Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ya Sa Aka Ɓoye Daren Lailatul Ƙadri?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis shin me ya sa aka ɓoye daren lailatul ƙadri?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Sheikh Ibn Uthaymeen Allah ya yi masa rahama Yana cewa:- "Allah ya ɓoye ilimin daren Lailatul Ƙadri ga bayinsa, dan rahama ga bayinsa dan su yawaita aiyuakan ɗa’a a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadana cikin neman wannan daren, da an sanya a wata rana ɗaya sananniya kamar ranar arfa to da sun yi ibada kaɗai Saboda ibadar dare ɗaya kaɗai za su yi, amma da yake ya ɓoye hakan sai su yawaita ibada a daren goma gaba ɗaya suna neman dacewa da shi hakan ya fi falala da Yawaita ibada da samu lada da matsayi mai yawa da girma a wajen Allah.

Dan haka ake so su yawaita yin waɗannan manyan ibadun a cikin waɗannan dararen don dacewa da daren Lailatul Ƙadri.

Ibadun sun hada da:- Sallah, Zikiri da Addu'a da Karatun Al-Ƙur'ani

@ﻣﺠﺎﻟﺲ ﺷﻬﺮ ﺭﻣﻀﺎﻥ 173]

Ibn al-Jawzi, Allah ya yi masa rahama, mai albarka da daukaka Yana cewa:- Ayyub ya ruwaito daga Abi Ƙulabata yana cewa:- "Daren Lailatul Ƙadari yana chanchanzawa a kwanakin goman karshe na Ramadana, a cikin mara, hikimar ɓoye wannan dare kuwa shi ne dan mutane su dage da Yawaita ibada a karshen watan Ramadana suna neman dacewa da wannan daren mai albarka, ibadar su da aiyukan ɗa’a na su ya karu tare da samu falala mai girma........ "

@زاد المسير

Ibn al-Jawzi, Allah ya yi masa rahama, mai albarka da daukaka Yana cewa:- "An ɓoye daren Lailatul Ƙadri ne Saboda da manyan dalilai guda biyu:-

1- Rahama ga bayin Allah dan su dage da aiyuakan ɗa’a a kwanakin goman karshen Ramadana suna raya daren da ibada dan karshen wata ya zama sun yi aiyuakan masu yawa fiye da farkon Ramadana.

2- Dan su dage da aiyuka masu yawa Saboda ba su da tabbas ko za su kara riskar wani Ramadan nan gaba, kila wannan shi ne Ramadan nasu na karshe a rayuwar su".

@التبصرة (٤٩٣/٢)

Allamat Abdul Hamid bn Badis Allah ya yi masa rahama, albarka da daukaka Yana cewa:- An ɓoye daren Lailatul Ƙadri ne dan wanda zai neme shi kaɗai sai wanda yake neman lahira fiye da duniya sai ya nace cikin neman sa cikin kwanaki goman karshe dan ya dace da wannan dare..... "

@آثار ابن باديس

 Allah ne Mafi sani

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments