𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah malam Barka da warhaka ya ibada ya kokari, malam tambaya ta ita ce shin mutum zai iya yin zakkar fidda kai, da abin da aka bashi kyauta kamar shinkafa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
waalaikumussalamu Eh zai iya yi in shã Allahu matukar dai 'kimar abincin takai ya fitar da zakkar fidda kan, kai ko da shi wanda aka bawa zakkar fidda kan to idan an tara masa ita da yawa yadda shi ma zai iya fitarwa to shi ma An wajabta masa fitar da itan bawai zuwa zeyi ya tare ta a ma'ajiyar abincinsa ba a'a shi ma ya yi zakkar fidda kan ga mabukata da abin da ya yi ragowa daga abincin da aka tara masa Domin so ake yi musulmi ya kasance cikin farin ciki da walwala a wannan lokacin. Kuma wannan zai nuna maka kuskuren da wasu suke yi za ka samu an tarawa wani sadakar fidda kai wacce zai kai tsawon kwanaki yana ci Amma sai ya jibgeta a cikin gida bayan akwai sauran mabukata waɗanda basu samu ba
WALLAHU A'ALAM
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.