina usulu ina shike
Bari in faɗa maka inda dangina suke
Kwat tambaya birni na Sakkwato nan
suke
Manyan Giɗaɗawa gidan albarka.
(Ƙorama)
Haliru ya sake kawo irin wannan bayani
a wata waƙarsa mai suna ‘Jirgi’, ita ma ta
madahu, inda ya ce:
Alhaji yay yi waƙag ga Alƙali ga dauri
Nan shinkafi niy yo ta niy yabi
Annabin ga
Bayan Azzuhur tat taho min nir rubuta
Ran Narba watan Hajji niy yabi Annabin
ga
Salla na da kwananta ukku ji in faɗa ma
Ƙarshen Rajmu mai hajji shi ka sanin hakan
ga
Kun san Wurno birninsu ta can anka
haifai
Sakkwato yay yi wayo cikin
Birnin ƙasag ga
Sarkin Rima Kakansa na bari in faɗa ma
To Maigandi tsohonsa na in ka ji wagga
Shi ad Daudu can Wurno wan Mallam Alu
na
Mallam Shaihu Mallam Yahayya ‘yan uwan
ga
Sa da Magaji Mamman Marafa ji in faɗa ma
Diba “Ƙorama” na yi ma zanen waɗanga.
(Jirgi)
Saboda haka Haliru yana da dangi a Sakkwato kuma yana da su
a Wurno, kamar dai yadda Sakkwatawa da dama suke. Bari ma ta wannan, da
Sakkwato da Wurno sun yi tarayya ga sunayen shiyyoyin da ke cinkinsu.
Haliru Wurno ya tashi cikin zuri’ar da
ilmi ne safararsu. Wato Giɗaɗawa, waɗanda suka samo sunansu daga Usman Giɗaɗo ɗan Laima. Shi kuwa Giɗaɗo shi ne wazirin Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello ɗan Shehu Usmanu ɗan Fodiyo, Allah ya yi mu su rahama,
amin. Bagiɗaɗe ba ya da wani abin tinƙaho da ya wuce ilmi da neman sa. Saboda haka Haliru ya buɗe ido da neman sani. Ya yi karatu a
gida da kuma makaranta kamar sauran giɗaɗawa. Ya yi karatun allo da na sani a
makarantar Liman Macciɗo a garin Sakkwato4 Haka
nan kuma ya yi karatu wurin wasu malamai, a cikinsu kuwa har da dangisa
musamman kakanni da iyaye. Waɗannan sun haɗa da Waziri Junaidu da Malam Joɗi. A Wurno ya yi karatu wurin Malam
Bayero da Malam Abubakar Uban Lale. Waƙoƙin Alƙali Haliru Wurno sun isa shaida ga
irin tarin sanin da ya tsotsa daga waɗannan malamai. A cikinsu yakan kafa wa
duk maganar da ya faɗa hujja daga Alƙur’ni Mai Tsarki da Hadissai da kuma littattafan magabata.
Misali, bayan da ya ambaci sunayen iyaye da ‘yan uwansa cikin wasu baitoci na
waƙarsa ta madahu, sai ya kawo wannan baiti:
An so sanin dangi ga aya na ga ta
Ka sano zumunta taka to kyauta mata
Wada nig gani kuma nik karanta tabbata
Ban yo faɗin ga ba don fahar na tabbata
Li ta’arafu ayag ga tah hore ka.
(Ƙorama)
Kai mai karatu da ganin wasu waƙoƙin Haliru ka san sai zuzzurfan ilmi
yake iya saƙa su. A wata waƙarsa ta wa’azi ya taɓo tauhidi inda yake cewa:
4Mu yo kalimar shahada tun da farko
Mu tabbata shi kaɗai na bai gushewa
5.Mu yarda mu shaida shi Ɗai na Guda na
Da yaz zam tun azal yake babu kowa
…
Ina rani ina kaka da ɗari
Ina suke tun da babu ruwan
zubawa
Azal yake tun azal yake ko azal ma
Ga Allah ba azal don babu kowa
(Yana Wa’azin Ku Har Shi Bai Cirewa)
Tsakanin shekarar 1943 da 1947 Haliru
ya yi makarantar horar da alƙalai ta Sakkwato, wato “Sokoto Qadi
School” a Turance. Daga cikin malamansa a wannan makaranta akwai Waziri Junaidu
da Malam Ahmadu Ɗan Hannun Giwa.
Haliru yana sauka a wannan makaranta
sai ya zarce zuwa makarantar nazarin ilmin Sharia ta Kano, wato ‘Kano Law
School’. Ya shekara huɗu a can inda ya kammala a
1951. Malamansa a wannan makaranta sun haɗa da Shaikh Awad Muhammad Ahmad da
Malam Nasiru da kuma Malam Abubakar Gumi.
An ɗauki Haliru aiki bayan da ya kammala
karatu a makarantar Kano, a matsayin malami mai karantar da ilmin addinin
Musulunci da Larabci a makarantar Maru wadda a lokacin ake kira Elementary
Training Centre (E.T.C.) Maru. To amma bayan shekara ɗaya da wata shida sai aka ɗauke shi aiki a ma’aikatar shari’a ta
lardin Sakkwato. Ya yi aiki nan a matsayin akawun kotu tun daga 1952 har zuwa
1965, lokacin da ya bari ya koma ga karantarwarsa. Ya zauna a makarantar
Nizamiyya ta ‘Yar Akija a garin Sakkwato a matsayin malamin addini da Larabci.
A lokacin ne ya rubuta ‘Waƙar Fanda’ ko ‘Waƙar Danja’ wadda ta shahara a tsakankanin ‘yan makaranta a
Sakkwato da kewaye.
Shekara biyu da ‘yan watanni ya yi
yana karantarwa a Nizamiyya kafin ma’aikatar shari’a ta neme shi da ya koma ya
yi alƙalanci. Ya karɓi wannan gayyata ya kuma ci gaba da
aikin har zuwa 1981 lokacin da ya bari don ganin damarsa, ya sake komawa ga
karantarwa.
Ta fuskar aikin shari’a Haliru ya
zauna garuruwa da ƙauyuka da dama na jihar Sakkwato.
Haliru ya ambaci wasu daga waɗannan wurare cikin wata waƙar wa’azi da nasiha da
komawa ga Allah Ta’ala:
Ji Alhaji Wurno Alƙali na dauri
Ina tuba ga Rabbul alamina
Ka yafe min zaman Maru har Bakura
Maradun mufti wayyo ni jiƙai na
A Sabon Birni Gobir nai zama can
Bakwai na shekare Gobir zamana
Ka yafe min zaman Gwadabawa shi ko
Kurena ko da gangancin halina
(Sabilul Haƙƙi Bi Ƙaulis Sidƙi)
Sauran wuraren da ya sha ambata
cikin waƙoƙinsa sun haɗa da Yaldu da Silame da Tangaza da Raɓa. Su kuwa garuruwan da ya zauna
lokacin karantarwar da ya yi sun haɗa da Maru da Wurno da Sakkwato. A
Sakkwato ne kuma Allah ya karɓi ran Haliru cikin gidansa na Kwalejin Abubakar Gumi Ta
Fasaha Da Larabci, ranar
Alhamis 16 ga Oktoba na 2003 bayan
sallar La’asar kuma kusan sallar magariba.
Alƙali Alhaji Haliru Wurno
mutum ne wanda duk wanda ya san shi zai tabbatar da kasancewarsa mutum mai
fara’a da sakin fuska. Da wuya mutum ya iya haƙiƙance fushinsa, muddin dai fushin bai danganta da saɓon Mahalicci Allah Ta’ala ba. A nan ma
Haliru ya kasance mai hucewa ya dawo yana lallashin mai saɓon, yana nuna masa aibin saɓon da ya sa shi Haliru ya fusata.
A ƙarshe zai saka wannan mutum cikin
halin nadama da kuma dariyar kansa da kansa duk a lokaci guda. Haliru ba ya
bari abokin hulɗarsa ya bar gidansa cikin ɓacin rai, saboda wai wata magana da
shi Haliru ya faɗa masa. Shi a kullum
na’am-na’am yake yi da jama’a. A ra’ayin marubucin wannan maƙala, tabbas! Haliru ya gadi abubuwan da shi kansa ya faɗi game da kakansa Waziri Junaidu cikin
wannan baiti:
In mutum ya ƙi gaisai shi gaishe shi
Shi da baƙonsa dan nesa zai tashi
In fa ya san ka ko kai fa kas san shi
Ba ka cewa da baƙi ga ƙirjinshi
Ga sakin fuska ko ba ka san shi
(Waƙar Yabon Waziri Junaidu)
Haka kuma lalle baitin nan da Haliru
ya yabi Sarkin Musulmi Abubakar III da shi, shi kansa Haliru Wurno tsaf da tsaf
ya dace da shi:
Son zumunta da hani da alheri
Ga zalaƙa kuma ga shi ba kibri
Ga sakin fuska ga shi mai sabri
Ga amana koyaushe ba sharri
Ƙeta ko can bai gane sunanta
(Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)
Wani halin Haliru shi ne karimci. Duk
wanda ya san wannan bawan Allah to kuwa zai shede shi da irin wannan hali.
Haliru masoyin zuma ne kuma mai yin iyakar ƙoƙarinsa ne ya ga ya yi tanadin ta a gidansa. Idan ya yi baƙo sai ya haɗo da faraufarau na zuma cikin tarbar da zai yi masa. Abu ne
mawuyaci ka baƙunci Haliru ya kasa tarbon ka da wani
abu na sa wa a baka, sai dai abin nan ya ƙaranta. Idan ma baƙo bai tarar da kome ba to aƙalla Haliru zai cusa masa
fara’a da maganganun da zai yi masa. Wani ƙanen mai maƙalar nan ya ba da labarin cewa lokacin da yana ɗan makaranta a Tangaza shi kuma Haliru
yana alƙalanci a can. To takanas ne Haliru zai
aika a ɗauko masa ƙanensa daga makaranta, ba don kome ba sai don ya gane shi
ya yi masa alheri. Yakan zaunar da shi a kan shimfiɗarsa ya sa a kira mai balangu, ya yi
ta yanka masa nama. Yaron zai ci naman nan har ya gundure shi, amma ba fasa
yanko masa ake yi ba. Kai ta kai har sai ya kaikaici idon mutane ya yi sauri ya
hankaɗa shinfiɗa ya ɓoye nama. Bayan duk wannan, idan zai
koma makaranta sai a ƙumsa masa a kuma haɗa masa da masu gida rana!5 Babu
wata tantama idan mutum ya san Haliru zai tuna da wannan karimci nasa idan ya
karanta waɗannan baitoci na waƙarsa ta madahu:
Baƙo idan ka yo shi kawo mai
zuma
Masa da ƙosai to ka yo mishi sallama
Kuma kai fura sannan da ƙosan alkama
Daifun mabuɗi na ga Aljanna zama
Manzon Ta’ala yaf faɗi mun ɗauka
In ka ga baƙo ya taho maka kar ka ce
Koma ka ba ni wuri ka san
suturakka ce
Ka yi mai maraba ka ba shi ci haka
anka ce
Koway yi baƙo yay yi mai wada anka ce
An buɗa aljannakka don baƙonka.
(Ƙorama).
Idan kuwa aka nemi sanin kamannu da
suturar Haliru6, to wannan ɓangare zai misalta. Haliru dai mutum
ne mai tsayi wanda tun daga nesa ake iya hango cewa ya kere mafi yawan na tare
da shi Baƙi ne ga launi kuma mai tsawon fuska.
Idonsa matsakaita ne ga girma, sannan kuma yana da faɗin goshi da tsawon hanci, da baki mai
siraran leɓɓa. Idan yana maganar da ya
tabbatar da cewa ƙaƙƙarfar hujja ce, tun ma ba
a ce daga nassi hujjar take ba, idonsa sukan turo waje su kuma kafe a kan wanda
yake magana da shi.
Haliru ya kasance mai son sutura
wadatacciya, mai kammala Bahaushen mutum.Wato tufafinsa su ne riga da taguwa da
wando mai faɗi da hula da rawani. Idan
akwai rana mai kaifi yakan sanya baƙin tabarau. Waɗannan tufafi su ne na fitarsa. Idan
kuwa a gidansa yake, to idan bai zauna haka nan da su ba yakan cire riga ya bar
taguwar, wadda a koyaushe mai tsawo ce har zuwa rabin ƙwaurinsa. Haƙiƙa wannan baiti na tafe ya zayyana irin fitar Haliru:
In za ka salla yo naɗi da mubarrashi
Manyan tufafi masu kyau na haɗallashi
Kuma zanka yin fara’a ka samu
tagomashi
Azumin da kay yi yini guda lillahi shi
Ka tsira shekarru da kai da wutakka
(Ƙorama)
A fagen waƙa Haliru gwani ne na ji da gani. Waƙa a wurinsa kamar maganar yau da kullum ce. Wato mai ƙaƙa waƙa ne a duk lokacin da ya
tashi ko aka bukace shi da ya yi ta. Baiwa ce Allah ya yi masa. Haliru
marubucin waƙa ne a koyaushe, kuma cikin kowane
irin hali yana iya yin ta. An taɓa tambayar sa yadda waƙa takan zo masa sai ya ce babu yadda ba ta zo masa,
matsalarsa guda ita ce idan bai da alƙalami da takarda a
hannunsa. Wato muddin dai yana tare da waɗannan to kuwa waƙa tana zo masa7 Tamkar dai lisafin da za a
gabatar wa Ka-fi-Komfuta-Sauri na Zariya8
Haliru ya fara rubuta waƙa tun yana ɗan shekara goma sha biyar, kuma abin
mamaki da harshen Larabci ya fara9 Wato ke nan ba a Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya ne kurum za a iya nazartar gudunmawar da Haliru ya
bayar ga al’umma ba. A’a, har ma da Sashen Koyar da Harshen Larabci. To a ɓangaren rubutattun waƙoƙin Hausa Haliru ya faɗi cewa shi kansa bai san ko waƙoƙi nawa ne ya rubuta ba. Abin da wannan
bincike da waɗanda suka gabata suka
tabbatar shi ne waƙoƙin ba kaɗan ne ba. Da yawa daga waƙoƙinsa bai ba su suna ba, abin da
manuniya ce ga cewa Haliru mai zara ne ga tunani da rubuta waƙa da kuma ƙaiƙayin hannu wajen rubuta ta10.
Jigogin waƙoƙin Haliru masu yawa ne. Ya rubuta a
kan madahu da wa’azi da nasiha da yabo na mutane da kishin ƙasa da waƙa ita kanta. Haka nan kuma ya rubuta a
kan gyaran al’umma da ɗanɗana da faɗakarwa da ilmi da tauhidi da ƙwarewa ga harshen Hausa da addu’a da marsiyya da kuma
soyayya, kai, har ma da waƙoƙi a kan kansa. Ya kuma
rubuta waƙoƙi a kan al’adu da waƙoƙin yara da martani da siyasa ta
gaba ɗaya da ban kwana da abokai
da ‘yan uwa.Waƙa a wurin Haliru zuwa take yi ba ƙaƙƙautawa, kamar yadda baitocin nan suke
da saresarin faɗar haka:
Waƙar da niy yi yabon mutane
na tuna
Na wa aminnai ‘yan uwa na yo kina
Wasu ko ga fili nif faɗi nib bayyana
Na ɗaura waƙoƙi ubana yah hana
Ta yabon mutane na bari sai taka
….
Waƙar mutane na yi ga ta a
kai a kai
Wasu na yi zambo sun ji har aike nikai
Wasu na yaba su suna biɗa aike sukai
Na rera waƙoƙin saraki hakimai
Na ya da saiɓi ‘yan kazagge ka ɗauka
(Ƙorama)
Haliru bai tsaya a kan rubuta waƙoƙinsa kurum ba. Ya yi wa waƙoƙin wasu tahmisi sannan kuma ya yi wa
nasa tahmisin! Ya kuma yi wani abu wanda saboda rashin kalmar da ta dace, zan
kira bin sawu na wani mawaƙi ko wata waƙa. Bin sawu yana nufin a samu mawaƙi ya rubuta waƙa wadda
ta ɗauko
jigo ko jigogi, da kari da jimloli, har ma da salo, irin na wata waƙa ɗaya (ko fiye) ta wani mawaƙi dabam, har wannan waƙa ta
daga baya ta kasance kamar dai waccan ce ta farko. To amma fa akwai bambanci duk da
waɗannan kamannu. Waƙar Haliru mai suna “Tura Ta Kai Bango” misali ne na bin
sawu. Waƙar ta bi sawun shahararriyar waƙar nan ta Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa, mai suna
‘Zaɓaɓɓiya’. Dubi wannan misali:
Zaɓaɓɓiya (Alhaji Umaru Nasarawa Wazirin
Gwandu) |
Tura Ta Kai Bango (Alƙali Alhaji Haliru Wurno) |
1. Na kirayi mai iya jinƙai na Wanda shi ka ɗaukaka sunana Nan da nan shi kammala girmana Tun da na kirai ban donewa 7.Ko da ban yi ƙwazon komi ba Ya Azimu kai ɗai nika duba Tun da ko daɗai ban san wani ba Ban da kai Guda Mai gyarawa 9. Can wurin da kac ce ‘Fad’u ni Astajib lakum’ ba nisyani ‘Ba-ni-ba-ni’ bai sa ma ramni Naka arziki bai ƙarewa 12. Dauri anka kasan nid daure Anka koma kasan nij jimre Yanzu hanƙurina ya ƙare Ƙadiran nufan ni da ramawa 18.Ga garinmu ban kwana daji Ga Ka ban biɗar wani budeji Tun da na sani Kai am Munji Malja’inka nan nika dagewa 50.Wanda yay yi waƙa sunanai ‘U’ da ‘Ma’ da ‘Ru’ ga
mazamninai Sai ka zo ka ‘Bi Ke’ birninai Nasarawa can kaka komawa |
1. Na kirayi
Allah Ƙahharu Wanda ad da baiwa Jabbaru Shi ka yafane mini Sattaru Ga ni na yi laifi Gaffaru Nai kure ina son yafewa 18. Ko da ban yi aikin daidai ba Jalla ban fa mance laifi ba Ban ga wanda za ni ya cetan ba Ban da Kai Ilahi don Ɗaiba Ba ni nau muƙamin takawa 23. Rabbu tun da ka ce ‘Fad’u ni’ ‘Astajibu’ Allah kama ni Na ɗime jikina yai ramni Ba ni kai ka bai in ka ba ni Ba ni duk wadat da ka ɗorewa 14 Rabbu dut abina
ya ƙare Dauri anka yo mini na jimre Yanzu hankalina ya tsere Ga shi hanƙurina ya ƙare An buge ni ban iya ramawa 11 Na ɗimauta har na kwan daji Na yi kwance ba inwar gamji Ni kaɗai ga rana sai tuji Wanda bai kiyo ga hakin samji Ya Ƙawiyyu na so komawa 49 Mai biɗat sanin ma’ajin waƙa ‘Ha’u’ ‘Dadu’ ‘Ra’ shi yas sarƙa Wurno ag garinsu gida haƙƙa Fassararsa Alhaji Ishraƙa Ko da yaushe bai rasa shiryawa |
Wannan, a taƙaice, shi ne bayani a tarihance na wannan mashahurin mawaƙi mai basira kuma haziƙi. Mutum ne mai tsoron Allah, mai ƙasƙantar da kai, ma’abuci raha, ga kuma sakin fuska da karimci da son zumunta. Malami ne gwanin bayanin darussa, mai koyi da Sunnar Manzon Rahma (S.A.W.). A duk inda ya zauna, musamman a makarantun da ya karantar, ya kasance malami wanda ɗalibai suke matuƙar ƙauna da kuma son su zama kusa da shi, suna masu girmama shi. Shi ne kuma limami a wuraren. Karantarwa ta kasance cikin jininsa, domin ko a cikin aji, ko a gidansa, ko a hanya, a shirye yake da ya ba da sani, kuma a haka ya bar gidan duniya. Ɗiyauci ne wata jami’a musamman Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta karrama wannan bawan Allah da digirin girmamawa na D.Litt. Wannan shi ne Alƙali Alhaji Haliru Wurno. Allah ya yi masa gafara ya ba shi mafi darajar karramawa, gida a aljannar Firdausi. Amin.
Tsattsafi
Bayani ya gabata cewa tsattsafi wani salo ne na yayyafa ko
barbaɗa wata magana (jigo), ko
haliyya, ko ma wani salo daga salailai, cikin waƙa ko waƙoƙin mawaƙi. Idan a waƙa guda ce salon yake sai a ce akwai tsattsafin abu kaza a
cikinta. Idan kuwa a cikin dukkan ko mafi yawan waƙoƙin mawaƙi ne salon yake, sai a ce
akwai tsattsafin abu kaza cikin waƙoƙinsa. A nan sai a kalle shi a matsayin salon mawaƙi na gaba ɗaya domin kuwa salon tsattsafi a irin
wannan siga yakan taimaka wajen tantancewa da waƙoƙin mawaƙi.
Waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno ɗauke suke da tsattsafin raha, duk kuwa
da cewa ya rubuta waƙoƙin a kan ɓangarori da jigogi masu tarin yawa. A
wannan ɓangare kaɗan daga waƙoƙin ne bayani zai mayar da hankali,
amma kuma da nufin waƙoƙin su kasance wakilai na
sauran.
Waƙoƙi ‘Yan
Sakayau
Haliru ya rubuta waƙoƙin da za a iya cewa saƙonninsu sakayau suke. Wato ba masu nauyi ba ne, ba su
bukatar zukata su kasance cike da natsuwa da ladabi. Ba kamar waƙoƙin wa’azi ko madahu ba waɗanda suke sa zuciya ta yi taushi ko ta
natsu tare da tawali’u. Irin waɗannan waƙoƙi masu saƙonni sakayau na Haliru sun haɗa da na soyayya da wasu na yabon
mutane da kuma wasu na ɗanɗana. Babu mamaki idan aka
samu baitoci masu raha cikin waɗannan waƙoƙi, domin kuwa suna da
dangantaka da ita, kuma wasu ma sakamakonta ne. Mai karatu ko saurare zai iya
jin samatar raha a duk tsawon wata waƙa wadda ya yi wa Alhaji Giɗaɗo Yabo. Haliru ya gina waƙar da salon shillo11. Wato mawaƙin bai fara kai tsaye da ainihin jigon waƙarsa ba. A maimakon haka sai muka riƙa ganin sa a wannan wuri da wancan yana neman a riƙa shi ko a taimake shi, amma kuma a ko’ina ya tafi sai ya
gane cewa babu madafa. A wani wuri ma fitar kutsu ya yi. To sai bayan ya ƙare duk wannan jerangiya (salon shillo) sannan ya samu
wanda ya ɗauke shi ya kuma nuna
masa ƙauna. Daga nan ne yabon gwarzonsa ya
fito ɓaro-ɓaro.
Yin amfani da wannan salo na shillo ya
taimaka wa Haliru wajen cusa haliyyar raha cikin wannan waƙa. To amma akwai baitocin da rahar ta fi bayyana. Dubi waɗannan baitoci:
Na ga dila da biri ga kura
Zaki na kusa yah haure ni
Na ce gawa ukku kuna nan
Ba ni zama ƙura ta bito ni
35Na yi gabas wajjen yanyawa
Kila dibaratai ta ishe ni
Na ishe limami yanyawa
Ga ni mu’allimu zo ka
daɗe ni
Na ga ashe shi ma tai zahi
Sa’alabu ya ce tashi ka bar ni
Na yi zugum ya ce kai tashi
Ba ka ganin inwa ta bar ni
Na yi zufa rana ga zafi
Matata ita ma ta bar ni
40Na ce Mallam ka san Allah
Yac ce min ai shi yay yo ni
Na ce dubi hadisin tanyo
Ba ka yi min girman Addini
Na ga kamar maganar ta kam mai
Sa’alabu ya ce kai ka fi ni
Na ga kana iya kanka da kawo
Kwanana huɗu ban da sukuni
Na yi biɗar ƙannen matata
‘Ya‘yana huɗu dut sun bar ni
Na ce assha na sa ƙaimi
Kar ya tumam mini ko ya buge ni
(Gudale)
A waɗannan baitoci, Haliru ya yi amfani
da jinsintarwa12 domin ya samu yin amfani da
salon hira, 13 ya tattauna da shi da yanyawa,
wato dai yanyawa ya yi magana da shi. Ba a nan ta ƙare ba. Haliru ya kira shi malami, shi kuma yanyawa ya
yarda da wannan matsayi, wato mu’allimu. Haliru ya je
wurin yanyawa ne domin wataƙila ya ƙaru da dubarunsa. To amma sai ya tarar ba haka abin yake
ba. Kalaman yanyawa suna da ɓurɓushin raha ta fuskar ban-dariya. A
wannan wurin ne, inda yanyawa ya karɓa sunan liman da malam, kuma har ya
tabbatar da yana da ilmin tauhidi, ban dariyar take ga duk wanda ya san
yanyawa. Haka kuma sai ban dariyar ta ƙaru lokacin da Haliru ya
kawo masa karantarwar Hadisi dangane da taimaka wa masu rauni. A madadin ya
amsa sunansa na malami kuma limami, ya tausaya wa Haliru, sai kurum ya mayar da
jawabi da cewa / kai ka fi ni / ! Daga nan sai ya shiga maganganun da suka yi
wa Haliru nuni da cewa yana iya mayar da shi Halirun namansa, ya yi watsi da
malantarsa. Cewar da Haliru ya yi sai ya sa ƙaimi, ita ma magana ce
mai ɓurɓushin ba da dariya ga mai saurare.
Haka nan kuma labarin da Haliru ya ba
mu cewa ya ga dila da biri da kura a wuri guda, sannan kuma ga zaki kusa,
labari ne mai ɓurɓushin ban-dariya. Kiran dabbobin nan
uku a matsayin gawa uku alhali da ransu, shi ne yake ƙunshe da ban-dariyar. A nan take mai saurare zai yarda da
maganar Haliru, domin kuwa zakin da yake kusa ne zai mayar da su gawa. Saboda
haka ne Haliru ya yi gaba kada sanadin da zakara yake gudun shaho ya jawo masa,
ya far masa, zaki ya haɗa da shi, shi ma ya zama
gawa.
Duka duka dai, yadda Haliru ya kawo
abin da yake son ya faɗa, wato zaɓen kalmomi da na salo, shi ya cusa
sashen raha, wato ban-dariya, cikin waɗannan baitoci. Haliru yana da zaɓin kawo labarin dila da biri da kura,
alal misali, cikin murya mai ban tausayi ko mai ƙarfafa irin ƙarfin da zaki yake da shi.
Haka nan kuma yana iya nauyaya saƙonsa ta hanyar jan
hankalinmu zuwa ga yadda rayuwa, musamman ta namun daji take, wato rayuwar
fin ƙarfi. To amma mawaƙin bai zaɓi ko ɗayan waɗannan ba. Saboda me? Saboda yana son ya cusa raha cikin
baitocin.
Wata waƙa da Haliru ya rubuta ita
ce “Waƙar Fanda” (Honda) ko kuma “Danja” (danger da
Ingilishi). Ita wannan waƙa tana cikin wannan rukuni na waƙoƙi ‘yan sakayau, domin kamar zambo ne
(wani abu mai haifar da ban dariya) Haliru ya yi wa babur. Lalle Haliru ya sha
kayen babur kuma har jinya sai da ya yi. To amma, kamar yadda halinsa yake, ya
yi ƙoƙarin ya ba mutane labarin
wannan haɗari cikin raha domin
wannan lamari ya riga ya zo har kuma ya wuce, sai labari. Tun da kuwa labari ne
zai bayar ai gara labarin ya nishaɗantar.
To a baiti na kusa da na ƙarshe ne raha ta fi bayyana a wannan waƙa. Abin da mawaƙin ya yi shi ne kawo mana
bayani a kan yadda matansa suka kansance lokacin da yake jinya a sanadiyyar
wannan haɗari da ya yi. Ga abin da
ya ce:
A’i ka cewa Mallam na falke
Tumba ka cewa Mallam bai falke
Ga Ige na can ɗaka kai na soke
Babu zama Joɗa da hannu rabke
Balki kiran Nana da wa ba ƙwabri
(Waƙar Fanda)
Idan aka yi la’akari da yanayin zaman
matan Hausawa, wannan baiti a jere ya kawo sunayen matan Haliru. Wato uwargida
da kishiyarta sannan mata ta uku wadda daga hannunta ne amarya (mata ta huɗu) ta karɓi muƙamin amarci. Saboda haka
A’i ce uwargida sannan Tumba sannan Ige, sannan Joɗa wadda ita ce ba ta daɗe da zuwa ba. Wato amarya ce.
Yadda Haliru ya bayyana irin
halin da kowace mata ta samu kanta lokacin da yake jinya abu ne mai muhimmanci
ta fuskar ƙoƙarin cusa raha cikin
wannan baiti. Halayen a mataki-mataki suke kuma daga mafi ƙarancin damuwa zuwa mafi tsanani. A’i wadda ita ce uwargida
kuma wadda ta riga ta saba da Haliru, ta san rashin lafiyarsa mai tsanani ko
marar tsanani. Wato tana iya gane idan rashin lafiyarsa ta tsananta. Saboda
haka ita hankalinta bai tashi ba. Don haka take faɗin ai Haliru a falke yake. Tana nuni
da cewa bai yi nisa ba. Ita kuwa Tumba ta san Haliru amma ba kamar yadda A’i ta
san shi ba. Saboda haka ba mamaki idan ta kasa gane cewa hutawa ce kurum yake
yi, ba suma ya yi ba! Ita dai a ganinta ba a falke yake ba (a sakaye, ya suma)!
Ige kuwa saninta bai ko kai irin na Tumba ba, balle na A’i. Tsoro ya kama ta.
Za ta rasa miji. Joɗa fa wadda ita ce amarya? Ita kam ta
gigice, sai zullumin abin da zai biyo baya. Ba wai rasa miji kurum ba, a’a, ai
ga al’adar ƙasar Hausa akan camfa matar da mijinta
ya rasu ɗan lokaci kaɗan bayan tarewarta a gidansa. Akan ce
duk wanda ta aura zai rasu ba da daɗewa ba. Wannan tunanin ne ya ɗimauta Joɗa. A raƙaice, a cikin wannan baiti
Haliru yana zolayar matansa ne. Jin haka kuwa kan sa mai sauraren sa aƙalla ya yi murmushi. Su kuwa su Balki da Nana ƙannen Haliru ne. Balki ce ta ruɗe saboda ganin yayansu cikin wannan
hali, don haka ne kuma ta ƙwala wa ‘yar uwarta, Nana, kira domin
ta zo ko za su samu ganawar ƙarshe da shi.
“Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau” waƙa ce daga ɗaiɗaikun waƙoƙin da Haliru ya ba suna da kansa. Wannan waƙa ta ƙunshi wasa da maganganun hikima na
Hausa, musamman karin magana. Manufar waƙar ita ce ishara, Wannan
kuwa shi ya sa waƙar ta zama ta nasiha. Duk kuwa da
kasancewarta haka saƙonninta ‘yan sakayau ne ba nauyaya ba.
Hasali Haliru ya faɗa cewa waƙarsa wasa ƙwaƙwalwa ce:
Da mallammai da su yara
Kurallu ku daina kisnawa
(Ko Ba Ka Raƙumi…)
A cikin wannan waƙa Haliru ya yi amfani da kare-karen magana masu ban-dariya.
Ya yi haka ne ta ɗabi’ar nan da aka san mawaƙa da ita ta jan harshen ɗan Adam har iyakar gaɓa, dab da wurin da nan take bami zai
auka. Haka ne Haliru ya yi a waɗannan baitoci na tafe. Da shi bami ne ko jahili da kuwa
batsa ta cika su. To amma gwani ne kuma mai ilmi. Raha ce kurum manufarsa kuma
ya san iyakar gonarsa. Don haka ba zai wuce ta da iri ba:
Mutum komi rashin kumya
Garai ba za shi damƙowa
Tulin nonon uwar mata
Bajinta ba za shi shahowa
Bale walle gaban suruki
Da gangan ba shi farawa
(Ko Ba Ka Raƙumi…)
A baya kaɗan misali ya zo daga waƙar da Haliru ya rubuta a kan haɗarin da ya yi da babur. To ko bayan
babur mota ma ta ɗan girgiza shi. Haliru ya
yi haɗari da ita, kuma tasa ce
ba ta ƙanensa ba. Wannan mota ta lalace a
sakamakon wannan haɗari, shi kuwa ya samu fita
/ amma fa ba da alheri ba/, ta bakin Nomau Na Magarya, in ji Kassu Zurmi. Nan
take ya zama marar mota. Tun a baiti na farko ya faɗa mana:
Yi zafi tafi kai iske ƙanen naka da kanka
Faɗa mai bari shakkar ka faɗa mai maganakka
Ta motakka da taf faɗi da kyar kaf fita kanka
Faɗa mai haɗari wanda ya faɗa bisa kanka
Ji ta ɓaci ƙwarai yanzu zama ba ta ɗagawa
(Babban Bajini Bello Ƙanena)
Wannan shi ne farkon waƙar da Haliru ya rubuta domin ya shaida wa ƙanensa irin haɗari da hasarar da suka same shi. Haka
nan kuma yana son ya samu taimako daga ƙanen, watakila ma ya samu
wata mota don ga abin da ya ce ma ƙanen:
….
Sanin ka isa yas sa ni barin Gwaggo da
Inna
In shawo firi in
ga ka gamo na da cikawa
(Babban Bajini Bello Ƙanena)
To, a cikin wannan waƙa akwai wuraren da Haliru ya yi tsattsafin raha. Misali a
baiti na 14 ya nuna cewa asalinsa ne kurum zai tuna ya kasa kiɗa taushi ga wannan ƙane nasa. Zancen wai Bello ƙanensa ne bai ma taso ba, mun kuwa san cewa a al’adar
Bahaushe wa bai roƙon ƙane. To amma shi Haliru ya
yi watsi da wannan al’ada. Shi kam gudun a ce ga Batoranke nan, kuma jinin
Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, yana kiɗa, shi ne kurum dalilin da ya hana
shi ɗaukar kalangu ya kiɗa wa ƙanensa. Ga dai baitin wanda ta amfani da kirari da waskiya
Haliru ya cusa ban-dariya cikinsa:
Babban bajini Bello ƙane ka zama wana
Haskenmu ɗiyan Baba ina son ka ga raina
Na Abbas bahagon Manuga walla maɗi na
Ba don asuli wanga da yah hau bisa
kaina
Tabshi nika yo ma na kiɗi za ni kiɗawa
(Babban Bajini Bello Ƙanena)
Dubi yadda Haliru ya zaɓo kalmomi kamar /ɗiyan Baba/ da /ina son ka ga raina/
da /walla/ da /ba don asuli wanga/ da kuma /yah hau bisa kaina/, ya ƙirƙiro irin yadda Bahaushe na gidi (wato
wanda Hausarsa ba ta gurɓata ba ko don zaman birni
ko kuwa saboda tasirin ilmi) yakan bayyana ƙauna ga masoyinsa. Wannan
zaɓi yana daga abubuwan da
suka haɗu suka cusa raha cikin
wannan baiti.
Wani misali daga waƙar shi ne baiti na ƙarshe:
Halir Alhaji Alƙali da yay yo shi na dauri
Shari’a jiya yay yo ta ga yau ya fita
uri
Gidana nake can Wurno ina rangaɗa gari
Ga yau na fita na bar jama’an nan na
Ilori
Nufina mu aje wagga da sauran furtawa
(Babban Bajini Bello Ƙanena)
Haliru ya ce ya / fita uri /. Abin da
yake nufi shi ne ya hutar da kansa daga shiga cikin wahala da shirme yana ji
yana gani, alhali ba wanda ya tilasta shi ya shige su tun da fari. A taƙaice dai ya ‘yantar da kansa. Wato aikin shari’a na alƙalanci irin na zamani wanda ya yi, aikin wahala ne da kuma
wani ‘babban shirme’- a addinance. Aiki ne mai wuya, marar yanci, a wurin
Haliru, ko da kuwa mai daɗi ne ga wasu. Daɗi da ‘yanci a wurin Haliru kam suna
nan cikin gidansa a garin Wurno inda yake /rangaɗa(-r)/ garinsa. Da farko dai kalmar
“rangaɗa” kalma ce da aka fi jin
ta a bakin mata. Watakila maza za su fi amfani da kalmomi kamar “kwankwaɗa” da “shari” da “zuƙa” da “zuba” To, wannan amfani da kalmar da mata ne suka fi
furta ta da kuma kwatancen bambanci da ya yi tsakanin alƙalanci da zama a gidansa, kai har ma da sukar da ya yi wa
wasu mutane (watakila alƙalai), duk sun haɗu sun mayar da baitin mai ba da
dariya.
Daga cikin waƙoƙin Haliru na soyayya akwai waɗanda suke ‘yan sakayau ne saboda
jigogin ƙauna da kyawo ne suka mamaye su. Waƙar 'Soyayya Ruwan Zuma’14 da “Waƙar Habbi” suna daga cikin
waɗannan waƙoƙi. Ya rubuta ‘Waƙar Habbi’ cikin samartakarsa, yana matashi ɗan kimanin shekara ashirin da bakwai.
Samartaka ta yi tasiri a kan wannan waƙa. To amma ko bayan ita akwai wasu salailai waɗanda suke da tasiri a kan shigar da
raha ta yi cikin wannan waƙa. Na farko shi ne salon kamancen
kasawa wanda shi kuma sai ya haifar da salon kambamawa. Bayyana matarsa a
matsayin wadda babu wata mace da ta kai ta kyawo ko hali, ko dai duk wani abu
mai daraja da za a danganta ga mata, magana ce mai ɓurɓushin ƙarin gishiri, wato kambamawa. A al’adar Bahaushe a ji irin
wannan magana daga bakin namiji game da matarsa, dalili ne sat da ya isa a ce
mutum mai saiɓi ne. Shi kuwa saiɓi a cikin al’adun Bahaushe yakan ba
mai sauraren wanda yake yin sa dariya. ‘Waƙar Habbi’ tana cikin irin
wannan tsari na saiɓi. Dubi wannan baiti mai
cike da ban-dariya:
Ita af fara ko Azbinawa sun saki
In sun ga Habbi suna faɗin ba mu kai ba
(Waƙar Habbi)
A nan wai Azbinawa ne da kansu, waɗanda farar fata ce da su, kuma su ne
Hausawa suka fi gani a matsayin fararen mutane, su ne da kansu suka sallama nan
take da ganin matar Haliru, suka ce /ba mu kai ba/! Haliru bai yi amfani da
lamiri ga’ibi na “su” a ƙarshen baitin ba, kamar yadda ya faro shi.
A madadin haka sai ya yi amfani da lamirin “mu”. Wannan shi ya taimaka ga cusa
raha cikin wannan baiti domin kuwa mai sauraren zai ji ainihin maganar da
Azbinawa suka faɗa, ba wai cewa aka yi sun
ce ba.
Wasu baitoci makamantan wannan, kuma
tattare da saiɓi su ne:
Ni na yi begen Habbi ya kai Ummaru
Begenta cilas na garan ban so ba.
In ta shigo shigifa shi zan kuma ga
duhu
Huskatta ah hitila duhu bai zam ba.
In Larabawa sun gane ta kira sukai
Ya aljamalu ɗiyanmu dub ba su kai ba.
…
Gashin idanun Habbi ba shi da lanƙwasa
Duba giratta ka so ta ko ba ka so ba
…
Tabshin jiki tabshin hali kyawon wuya
Kyawon ɗuwawu macce dut ba ta kai ba
…
Kwad damƙi damtsen Habbi ba shi baƙin ciki
Maganarta ta fi zuma ruwa ba su kai ba
Tsaye zamne Habbi irinta kam ba a gan
ta ba
Na dubi mata ba kamar mahbuba
…
Mata ku hanƙura Habbi ta wuce macce dut
Halirunku Alhaji Wurno na ba wai ba.
(Waƙar Habbi)
Waƙoƙi
Nauyaya
Waɗannan su ne waƙoƙin da suke ɗauke da jigogi ko saƙonni masu nutsar da hankali cikin tunani, masu kawo
natsuwa, idan na addini ne su kawo tawali’u da taushin zuciya. Nauyin da ake
nufi a nan bai nuni da muhimmancin waƙa ga mai saurare ko mai
ita ba. Manufa ita ce a maimakon waƙar ta cusa masa raha sai
ta saka shi cikin halin tunani da tsokaci da nazari da natsuwa da makamantan
haka.
Waƙoƙin Haliru waɗanda suke cikin wannan rukuni sun haɗa da na ilmantarwa da na wa’azi ko
nasiha, da na kishin ƙasa da wasu na soyayya, da na madahu
da na addu’a da na addini gaba ɗaya. Haka nan kuma akwai na faɗakarwa da na suka ko gyaran al’umma da
kuma wasu na mayar da martani da zambo,
Haliru ya rubuta wata waƙa mai suna “Waƙar Maƙiya Amada” wadda a cikinta ya yi wa waɗansu mutane zambo. Ga dukkan alamu
wannan waƙa tana magana ne a kan mutanen da
Haliru yake ganin ko kuma ya haƙiƙance cewa sun cuta masa.
Saboda haka ko bayan zambo tana kuma ɗauke da addu’a da mayar da martani. A
baiti na ɗaya da na biyu ne mawaƙin ya yi nuni da duk waɗannan:
Na yi nufi don haka zan tsarawa
In yi rubutu wada zan ganewa
In yi bayani wada zan shiryawa
Rabbu riƙa min wada ban kasawa
Ba ni mataki wada ban ƙallewa
Kai ka isa Jalla ina nan gun Ka
Na natsu kallo bisa dut aikinKa
Ban da dibara wata baicin bin Ka
Alamu dut ga mu cikin mulkinKa
Ba mu fita babu wurin ɓoyewa
(Waƙar Maƙiya
Amada)
Duk da cewa Haliru ya danganta waƙarsa da cewa ta maƙiyan Allah ne masu cuta
masa, sannan kuma duk da cewa ya haɗa da zambo cikin waƙar, waɗannan duk ba su hana salonsa na tsattsafin raha fitowa fili
ba. Addu’a da zambo da mayar da martani kamar wada Haliru ya gabatar da su
cikin waƙar, abubuwa ne nauyaya. Addu’a dai
tana bukatar natsuwa da ladabi. Zambo kuwa yakan taƙalo fusata a yayin da mayar da martani kan bukaci game
fuska da kuma fushi. To amma dubi waɗannan baitoci:
Babu mutum wanda ka yo ma sheɗa
Ba ni biyar mai riƙa hauyar huɗa
Mai mutuwa mai gajiya mai son ɗa
Mai taɓa nono ya laɓe mugun ɗa
Ba ka ganin ya biɗi Mai shiryawa
Tashi hawa sai ka ga ya sha maƙil
Wai ya waye ka ganai can fotal
Ya bar gashi da yawa ɗan buntsul
Ba shi ibada ƙwanƙil ɗan ƙwanƙil
Ba shi amini illa lecewa
Shi aj jaki ƙasa ya sha kabra
Shi a aura bana ya sha kora
Ya yi shige sun bugi ɗan jan gora
Ya sha murza ƙasa ya yo ƙura
Ba shi da ƙarfi wada zai tserewa
(Waƙar Maƙiya Amada)
A nan mawaƙin ya bayyana rashin dacewar biyar mutum a matsayin wanda
ake yi wa ibada saboda dalilai da dama. To a wajen zana waɗannan dalilai ne Haliru ya cusa raha.
Mutum dai mai riƙa hauya ne, wato manemin abinci.
Mutuwa dole ta zo masa. Ga shi kuma mai rauni na gajiya kuma mai son ‘ya’ya,
mai rauni a hannun mata. Zurfin ma’ana kalmar / laɓe / take da. Bai son a gane shi yana
wannan aiki amma kuma ma’abucin aikata shi ne. Wata ma’ana ita ce mai tsananin
rauni ne na ƙarfi da hankali bayan ya aikata ƙololuwar wannan aiki. Mutum dai abin renawa ne, kome nasa
na ƙasƙasci ne saboda raunin da
yake da shi. Muzi ke nan! Haliru ya muzanta ɗan Adam, abin dariya!
Daga wannan baiti na huɗu sai Haliru ya ɗora da zambo inda ya zayyana sifar
abokin adawarsa. Ya yi amfani da kalmomi bi-ma’ana, /maƙil/ /buntsul/ da /ƙwanƙil ɗan ƙwanƙil/, waɗanda ke ƙoƙarin kawo yadda mashayin giya yake
tafiya. Bayan haka sai kuma aka sake kawo maganar neman mata inda aka ce wannan
abokin adawa kwarto ne, wanda dubunsa ta cika ya sha wahala a hannun waɗanda suka kama shi.
Muzantawa da zayyana tafiyar abokin
adawa da kuma yi masa zambo kai tsaye duk sun taimaka wajen cusa raha cikin waɗannan baitoci.
Wani abin sha’awa cikin wannan waƙa shi ne cewa Haliru ko shi kansa bai bari ba wajen yin
zambo, amma fa mai taushi, mai armashi. Wato zambon da aka gauraya da kirari,
abin da nake son in kira zambo-kirari.15 Kawo
wannan a cikin baitinsa shi ya haifar da tsattsafin raha. Ga baitin:
52Ban da ruhi Alhaji yas shirya ta
Wanga da yaz zan Gado sarkin wauta
Dankali sha kushe mijin ‘Yar Auta
Wurno gida Alhaji yas shirya ta
Na karu na ɗuru wurin roƙawa
(Waƙar maƙiya
Amada)
Haliru ya kira kansa /Gado sarkin wauta/ da /dankali sha kushe/ da kuma mijin /yar auta, /, waɗanda dukansu suna ɗauke da kirari amma kuma mai ɓurɓushin zambo. Sai dai zambon ba mai cutarwa ba ne, nuƙurar da take cikinsa ba ta taka kara ta karya ba. Wautar da ya yaba kansa da ita a haƙiƙani ba wauta ba ce. Da ita yake yi wa maƙiyansa alka. Su suna ganin sa a matsayin wawa alhali tasu wautar ta fi tasa, idan har za a iya a kira ta haka nan. Haka kuma Haliru sha-kushe ne amma fa ya riga ya tsira kuma tilas a yi da shi ko da an kushe masa. Kushe bai yi masa kome.
Salon raha ya taka muhimmiyar rawa
cikin waƙar Haliru mai ɗauke da wa’azi da nasiha ga Musulmi,
ciki kuwa har da shi kansa, wato “Sabilul Haƙƙi Bi Ƙaulis Sidƙi”. Nauyin saƙon wannan waƙa da kuma kasancewarta mai
tsawo16 suna iya gundurar da mai saurare ko karatun ta. To amma
saboda amfani da wannan salo da mawaƙin ya yi sai gunduraswar
ta ragu, idan har ba ta kau gaba ɗaya ba. Wannan shi ne muhimmancin
salon a cikin waƙar. Wannan shi ne yanzu abin da wannan
maƙala za ta duba, wato, tabbatar da samuwar salon a cikin waƙar.
Haliru ya kawo hujjojinsa bayan
ya ba mai sauraren waƙarsa shawara cewa kar ya nemi sanin
addini daga malaman da suka kasance miyagu masu fallasa. Daga cikin waɗannan hujjoji akwai masu ɗauke da raha Misali, dubi waɗannan baitoci: G
Ƙurungu daɗai ga tabki in shina nan
Baƙin kifi da uri a nan faɗi na
Gida ko in akwai mussa ciki nai
Zaman kusu a nan shi kam ba’a na
Ruwa da wuta cikin kasko guda ɗai
Gudansu ka ɗaukaka ciki ɗan uwana
Masallacin kare kura ta zona
Ina liman kare yake in ya zona
(Sabilul Haƙƙi Bi Ƙallis Sidƙi)
Tunani a kan yadda kyanwa da bera za su zauna a wuri ɗaya kuma lami lafiya, shi zai ba mai sauraren waɗannan baitoci dariya, domin ya san cewa haka ba zai taɓa aukuwa ba. Mai saurare zai shiga mamaren kalmar da za ta bayyana rashin yiwuwar wannan zama. Haliru ne ya hutar da shi a ƙarshen baitin inda ya kawo masa kalmar / ba’a /, mai kaifin ma’ana.
Baiti mai ɗauke da raha cikinsa na biyu shi ne na
65, kuma kamar na 63 yake. To amma yadda aka cusa raha cikinsa ya bambanta da
na farkon. A yayin da aka yi amfani da kalma mai kaifin ma’ana a na farko, a
baiti na 65 tambaya mawaƙin ya kawo. Wannan tambayar kuwa ba ta
bukatar jawabi domin yana nan ƙumshe cikinta. Duk wanda
ya san taren kura da kare to kuwa ya san jawabin wannan tambaya. Ba su shan
inwa guda. Kare naman kura ne. Ashe kuwa ko da shi ne ya gina masallaci da kuɗinsa kuma wasu suka zaɓe shi a matsayin limami, daɗewar wannan limanci nasa shi ne idan
kura ba ta zo ba! Idan ta zo ba limanci ba, ko ma ya yi sallar a matsayin mamu
ya san gatana ce don ba zai tsaya ba!
Waɗannan su ne hujjoji biyu da Haliru ya
bayar. Fashin baƙin wannan shi ne samun koyarwar kirki
daga miyagun malamai “faɗi” ne, “ba’a” ce, kuma
babu tabbas ga ko akwai amfanin da za a iya a samu, sai dai aibi. Idan mai
neman sani ya nemi ya san addini daga waɗannan malamai, to ya kwan da sanin
cewa wanda ma ya riga ya samu zai salwanta, tabbas kamar yadda ta auku ga kare.
A cikin wannan waƙa Haliru ya yi magana mai yawa a kan aikin Alƙalin zamani. Ya soki shari’ar zamani. Haka kuma ya soki Alƙalan zamani. Cikinsu kuwa har da shi kansa. Hasili da kansa
ya fara. Ya yi nadama, ya kuma yi tuba ga Mahaliccinsa Allah Mai gafara. Ya haƙƙaƙe cewa aje aikin Alƙalanci da ya yi babban arziki ne gare shi. A ganinsa Alƙalancin da ya yi babban kuskure ne kuma babbar ɓarna:
Wa man lam fasiƙi kake ka yi kufri
Dukan azzalumi Wuta za shi kwana
Zama shi wanda yaƙ ƙi ya yo hukumci
Na Allah kafiri na zalumi na
…
Ina hujjarka Alƙali Halir nau
Wane nassi gare ka na tabka ɓanna
Ƙisasi ba ka yi uznun bi uznin
Yadan bi yadin ka ce min ja’izun na
(Sabilul Haƙƙi…)
Cikin irin wannan magana mai nauyi ce
Haliru ya yayyafa baitocin raha a wannan waƙa. Misali:
Da ɗarɗurinka ga ka da saulajani
Da zunnarinka zainul
kafirina
Bale ƙiyyaru mai
shafa ta hoda
Da barniɗa ji fullar kafirina
A sa gashi kamar namijin agwagwa
Ana bahasi da halshen zalimina
(Sabilul Haƙƙi…)
A nan Haliru ya kamanta shigar Cif
Joji da siffar namijin agwagwa. Ban san wani kamancen daidaito mai ban-dariya
da muzantawa wanda ya fi wannan ba!
Misali na ƙarshe da zan kawo daga wannan waƙa shi ne na da-na-sanin da Haliru ya yi lokacin da ya tuna
da daular da ya yi a can da. A cikin baitocin da wannan misali yake mawaƙin ya kawo maganar ƙwazonsa na neman ya samu
girma, da kuma shawarsa ta ya tara matan aure. Ya samu duka biyun. Yadda ya
kawo wannan bayani tattare yake da haliyyar raha:
Biɗar girma biɗar in amri mata
Sabadda kwaɗan su niɗ ɗaukam ma kaina
Ji na tara su sun watse gaba ɗai
Ga yau sun bar ni fanko mulmulena
Ina nan duniya haka yak kasance
Bale can gobe ni nic cuci kaina
Aje su da na yi na yayo haramun
Suna lashe ta ni ko kuskure na
Ina ƙamnar su sun gudu sunka bar ni
Sakin wasu niy yi nif futad da raina
Bale su yi zamne tsufa ga shi ya zo
Inai musu mi ina ƙarfin jikina
Cikar ran kassuwa ta sunka yo min
Marece sunka watse min gidana
Sarautar ba ta ba samu na dauri
Bukata babu mi suka yi wurina
(Sabilul Haƙƙi…)
Dubi irin girma da samu da ni’ima waɗanda waɗannan baitoci suka ambata. Haka nan
kuma dubi yadda baitocin suka bayyana salwantar da duk waɗannan ni’imomi suka yi. Sarauta ta
tafi, ƙarfi ya tafi, tsufa ya kama, sannan
matan nan duka sun tafi sun bar Haliru! Akwai tausayi ga jin wannan idan a zube
aka rattabo shi. To amma a cikin waƙa mai tsattsafin raha aka
yi rattaben. Ya yi amfani da salon kinaya ya kira kansa /fanko/ da /mulmule/,
wato falalin dutsi. Kalmomin nan biyu na kinaya kalmomi ne masu kaifi da zurfin
ma’ana gaba ɗaya. Kuma su ne suka sa
baitin da suka fito cikinsa zama mai haliyyar raha. Haka nan kuma kalmar /
lashe / tana da kaifin da ke bayyana kwaɗayin da matan Haliru suke da ga cin
/’haramun/ ɗin da yake samo musu. Shi
yana kan tafka kuskure, su kuwa suna murna da samun sakamakon kuskuren. Kalmar
ce ta / lashe / ta barbaɗa ban-dariya cikin baitin.
Su kuwa baitoci na 215 da 217 ɗauke suke da salon tambaya domin su
kasance masu cusa raha cikin ran mai saurare. A baiti na 215 tambaya biyu ne
Haliru ya yi waɗanda ba su jiran jawabi
domin yana nan tare da su, kuma shi ne “babu”. Shi kuwa baiti na 217 tambaya
guda ce kuma makamanciyar na baitin da ya gabata. Dukansu dai masu ba mai
saurare dariya ne.
Akan samu tsattsafin raha cikin waƙoƙin madahu kamar wada muka gani a cikin
wƙoƙin wa’azi da nasiha. Waƙoƙin madahu dai su ne waɗanda aka yi a kan yabon Annabin
Rahama, Muhammadu (S.A.W.). Saboda haka waƙoƙi ne masu bayyana tawali’u da nuna tsananin ƙauna zuwa gare shi tare da girmamawa mafificiya. A taƙaice waƙoƙi ne masu nauyi.
To amma duk da nauyin da waɗannan waƙoƙi suke da Haliru mai iya yin tsattsafin raha ne a cikinsu.
Ya kuma san wuraren yin haka. Dubi waɗannan baitoci daga waƙarsa, “Jirgi”.
Yai hijira barin Makka dangi sun matsa
mai
Za shi Madina Allahu yac ce mai hakan
ga
Ya tafi Garba Siddiƙu sun tafi tare kogo
Su biyu sunka kwan ukku ko huɗu nan wurin ga
Kafirran da am Makka sunka bi swansu
kogo
Ba su ganin su Allahu yaɓ ɓoye waɗanga
Sun tafi tare bokansu yac ce nan wurin
ga
Ku duba nan ga kogon ga Ahmadu na
wurin ga
Sai ɗai sunka duba ga kogo saƙe-saƙe
Ga yana da ƙwan kurciya ga kurciyag ga
Dut taron da an nan gaba ɗai sun yi zonai
Kafirran ga sun gane ƙaryar mai faɗin ga
Sai ɗai sunka ce mai Saɗifu irin hakan ga
Ƙarya ba mu ɗaukat ta ka mutu nan wurin ga
Kun san alkawal ba shi tashi sun kashe
shi
Kun ga Saɗifu shi am musanyar Annabin ga
(Jirgi)
Haliru ya ba mu labarin Hijira cikin
waɗannan baitoci. Wato
lokacin da Annabi Muhammadu (S.A.W.) ya bar Makka zuwa Madina yana mai bin
umurnin Mahaliccinsa. To bayan ya fita da shi da Sayyidina Abubakar sai kafiran
Makka suka bi su da niyyar su kashe shi. To amma fa da bokansu suka bi Annabi (S.A.W.)
Da ma kuwa bokan ya tabbatar musu cewa zai nuna musu inda Annabi (S.A.W.)
ya ɓoye. Da ya nuna musu kogon
da Annabi (S.A.W.) yake sai suka duba ba su ga kome ba in ban da yanar
gizo-gizo da kurciya kusa da ƙwanta. Wannan mu’ujiza ce.
Amma su ba su san da haka ba. Saboda haka sai suka fusata. Bokansu ya wahalar
da su a banza ke nan. Nan take suka kashe shi.
A baiti na 115 ne muka ji
maganar da kafiran Makka suka yi wa Saɗifu, bokansu. A nan ne kuma Haliru ya
cusa raha dangane da labarin da ya ba mu. To yadda maganarsu ta zo da kuma
yadda maganar Saɗifu ta zo a baiti na 112,
shi ya haifar da rahar. Shi dai Saɗifu da ƙarfafawa ya faɗi tasa magana, ba tare da wata shakka
ba. Su ma da ƙarfafawa suka yi tasu kuma suka zartar
da ita. Saboda haka ta amfani da salon hira Haliru ya ƙirkiro tsattsafin raha cikin waƙarsa.
Haka nan kuma tsakanin baiti na 122 da
na 132 Haliru ya kawo bayani a kan Ɗan Mugira dangane da ƙiyayyar da ya nuna wa Annabi (S.A.W.). Ya kuma yi bayanin
irin sunayen da Allah Maɗaukaki ya ba Ɗan Mugira, da yadda shi (Ɗan Mugira) ya yarda da
dukansu in ban da guda. To yadda Haliru ya kawo waɗannan sunaye na zargi da yadda Ɗan Mugira ya yarda da su da ɗai ɗai, sai ga na ƙarshe ya yi musu; da kuma yadda Haliru ya kira shi, sun
taimaka ainun wajen gina tsattsafin raha. Haliru ya ce:
Allah yaf faɗa mai saboda takabburatai
Hammazin namimin ji ba shi musun hakan ga
Massha’in wurin hairi manna’in matcaci
Allah yaf faɗa mai asimin duniyag
ga
An ce Ɗan Mugira utillin mu’utadin na
Dut ya amsa sunansa ba shi musun batun
ga
Sannan anka ce mai zanimin ɗan shige na
Shi ɗai yam musanya ma shegen duniyag ga
An ce tsohuwatai ga layi tai cikinai
Tal liƙa ma tsohon da yag gada
gidan ga
(Jirgi)
Kalmar / matcaci / a baiti na 128, da / ɗan shige na / da / shegen duniyag ga / a na 130, musamman sun fi ƙunsar raha saboda takaicin da Haliru yake ji wanda kuma ya nuna cikin wannan zagi da ya nanata wa Ɗan Mugira, kamar wada Allah ya kira shi. Sannan kuma labarin da Haliru ya kawo a baiti na 131 ya ƙara kafa rahar.
Idan kuma aka dubi waƙoƙin da Haliru ya rubuta na yabon
mutane, a nan ma akwai tsattsafin raha. A waƙar da ya yi ta yabon
Sarkin Musulmi Abubakar III akwai waɗannan baitoci:
Ɗan Musulmi in dai Musulmi na
Ya sani ɗan Sarkin Musulmi na
Wa ka zagin tsofonsa zan shi na
Ban batun wancan shi kurege na
Fatiha ma bai i da ƙarshenta
…
Wanga Sarkin ɗa na karimi na
Ko da dai sun ɓoye sharifi na
Tabbata Bubakar ɗan waliyyi na
Hattara kila ma shi waliyyin na
Don akwai hanyoyin alamunta.
…
Wa ka ja mai wane na ka gasa tai
Wa kai i mai wane na ka tausa tai
Ba kamatai ko an yi tono nai
Ba irinai ra’ayi da hangenai
Ko’ina na maganag ga in yo ta
Son zumuta da hani da alheri
Ga zalaƙa kuma ga shi ba kibri
Ga sakin fuska ga shi mai sabri
Ga amana koyaushe ba sharri
Ƙeta ko can bai gane sunanta
(Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)
Karanta ko sauraren waɗannan baitoci kan iya sa mutum ya ji kamar babambaɗe ne ya sa Sarkin Musulmi gaba yana furta su. Wato kamar kirari kumburau17 ne ake yi ma Sarkin Musulmi, shi kuwa kirari sai in akwai raha ake iya yin sa. Haka nan kuma wanda aka yi wa shi, an yi ne domin ya shiga wani nau’i na raha kafin ya kai ga kumburewar. Haliru ya yi nasarar kawo wannan tunani ga zukatan masu sauraren waƙarsa, tare da cusa raha cikinta ta hanyar zaɓen gaɓoɓi masu bukatar a fara furta su da sauti mai ƙarfi. Waɗannan gaɓoɓi kuwa sun zo ne a farkon kowane ɗango in ban da ɗango na ɗaya na baitin ƙarshe. Gaɓoɓin su ne ɗan da ya da wa da ba da fa da ta da wa da ga da ko da kuma ƙe. A wasu wurare ma kalmomin da suka ƙunshi waɗannan gaɓoɓi su ma da ƙarfi ne ake furta su. Misali, kalmomin tabbata da hattara.
Bayan wannan siga ta kirari akwai kuma
shammata ko zambo da kuma salon kambanawa. A baiti na farko an yi amfani da
salon kinaya ga wani mutum wanda yake zagin Sarkin Musulmi, aka kira shi
“kurege”. Sannan kuma aka ce ba ya iya karanta Fatiha duk kuwa da cewa shi
Musulmi ne. To a waɗannan ɗangogi biyu ne shammatar take. A nan
kuma ban-dariya take saboda da ma akan yi shammata ne domin a yi dariya.
A baiti na ƙarshe Haliru ya yi amfani da salon kambamawa a ɗangon ƙarshe inda ya ce Sarkin Musulmi bai san kalmar ƙeta ba sam sam, balle daɗa ya san ƙetar ko ya aikata ta! Wannan salo na kambamawa da Haliru ya
yi amfani da shi shi ya girka kirarin da muka ambata a kan ƙololuwar matakin kumburarwa. Shi kuma zai haifar da
ban-dariya cikin baitin.
Haliru Wurno ya rubuta waƙoƙin soyayya a kan matansa. Wasu daga
cikin waƙoƙin ‘yan sakayau ne, kamar
waƙar “Soyayya Ruwan Zuma”, a yayin da wasu suka kasance
nauyaya. ‘Waƙar Hassi’ wadda a haƙiƙanin gaskiya waƙa ce a kan soyayya da zaman aure a kan matan da ya aura,
musamman wata da ake kira Hassi. To ita wannan waƙa tana daga cikin waƙoƙinsa na soyayya nauyaya. A cikinta
Haliru ya kawo sunayen matan da ya taɓa yi da kuma halayensu waɗanda suka zama dalilan rabuwa da su.
Wasu daga waɗannan dalilai masu ban
tausayi ne, kamar yi masa sammu ko kwarce, wasu kuwa na tashin hankali da ɓacin rai kamar faɗa da shi ko ‘yan uwansa. Haka nan kuma
akwai dalilan da suka shafi addini, kamar rashin yin salla da ƙazanta.
To, ɗaya daga cikin matansa ita ce Hassi,
ga kuma abin da ya ce a kan ta:
Nata kwarce ya hau ni na ji shi
Na yi kuka rabuwarmu an ji shi
Na bi ko sawun Hassi domin shi
Ba ta nan kam halinta ta bar shi
Ba ni ƙamna tai ba ni begen ta.
Ta yi tashi na bi ta har daji
Na yi kwana da sununta har jibji
Na ɓakalkalce sai ka ce tuji
In dare na in rana har daji
Na yi kukan ‘yar Amma kwarcenta
…
Sai da nig gane na fice jama’a
Dariya ta aka yi ina far’a
Sai a ce ai Hassi akwai ɗa’a
Na yi roƙon Allah ya ban sa’a
In sakat ko raina ya ɗan futa
(Waƙar Hassi)
Baiti na 35 ya fito fili ya faɗi sakamakon abin da Haliru ya ce ya kasance a baiti na 30. A baiti na 30 ya ba mu labarin yadda ciyon so ya kama shi wanda a ganinsa ciyon kwarce ne. Ya bi Hassi ko’ina. Yar bar gidansa ya nufi dawa wai a zatonsa Hassi tana can. Haka nan kuma a wajen dakon ya gane ta ya ɓata darensa a wurin da bai dace ba, a juji. Watakila saboda babu wani wuri da zai raɓe in ban da juji! Hassi dai tashi ne ta yi amma maimakon Haliru ya yi abin da al’ada ta shimfiɗa, shi da kansa ya tafi biko ta! Wannan hali ne irin na son maso-wani. Yadda kuwa Haliru ya ba mu labari shi ne zai ba mu dariya, musamman kwanan da ya yi a juji. Haka nan kuma yadda ya kammala baiti na 35 da fatar cewa ransa zai samu hutu idan Allah ya ba shi sa’ar sakin Hassi, abu ne mai ban dariya. Haliru ya kasance mai tsananin son Hassi. Saboda son da yake yi ma ta har a juji ya kwana. To amma ga shi ya gane ashe kwarce ne ta yi masa. Wuya!! Saboda haka sai ya roƙi Allah sauƙi domin ransa ya samu ya huta! Ya dai gaji, ya gane!!
A waƙarsa ta tarbiya wadda tana
cikin waƙoƙinsa na gyaran al’umma ko
suka ga munanan halaye, Haliru ya surka da tsattsafin raha domin ya isar da
wannan saƙo. A cikin waƙar ya yi bayani cewa ummul haba’isin taɓarɓarewar tarbiyya a ƙasar Hausa su ne shugabanni. Shugabanni kuwa a ganinsa sun
haɗa da masu mulki da malamai
da kuma masu hali. Su ne suka aza yara ga hanyoyin rashin tarbiyya. Su ne
mayaudara waɗanda aka danƙa wa amanar dukiyar jama’a amma suka ci ta. Malamai ne suka
yi watsi da tsoron Allah da ƙana’a, suka rungumi
fadanci ga masu mulki da kuma kwaɗayin abin duniya. Haliru ya bayyana
halayen waɗannan malamai a matsayin
tushen rashin tarbiyya inda yake faɗin.
Mis sa haka wai ba a lura ba
Amsar rashawa ba a bar shi ba
Yau mallammai su ag gaba
Su ci hanci had da bugun gaba
Imani ya fita zucciya
…
Shafin kwalli ko karuwa
Ga biɗar mata ‘yan ga-ruwa
Da gida daji ko anguwa
An san haka balle karuwa
Wannan ita ak kan angaya.
Wa’azin mallammai don mitin
Dammu Salmu matan kicin
Malam Alaramma da tai wurin
Ɗakinai Zainabu ga ta can
Shi kirat ta fito ta yi mazaya
13.Sannan Larabci za su yi
Bi ta’ala huna shayi ki yi
Ita ko ta yi mai wani masgayi
Bil aini walau shi ma shi yi
Manyan mallamman duniya
(Waƙar Yin Tarbiyya)
Yadda Haliru ya siffanta malami mai
shafa kwalli domin matan banza su yi sha’awar sa, da yadda su kuwa matan (kamar
Zainabu) suke jan hankalinsa ta hanyar motsi da jikinsu, da kuma yadda ya
siffanta shi tare da kawo yadda yake juye baki zuwa harshen Larabci domin kada
na kusa su gane, duk waɗannan dabaru ne na cusa
raha cikin waɗannan baitoci. Lalle kam
sukar da Haliru ya yi a waɗannan baitoci mai kaifi ce. To amma duk da wannan kaifi,
baitocin sukan ba mai saurare dariya, musamman Larabcin da Haliru ya ce malamin
ya yi.
Irin wannan amfani da baƙon harshe ne Haliru ya yi a wata waƙa inda yake yin kira ga Hausawa su kula da al’adunsu. Ya riƙa kawo kalmomin Ingilishi cikin baitocinsa domin a fahimci
manufarsa. To amma fa kawo waɗannan kalmomi yakan ba mai saurare dariya domin ƙoƙarin muzanta masu dangantaka da su da
baitocin suka fito suke yi. A cikinsu Haliru ya nuna wasu al’adu da yara matasa
suka ɗauko daga wasu ƙasashe. Ya ce hatta su ƙasashen na waje daga baya
ne suka tsiri waɗannan munanan al’adu. Haka
nan kuma Haliru yana ganin cewa iyaye da malamai ne suka kai yara ga irin waɗannan munanan al’adu. Ga dai kaɗan daga waƙar:
20Suna cewa da an waye duhun kai
Zama wai yanzu gayu ne abutta
Akwai kuma har da Human Rait wajen
su
Ga kowa na da ‘yancin kanshi ƙatta
A nan aka samu tsohon bai da iko
A kan ɗa sai da yardar ɗan ji wauta
…
Iyayen yara su suka ɓata yara
Ga tarbiyyad da su haka nif fahimta
…
Ɗabi’ar ƙetare da ɗiyan ka yin ta
Uwaye su ka sa su suna ta yin ta
Su sai mu su ‘yan tufafi ‘yan
matsattsi
A tanke tsara da bel tamkar
biri ta
A sai feskap baƙar hulla a sanya
A bar zancen ta saƙa wa ka son ta
A ba su baƙin madibi shi ka daidai
Da no raspet a ba su
su sa fitarta
…
A yo gaye a sanya baƙi ga gashi
A yo askin ga fonk askin
mugunta
Ana yawo da kai sake babu hulla
Ana wani tsalle wai na gudun ƙazanta
Bale mata idan sun shace gashi
Ji ɗan kwalin ga hannu ake riƙe ta
…
Wajen ilimi a can ne yay yi tushe
Kujerin ‘yan maza a haɗe da mata
A ce wai diskashin aka
yi tsakani
Ga al’adarmu sam haka ba irinta
(Muhimmancin Al’adunmu…)
Kammalawa
A ƙoƙarin da wannan maƙala ta yi na ta nuna cewa salon tsattsafin raha shi ne salon marubuci na gaba ɗaya a cikin waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno, maƙalar ta kawo misalai daga waƙoƙi da dama kuma mabambanta ta fuskar jigoginsu. Waɗannan waƙoƙi sun kasu gida biyu: waƙoƙi ‘yan sakayau da waƙoƙi nauyaya. An karkasa su ta wannan fuska domin a nuna cewa ko a waƙoƙin da ake sa ran babu kafar shigar da raha, Haliru yana iya ya kawo ta ba tare da ya raunana waƙarsa ba.
Haka nan kuma an kawo tarihin Haliru
domin ya kasance wata manuniya ga dalilin da ya sa ake samun tsattsafin raha a
cikin waƙoƙinsa. A ganina halin
Haliru na rashin yarda da matsala ta tauye shi, kome tsananinta kuwa, shi ne ya
yi tasiri a kan rayuwarsa gaba ɗaya, ciki kuwa har da kasancewarsa
mutum mai raha da fara’a a ma’amalarsa da kuma rubuce-rubucensa na waƙoƙi.
Salon tsattsafi na raha cikin waƙoƙin wannan bawan Allah inuwa ce ta
halinsa mafi rinjaye a rayuwarsa. Halin kuwa shi ne ƙin barin matsala kome tsananinta ta tauye shi, halin da mai
ilmi irin Haliru, tushensa shi ne tawali’u da tawakkali ga Allah Ma’ishin bawa
ga kome.
Wannan maƙala wani yunƙuri ne na zurfafa nazari
cikin sigogin waƙa musamman haliyya wadda har yanzu ba
ta samu kulawar manazarta sosai da sosai ba. Nazari a kan haliyya cikin waƙoƙi wani fage ne da zai iya taimakawa
wajen wasa ƙwaƙwalwa da kaifafa tunani.
Ya kamata a yanzu a ga ɗaliban waƙoƙin Hausa sun fara maye
hanyar rattabe da ta motsa ƙwaƙwalwa da kutsawa cikin surƙuƙin tunanin mawaƙi. Ɗaya daga waɗannan hanyoyi ita ce nazarin haliyya cikin waƙa.
Tushen Bayani
1. Duba maƙalar Abdulƙadir Ɗangambo (1981) “ Ɗaurayar Gadon Feɗe Rubutacciyar Waƙar Hausa”, wadda ya gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani na Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, shafi na 12-13.
2. Domin ƙarin bayani game da haliyya duba maƙalar Abdullahi Bayero Yahya (1984) “Haliyya Cikin Waƙa”, wadda ya gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani na Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Sakkwato (yanzu Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo) Sakkwato, musamman shafi na 1-3.
3. Marubucin wannan maƙala ya fara saduwa da Alƙali Alhaji Haliru Wurno tun a farkon gomiyar 1970. To amma a lokacin sanin nesa ne domin bambancin yawan shekaru da lalurar zuwa makaranta ta marubucin maƙalar. Daga 1981 ne suka samu shaƙuwa da juna duk kuwa da cewa ‘yan uwan juna ne.
4. Liman Abdulƙadir Macciɗo ke nan, limamin Masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello. Ko kafin wannan mashahurin malami ya karantar da Alƙali Alhaji Haliru Wurno, ya karantar da wasu kakanninsa da babanninsa. Waɗannan sun haɗa da Waziri Junaidu ɗan Waziri Muhammadu Buhari da Yahya Nawawi ɗan Waziri Abdulƙadir Macciɗo. Domin ƙarin bayani duba Hamidu Alƙali (2002) The Chief Arbiter: Waziri Junaidu and His Intellectual Contribution, Kaduna: Baraka Press and Publishers, shafi na 30-36, littafin da mai wannan maƙala yake kan fassarawa da sunan ‘Shugaban Maslaha’.
5. Wannan ƙane shi ne Sambo Yahya Nawawi. Lokacin da zai fara tafiya makarantar sakandare ta garin Tangaza, mahaifinsa ya rubuta wasiƙa zuwa ga Haliru Wurno yana mai cewa, “… ga ƙanenka nan ka kula da shi game da karatunsa, na gida da na boko - - - “ Karatun gida a nan yana nufin karatun sani na addini.
6. A shekarar 1994 marubucin wannan maƙala ya gayyato wa ɗalibansa na ALH.312 Haliru Wurno domin su tattauna da shi a kan tarihinsa da waƙoƙinsa da ma waƙa gaba ɗaya. An yi wannan saduwa ranar 08/01/1994 kuma an ɗauke shi hoto, an kuma ɗauki wasu waƙoƙin da ya rera cikin kases na rikoda.
7. Cikin hirar da ya yi da ɗaliban kwas na ALH 312 a shekarar 1994 a Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, ranar O8/ 01 / 1994.
8. Wato Malam Musa Abdullahi Zariya wanda aka sha yin hira da shi a kafafen watsa labarai kamar Sokoto State Television (S.T.V.) (yanzu Rima Television, R.T.V.), da gidan telebijin na Nijeriya a Sakkwato (NTA). Mutum yana ƙare faɗa masa lisafin da yake bukatar amsarsa shi kuwa Ka-Fi-Komfuta-Sauri zai faɗi amsar. Mai wannan maƙala ya taɓa tambayar wannan bawan Allah yadda amsoshi suke zo masa ba tare da ɓata lokaci ko wahala ba. Sai ya amsa da cewa shi kansa bai sani ba illa haka kurum yake ganin amsar a gabansa, wato a idon zuciyrsa!
9. Duba Abdullahi Bayero Yahya (1987) ‘The Hausa Verse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style And The Background of Islamic Sources And Belief”, kundin digiri na Ph.D (Hausa), Sokoto: Jami’ar Sakkwato (yanzu Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo), shafi na 398 don ƙarin bayani. Haka nan kuma Mohammad Aminu Ibrahim (1984), ‘Alƙali Alhaji Haliru Wurno Da Waƙoƙinsa’, kundin digiri na B.A., Sokoto: Jami’ar Sakkwato, shafi na 15
10. Misali, marubucin maƙalar nan ya samu wata waƙar madahu a wurin Haliru mara suna, alhali ya mallaki “Korama da “Jirgi” da kuma ’Gulbi’. Da ya tambayi Haliru sunan wannan waƙa sai ya amsa da cewa, ‘To ai sai ka ba ta sunan, duka ɗai na” A nan ne ya ba mawaƙin shawarar a ba ta suna “Filafili” saboda an riga an samu “Ƙorama” da Jirgi” da kuma Gulbi, sai kuma Haliru ya aminta da haka.
11. Salon shillo shi ne yin jerangiya da wani jigo(wata magana) a farkon waƙa kuma jigon ya kasance ba shi ne ainihin babban jigon waƙar ba amma kuma daga bisani sai mawaƙi ya ƙulla su. Domin ƙarin bayani duba Abdullahi Bayero Yahya (2001) Salo Asirin Waƙa, Kaduna: FISBAS, shafi na 113 – 4
12. Jinsintarwa kamar wada Abdulƙadir Ɗangambo ya ba da shi salo ne wanda ‘mawaƙi yakan ɗauki wasu halaye, siffofi, darajoji da sauransu da mutum ne kawai aka sani da su, a laƙaba wa wani abu marar rai ko dabba, tsuntsu, ƙwaro da sauransu. To amma wani lokaci abin yakan zama akasin haka”. Saboda haka sai ya kasa wannan salo zuwa kashi uku; mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa. Dubi maƙalarsa (1981) ‘Ɗaurayar Gadon Feɗe Rubutacciyar Waƙar Hausa”, a ƙarƙashin ‘Mutuntarwa’, shafi na 14. Haka nan kuma a cikin Salo Asirin Waƙa da kuma “Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa” cikin Audu Yahya Bichi da wasu (2002), Studies In Hausa Language, Literature And Culture 5, Kano: Centre For The Study Of Nigerian Lanuages, shafi na 226, an kira wannan salo da sunan jinsarwa.
13. Duba Abdullahi Bayero Yahya (2001) T.D.A.S. shafi na 108 – 113.
14. Akwai cikakkiyar wannan waƙa cikin Ahmed Abdullahi Sokoto (1998) ‘Soyayya Ruwan
Zuma: Nazari Da Sharhi Kan Wasu Rubutattun Waƙoƙin Soyayya A Sakkwato’, kundin digiri na M.A. (Hausa),
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, shafi na 133-135.
15. A nan ina kwaikwayon Aliyah Adamu
Ahmad (2003) “Nazarin Zambo- Zagi A Adabin Hausa: Tsokaci Kan Siyasar Arewacin
Nijeriya (1950-1966)” kundin digiri na M.A. (Hausa), Sokoto: Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, inda ta yi amfani da abin da
ta kira salon zambo-zagi.
16. Wannan waƙa nusuha biyu take da su. Shafukan nusuha ta farko ba su
cika ba amma sun ƙunshi baiti 166. Wasu shafuka ne suka
salwanta domin shafin ƙarshen takardun shi ne na 12 kuma yana
da ja-makafi da ( بيا الله). Nusuha ta biyu kuma wadda nake ganin
ita ce ta biyo baya, tana da baiti 251 da kuma tammat, wanda ya nuna cewa
wannan nusuha cikakkiya ce. Ita ma shafuka goma sha biyu ne take da, sai dai
takardunta sun fi tsawo da kuma ɗaukar baitoci, Kowane shafinta in ban
da shafin farko yana da baiti 22. Na farkon yana da 17 saboda Bisimilla da kuma
sunan waƙar. Nusuha ta ɗaya tana da baitocin da yawansu yake
sauyawa daga wannan shafi zuwa wancan, sai dai babu shafin da yake da fiye da
baiti 16. Tsakanin 10 da 16 suke ɗauka.
17. A nan ina kwaikwayon Atiku Ahmad
Dunfawa ne inda ya karkasa zuga zuwa zuga kumburau, da zuga kariyau da zuga
ingizau, duba maƙalarsa (2002) “Zuga A Waƙoƙin Fada’, wadda ke a kan hanyar
bugawa. Kirari dai babbar manufarsa ita ce kwarzantawa da zugawa.
Manazarta
1. Alƙali, H. (2002) The Chief
Arbiter: Waziri Junaidu And His Intellectual Contribution, Kaduna: Baraka Press
and Publishers.
2. Ahmad, A. Aliyah (2003),
‘Nazarin Zambo-Zagi A Adabin Hausa: Tsokaci Kan Siyasar Arewacin Nijeriya
(1950-1966), kundin digiri na M.A. (Hausa), Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
3. Ɗangambo, A. (1981) “Ɗaurayar Gadon Feɗe Rubutacciyar Waƙar Hausa”, maƙalar da aka gabatar a
Taron Ƙara Wa Juna Sani na Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
4. Dunfawa, A.A. (1987) “Zuga A Waƙoƙin Fada”, maƙalar da aka gabatar a Taron Ƙawa Wa Juna Sani na Sashen Harsunan Nijeriya, Sokoto:
Usmanu Ɗanfodiyo, kuma tana kan hanyar bugawa.
5. --------------- (2002) “Waƙa A Tunanin Yara”, kundin Digiri na Ph.D, (Hausa), Sokoto
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
6. Sokoto A.A. (1998) “Soyayya Ruwan
Zuma: Nazari Da Sharhi kan Wasu Rubutattun Waƙoƙin Soyayya A Sakkwato”, kundin digiri na M.A. (Hausa),
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
7. Furniss, G. (1996) Poetry, Prose
And Popular Culture In Hausa, Edinburgh: Edinburgh University Press.
8. Bunza. A.M. (2003) “Ibarahim Yaro
Yahya A Mizanin Hasabi: Mamaren Ƙyallaro Ɗabi’unsa Da Shahararsa A Mahangar Malaman Hisabi”, cikin Ɗegel: Journal Of The Faculty Of Arts and Islamic Studies
VI, shafi na 266-275, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
9. Yahya, A.B. (1984) “Haliyya Cikin
Waƙa”, maƙalar da aka gabatar a Sashen Koyar Da
Harsunan Nijeriya, Sokloto: Jami’ar Sakkwato.
10. -------------- (2001) Salo Asirin
Waƙa, Kaduna: FISBAS Media Services
11. -------------- (2003) “Kana Shire
Baban ‘Yan Ruwa Na Bello Jikan Ɗanfodiyo: Waƙa A Kan Guri Da Hange Da Dahir”, cikin Ɗegel: Journal Of The Faculty of Arts & Islamic Studies
VI shafi na 252 – 265, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
12. ------------ (2002) “Siffantawa
Bazar Mawaƙi: Wani Shaƙo Cikin Nazarin Waƙa”, cikin Studies In Hausa
Language, Literature And Culture V, shafi na 220 – 240, Kano: Jami’ar Bayero.
13. Wasu waƙoƙin Alƙali Alhaji Haliru Wurno waɗanda mai wannan maƙala ya samu daga hannun mawallafinsu. Waɗannan waƙoƙi da ajami aka rubuta su kuma da hannun Haliru.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.