Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Ɗaukar Hoto?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ɗaukan hoto da muke yi da Handsets ko Camera, Halal Ne Ko Haram ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Malamai sun yi saɓani a kan hukuncin hoto, inda waɗansu malamai irinsu (Nasirudden Albani) sukeda fahimtar haramcin hoto kai tsaye indai ba na laruraba, kamar Fasfo (passport) na aikin hajji ko na shiga wata ƙasa dai kokuma dai duk wani hoto wanda larurace take hukunta ayishi toh sukace wannan babu laifi saboda larura, amma hakanan kawai dan gayu ko wani abu a yi hoto sukace bai halasta ba

Amma irinsu (Usaimin) idan ka duba fatawarsa zakaga ya yi wani tafsiri me ban ƙaye wanda muma akanshi muke, wato muna tare da fahimtarsu (Usaimin)

Malamin ya ce: haramun ne a yi zanen duk wata halittar Allah, kamar zana hoton mutum ko akuya ko kaza ko jaki kawai mutum yazauna yana zana hotonsu wannan kaitsaye haramun ne, wannan ya kunshi har hotunan da akesa yara yan primary suna zanawa na dabbobi, dakuma wanda yake sana'ar zana hoton mutane, kawai mutum yazauna ana kallonshi ana zana surarshi ahoto wannan dukansu haramun ne.

Amma hoto na camera sukace wannan babu laifi, baya cikin kwaikwayon halittar Allah matukar baza a yi editing ba, shi wannan editing ɗin haramun ne.

Masamman sanya fuska a wani gangan jiki da abin da ya yi kama da hakan. wannan haramunne kwarai da gaske

Amma dai shi ma hoton cameran sukace kar ayawaita a ɗan yinshi sama sama, musamman ga namiji sukace idan kabiyema yawan ɗaukar hoto sai kuma kazama tamkar ɗan daudu.

Aduba fatawa ta (Ibn usaimin) za'aga tafsirin da ya yi In shã Allahu, hakama a cikin littafin usulut tafsir yadanyi tsokaci gameda hakan.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments