Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin ya halatta mu riƙe Ƙur'ani muna bayan liman a sallah tahajjud?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam idan liman Yana karatu a sallar tahajjud muna bayansa muna riƙe alƙur'ani (Mus-haf) muna dubawa ana sallah, shin yin haka ya halasta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

وعليكم السلام ورحمة الله.

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Yafi dacewa ga mai koyi da liman (Mamu ke nan) a sallah kar ya riƙe Ƙur'an a lokacin da liman yake karatu a sallah. ya fi kyau mamu ya natsu ya riƙa sauraren karatun liman.

An miƙa tambaya ga babban malami Shaykh bin Baaz (rahimahullah) cewa "Meye hukuncin mutum dake bin liman sallar taraweeh amma yana riƙe da Al-ƙur'ani yana dubawa?"

Sai Shaykh bin Baaz (rahimahullah) ya amsa da cewa; Bansan wani asali (na Sunnah) ba ga yin hakan. ya fi dacewa ya natsu ya samu khushuu'i a sallar, kar ya riƙe Ƙur'ani (Mus-haf), sannan ya dora hannunsa na dama a kan na hagu a kan ƙirjin sa domin yin hakan Sunnah ne. Wannan shi ne ra'ayi mafi kyau.

Amma riƙe mus-haf (Ƙur'ani) zai hana shi aiwatar da wannan Sunnah. Kuma idonsa da zuciyarsa zasu riƙa kallon rubutun dake a shafukan mus-haf ɗin, yin haka zai hana shi sauraron karatun liman. Abin da nake tinani shi ne rashin riƙe Ƙur'ani ga mamu shi ya fi dacewa da sunnah, sannan ya yi sauraron karatun liman da kyau ba tare da ya riƙe Mus-haf ba. Idan yanada ilimin Ƙur'ani, zai yiwa liman gyara idan ya yi kuskure a karatu. Idan kuma shi baida hadda mai karfi toh wasu mutane (sauran mamu) zasu yiwa liman gyara idan ya yi kuskure a karatu. Idan kuma aka rasa Wanda zai yiwa liman gyara idan ya yi kuskure, toh babu laifi. Daman kuskure a cikin fatiha shi ne matsala, sabida Fatiha rukuni ce a cikin sallah kuma sallah bata inganta saida cikar Fatiha. Idan aka bar ayah a cikin karatun matuƙar ba a cikin suratul Fatiha bane, toh babu laifi idan babu mai iya gyara masa a cikin mamu.

Idan a cikin mamu babu wanda zai iya yiwa liman gyara idan ya yi kuskure ko tsallake a cikin karatu, toh anan babu laifi mutum ɗaya ya riƙe Ƙur'ani (Mus-haf) domin ya riƙa yiwa liman gyara saboda larura ne. Amma idan kowane Mamu ya riƙe Ƙur'ani (Mus-haf) toh wannan ya saɓawa Sunnah.

An sake tambayar Shaykh Bin Baaz (rahimahullah) a kan cewa; "Wasu daga cikin jama'a (Mamu ke nan) suna buɗe Ƙur'ani (Mus-haf) suna bibiyar karatun liman a sallah, shin akwai laifi a hakan?"

Sai ya amsa da cewa; Abin da ya bayyana agareni shi ne kar suyi hakan. ya fi kyau su maida hankalisu su kuma natsu ga sallah Su dora hannayen su a ƙirjinsu. Sannan suyi sauraron abin da liman ke karantawa. Saboda fadar Allah a cikin Alƙur'ani;

وَإِذَا قُرِئَ الْقُرْآنُ فَاسْتَمِعُوا لَهُ وَأَنصِتُوا لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ.

الأعراف (204).

Kuma idan an karanta Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.

(A'araaf, 204).

ﻗَﺪْ ﺃَﻓْﻠَﺢَ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ. ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻓِﻲ ﺻَﻼﺗِﻬِﻢْ ﺧَﺎﺷِﻌُﻮﻥَ.

Lalle ne, múminai sun sãmi babban rabõ. Waɗandan suke a cikin sallar su mãsu tawãli'u ne.

(Al-muuminun, 1-2).

ﻭقال ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ‏ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﺟُﻌِﻞَ ﺍﻹِﻣَﺎﻡُ ﻟِﻴُﺆْﺗَﻢَّ ﺑِﻪِ ﻓَﺈِﺫَﺍ ﻛَﺒَّﺮَ ﻓَﻜَﺒِّﺮُﻭﺍ ﻭَﺇِﺫَﺍ ﻗَﺮَﺃَ ﻓَﺄَﻧْﺼِﺘُﻮ

Kuma Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace; An sanya muku liman domin ku yi koyi dashi, idan ya yi kabbara ku yi kabbara, idan yana karatu ku yi shiru (Ku yi sauraron karatun sa).

(Majmu'ul Fataawa na Al-Shaykh Ibn Baaz, 11/340-342).

الله أعلم،

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments