Ilmi: Matashiyar Da Marubuta Waƙoƙin Hausa Suka Sha Karrarawa

    Daga tarkar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.

    Abdullahi Bayero Yahya
    Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
    Jami’ar Usmanu ƊanfodiyoSakkwato
    Email: 
    bagidadenlema2@gmail.com 
    Phone: 
     07031961302

    Tsakure

    Marubuta waƙoƙin Hausa na jiya da na yau, sun sha karrara muhimmancin ilmi ga ƙasa da alummarta. Sun karrara wannan saƙo a tsawon zamani saboda hangen nesan da suke da, da kuma nauyin da addinin Musulunci ya ɗora musu. To amma abin damuwa ne ganin cewa Hausawa (kuma ga alama da dukan al’ummomin ƙasashe masu tasowa) ba su saurari wannan kira ba, sai fa watakila da kunnuwan ƙashi! Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin sake kawo wannan saƙo na marubuta a wuri guda domin ita ma ta karrara shi.

    1.0 Gabatarwa

    Marubuta waƙoƙin Hausa ba su kasa ba a fagen ilmantar da jamaarsu da kuma faɗakar da su ta kowace fuska. Ƙudurin da wannan maƙala ta sa a gaba shi ne, bayyana saƙon marubutan dangane da muhimmancin ilmi. Za ta kuma yi tsokaci kan haɗarin da ke yi wa wannan alumma tamu barazana saboda watsin da muka yi da wannan saƙo, muka biye wa son ranmu da kuma bukatun wasu ko yaudararsu. Mun saurari wannan saƙo da kunnuwan ƙashi sai munka yi wada munka so, tilas kuwa mu ga wada ba mu so.[i] Ba nufin maƙalar ne ba ta bi tsawon tarihi don ta kawo faɗar dukkan marubuta waƙoƙin Hausa. Wannan aiki ne mai bukatar lokaci da bincike mai zurfi. Misalai za su wadatar a matsayin wakilai, da fatar cewa abin da Hausawa suka ce na daga maganganunsu na hikima zai yi tasiri kan mai karatu ko saurare. Wato, “Nuni ya ishi mai hankali”.

    2.0 Matashiya Kan Ilmi

    Mene ne marubuta waƙoƙin Hausa suka yi ƙoƙarin faɗakar da jamaarsu dangane da ilmi domin su ga cewa rayuwarsu ta inganta cikin mutunci? Amsar wannan tambaya ita ce maƙasudin wannan sashe.

    Ya kamata a fahimta da cewa Hausawa mutane ne waɗanda ke daawa da Musulunci a matsayin addininsu. Saboda haka ne kusan gaba ɗayan aladunsu suka kasance inwar wannan addini, domin shi Musulunci kansa hanyar rayuwa ne. Tsakaninsa da wasu hanyoyin rayuwa babu zancen hawan matsayin sasantawa ko na ‘yan-ba-ruwanmu.

    Musulunci addini ne wanda ya ɗauki ilmi da aiki da shi da muhimmanci ƙwarai da gaske, fiye da duk wani addini ko hanyar rayuwa. Su kuwa mafi yawan marubuta waƙoƙin Hausa, kuma musamman na can zamanin da, kafin ƙarni na ishirin, malamai ne waɗanda suka nemi ilmi suka kuma yi aiki da shi. Saboda haka ashe ba abin mamaki ne ba idan a cikin waƙoƙin da suka rubuta muka ga suna ƙarfafa muhimmancin ilmi ga alummarsu. Wannan ƙarfafawa kuwa kan zo ta fuskoki da dama na salon waƙa. Misali, dubi yadda Shehu Usmanu ɗan Fodiyo da mabiyansa suka nuna darajar ilmi:

    Hadisi da Ƙuran kuna ji zumaina
    Da ijma’u su ukku ɗai ab bukina
    Ga dubin su kullum dare in da rana
    Akul na ga littattafi in yi murna
    Suna gwada mai so ga Sunna tasa
    (Shehu Usmanu/ Isa ɗan Shehu/ Abdullahi Mai Boɗinga: Maamaare).

    Alamomin ilmi ne Shehu da mabiyansa suka yi amfani da su domin su jaddada muhimmancin ilmi. Sun bayyana wa jama’arsu cewa su ba su da wani abin da suke so kuma suke murna da shi wanda ya fi Alƙurani da littattafan hadissai da sauran littattafai. Da zarar suka ga waɗannan sai zukatansu su cika da murna domin littattafai ne, ba wani abu ba, masu yi musu jagora zuwa ga babban gurinsu, wato koyi da Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi. A taƙaice waɗannan marubuta sun yi amfani da alamomin ilmi domin su ƙarfafa muhimmancinsa.

    Su kuwa jama’ar da waɗannan marubuta suka jagoranta ta rage gare su su fahimta, su ma su zamo masu murna da littattafai kamar wada masu yi musu jagoranci suka yi. A bayyane take gare su cewa waɗannan masu jagora sun sami girma da ɗaukaka. Ƙaunar da kuwa suka nuna ce ga littattafai ta kasance sanadin wannan ɗaukaka. Sun so ilmi, sun neme ilmi kuma sun yi aiki da shi. A sanadiyyar haka ne suka gane yadda za su yi koyi da masoyinsu mai daraja, Annabi Muhammadu (T.AG.S.). Wannan ne ya jawo musu duk ni’imar da ake gani gare su, kamar dai yadda suka faɗa cikin waƙar:

    Da yin arziki har wadatag ga duk
    Gare ni da girma da samun su duk
    Da albarkacin Ahma yas samu duk
    Ƙawata ta addin da kyawonta duk
    Dalilin kirari da bege nasa.
    (Ma’ama’are). 

    A wata waƙa marubutan sun bayyana mana a fili cewa ilmi shi ne mabuɗin kowace irin daraja. Rashinsa kuwa kan kai mutum ga kowace irin halaka. Rashinsa ba alfanu ne ba ga marashinsa da kuma al’ummar da yake cikinta. Jahili bai da amfani ga kansa da al’ummarsa. Idan al’umma ta yi rashin sa’a ta sanya jahilai a gaba domin su shugabance ta, to kuwa tilas wannan al’umma ta jure wa zalunci. Ga dai abin da waƙar Tabban Haƙiƙan ke cewa a wani baiti:

    Kui karatu zumai ku zam tar da ilmi
    Shi ka sa ɗan Adam shi zam mai muƙami
    Kada ka zamna cikin waɗanda ba su san ta-komi
    Masu ƙwace cikin ƙasashen Musulmi
    Su wuta kam fa ƙwace tabbat haƙiƙa
    (Shehu/Asma’u Nana/Isa: Tabbat Haƙiƙa). 

    Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu, shugaba ne wanda ya san muhimmancin ilmi. Ya yi iyakacin ƙoƙarinsa don ganin jamaarsa ta nemi ilmi. Ƙanwarsa, Nana, ta tabbatar mana da wannan cikin waƙarta mai suna Waƙar Gewaye:

    Ya hore littaffai Usulu da fiƙihu duk
    Haka ɗibbu ko haka hadissai majilisa
    (Asma’u Nana: Waƙar Gewaye).

    Muhimmancin wannan baiti na Nana shi ne, ta yi amfani da kalma ɗaya wadda ke nuna cewa ba ilmin addini ne kurum daular Musulunci za ta kula da shi ba. Kalmar ita ce ‘ɗibbu, wadda ke nufin magani kuma take nuni da muhimmancin neman ilmin magunguna. Cikin baiti guda Nana ta bayyana irin muhimmancin da wannan Sarkin Musulmi ya ba ilmi kowane iri, na duniya da na Lahira.

    A cikin ƙarni na ishirin kuwa marubuta ba su gaji ba. Hasali ƙara tashi tsaye suka yi haiƙan don ganin jamaa ta yi amfani da wannan matashiya. Dalilai da dama ne suka haifar da haka. Na farko shi ne, sun lura da cewa mutane sun kauce ma hanyar da magabata suka shimfiɗa tun farko. Tun da kuwa suka kauce ashe kuwa da wuya ma su damu da matashiyar da magabatan suka yi dangane da ilmi. Dalili na biyu shi ne, a ƙarni na ishirin sai aka wayi gari da cewa aiki ya kasu kashi biyu ga marubuta dangane da faɗakar da jamaa ta fuskar ilmi. Wato, ko bayan irin matashiyar da aka riga aka san da ita, ta tun cikin zamanin Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, akwai kuma bukatar yin faɗakarwa ta fuskar wani fannin ilmi da ya shigo ƙasar Hausa. Wato ilmin boko wanda Turawa suka zo da shi.

    Ta fuskar ci gaba da matashiyar da aka faro tun kafin ƙarni na ishirin an sami marubuta da dama musamman waɗanda tarbiyyar da suka tashi da ita ta wancan zamanin ce. Malam Abubakar Maikaturu yana daga cikin waɗannan. Sanannen malami ne wanda ya rayu a Sakkwato tun da sauran danshin daular Musulunci wadda su Shehu Usmanu suka shimfiɗa.[i] Ya yi mana ishara ga muhimmancin ilmi ta hanyar bayyana cewa a duk tsawon tarihi ɗan Adam bai taɓa samun daraja ba face sai ya kasance yana da ilmi. Ya yi kashedi ga wanda ya bari mutane suka yaudare shi da cewa shi mai daraja ne alhali kuwa ya san da cewa shi jahili ne. Ga dai faɗar Maikaturu:

    Waɗansu nan suka naɗin na Allah
    Su azzama shi babu ko kamala
    Ana darajja bisa babu ilmi?
    Haƙiƙatan waɗanga su at awami
    Ka dubi anbiya’u mursalina
    Ka dubi auliya’a salihina

    Wa ad da jahli a cikin waɗanga?
    Kun mance ashabu rasulu gagga
    Jaki shi shuri ɗan uwanai jaki
    Kura ka ɗamre ta wurin sayaki
    (Abubakar Maikaturu: ‘Yan Jahadi).

    Shi kuwa Mu’azu Haɗeja biyu ya haɗa. Ya sami yin karatun addini da na boko. Saboda haka mai iya yin matashiya ne kan kowane daga biyu ɗin.Wannan shi ya sa ya nanata raayoyin Nana Asmau da Abubakar Maikaturu, har ma da na magabatansu, a cikin waƙoƙinsa fitattu. A waƙarsa da ya kira Mu Nemi Ilmi, wadda tun ma daga jin sunanta ka san da niyyar karrara muhimmancin ilmi aka tsara ta. Malam Muazu ya fara da fayyace mana ilmin da za mu nema:

    Ilmud duniya ilmud dini
    Su ne rabbai biyu don ilmu
    Ilmuf fiƙihu ilmuɗ ɗibbu
    Su ne ilmani na nemammu
    (Mu’azu Haɗeja: Mu Nemi Ilmi).

    Mu’azu ya ci gaba da rarrashin mu domin mu rungumi ilmi da aiki da shi, mu sami girma da ɗaukaka da ci gaba. Ya yi haka ne ta hanyar ishara ga halin da ake ciki da kuma tarihi:

    Duka kun ji muguntar jahilci 
    Kuma za ku ji amfanin ilmu

    Mota jirgin sama lantarki
    Su wayalis ga su ƙasashemmu

    Hikimomin Turawa sun zarce
    Mu lasafta su ƙasashemmu

    Kome ka gani masana’antu
    Na Nasara cikinsa Akwai ilmu

    Mil dubbai sunka taho suka ci
    Mu Saboda sanin zurfin ilmu

    Har ga wasu ma a maƙwabtammu
    Su ke ɗaga hanci sun fi mu

    Har suna tsammani su suka ka-
    Wo Turawa suka mulke mu
    (Mu’azu Haɗeja: Mu Nemi Ilmi)

    To amma a waƙar Ilmin Zamani Muazu Haɗeja ya warware mana zare da abawa na muhimmancin ilmi. A cikin wannan waƙa ya yi ta kawo misalai da isharori don ya tabbatar da cewa ba mu kuri saƙonsa ba:

    Gishiri in babu kai ba miya
    Ilmi mai gyaran zamani

    ...

    Ilmi shi ke gyaran ƙasa
    Har a san ta a wannan zamani
    (Mu’azu Haɗeja: Ilmin Zamani) 

    Dubi yadda Mu’azu ya yi amfani da salon kinaya ya kira ilmi da sunan gishiri, ya kuma kira zamani da sunan miya. Kowa dai ya san da cewa gishiri shi ke sa miya ta yi daɗin sha, idan babu shi to sai dai a sha haka nan don babu yadda za a yi, sai fa a ƙi shan gaba ɗaya. Idan kuwa aka ƙi shan, to kuwa ɓarna ta yi. To kamar haka ne Muazu yake son mu kalli ilmi da kuma zamaninmu na rayuwa. Wato, ilmi shi ne ke sa zamani ya yi daɗi a rayuwa. Idan babu ilmi cikin zamani, wato idan ba a tafiyar da zamani da ilmi ba, to salab yake kamar sallaɓar miya.

    A ƙoƙarinsa na yin bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sa ya ce ilmi ne gishirin zamani, sai Mu’azu ya ce ba a sanin ƙasa a duniya, kuma ƙasa ba ta samun inganci face da ta kasance wadda ta rungumi ilmi kain da nain. Ilmi ne mai gyara ta ta kyautu, ta amalta, har ta zamo sai da ita ake yi. Kyautatuwar kuwa ta haɗa da bunƙasar tattalin arziki da daraja da ƙarfi da lafiya da kuma faɗa a ji, kai har ma da sara a inda babu gaɓa (amma fa idan zalunci ya rinjayi aiki da ilmin!).

    Mu’azu ya tunatar cikin lafazi mai firgitarwa ko tsoratarwa cewa sanin duk abubuwan nan dangane da ilmi ba baƙon abu ba ne a gare mu. To amma duk da haka mun yi watsi da shi. Ya ce Turawa sun tarar da mu cikin halin ci gaba a wannan ƙasa. Sai dai kash! Abin takaici shi ne cewa a yau ba ma mu ne a baya ba, aa waɗanda ma Turawa suka tarar tsirara sun shiga gabanmu:

    Yanzu mu ne baya a duniya
    Gaskiya in za mu yi tuntuni

    Ga dalilaina da ya sa na ce
    Maka mun zama baya a zamani

    Tun Nasara gaban ba su zo su ba
    Muka san hanyar neman sani

    Sutura da sana’a sun tarar
    Mu muna yi ko su sun sani

    Sun tarar mu da halin ci gaba
    Ciniki da sarautu sun gani

    Wasu kan akasi aka tad da su
    Yanzu su ne manyan zamani

    Sun yi ƙwazo sun yi ɗawainiya 
    Bisa takidin neman sani

    Matuƙar ba mu tashi a kansu ba
    Za su hau mu a wannan zamani

    Su faɗa tilas mu biye musu
    Su yi mulkin kammu muna gani

     (Mu’azu Haɗeja: Ilmin Zamani).

    Ba ni da sanin gaibu. To amma dai na san da za a ce ni ne Mu’azu Haɗeja, kuma a yau, da kuwa aƙalla na sake rubuta wata waƙa don in faɗa wa jamaata wani abu makamancin, Ai ga abin da nake yi muku gudu nan!” A yau mun fita batun ilmi. Mun banzatar da shi. Mun mayar da shi dodorido. Duk wanda ya tashi a wannan nahiya shekara arba’in ko talatin da suka wuce ya san da cewa a makarantunmu ba a san wani abu wai shi ‘alfarma’ ko maguɗin jarabawa ba. A yau kuwa mu ne masu yin haka. Da yawa daga cikin ɗaliban da muke da su masu darajar A a kusan kowane fanni na ilmin makarantun gaba da firamare, ko rubutun kirki mai karantuwa ba su iya ba. Wannan kuwa sakamakon maguɗin jarabawa ne tun daga ƙoli. Mun wayi gari da jihohin da a bara su ne na baya ga sakamakon jarabawa, amma yau duk ɗalibansu darajar A ne da su ciki da waje. Anya kuwa babu goro cikin wannan miya?! Ashe kuwa gyara ya yiwu cikin dare guda? Dalili ke nan da ya sa ko bayan waɗannan ɗalibai sun sami gurabun shiga jami’a, bayan shekara guda kacal sai ka tarar da su ne kuma suka mahe jerin sunayen waɗanda jamiar ta kora saboda rashin ƙoƙari.

    Alhaji Garba Gwandu ya nuna cizon yatsan da ya sha yi saboda rashin samun zuwa makaranta a sakamakon curutar rashin gani da ta same shi tun yana ƙarami. Ya ɗanɗani zaƙin ilmi kuma duk da wannan lalura da ta kama shi ya dage sai da ya sami ilmi gwargwado. Ya faɗa mana dalilin da ya sa ya hori yayansa da lalle su tafi makaranta. Mutum kuwa in dai mai hankali ne ba zai yi watsi da wannan dalili na Garba Gwandu ba:

    Ilmi rabo na wanda babu awa shi
    Shi mif fi kowane arziki ce min shi
    Don ba ka yin barci a sace ma shi
    Kuma fada ba ka zuwa a ƙwace ma shi
    Na hori ‘ya’yana su je makaranta
    (Alhaji Garba Gwandu: Bulaliya)

    Ilmi ne kurum dukiyar da mai ita ba sai ya rufe ƙofar gidansa ba idan zai shiga kwana, wai don gudun ɓarayi. Ko da waɗannan ƙwari sun zo sai dai su ɗauki wani abu, amma ba ilmin mai ilmi ba. Mai ilmi ba ya bukatar ya kewaye gidansa da katangar da ta yi kama da ta gidan yari, ko kuma ya sa gambun da yake ƙi-albarushi a ƙofar gidansa.. Saboda haka hankalinsa a kwance zai shiga kwana, ya kuma yi mafarki mai daɗi. Haka nan kuma kome zaluncin shugaba dole ya bar mai ilmi da hajarsa. Duk handama da babakere da danniya da rub-da-cikin masu ci da wala-walar ƙuria ba za su iya wawure ilmin mai ilmi ba. Sai dai su ga baya gare shi, wannan kuwa yin Allah ne ba na wani taliki ba. Ilmi ne kurum ya zamo gani-nan-bari-nan ga azzaluman duniya. Wannan shi ne abin da Garba Gwandu ke nufi cikin wannan baiti.

    Garba Gwandu ya ci gaba da faɗakar da mu game da ilmi a wata waƙarsa inda yake cewa,

    Babbar baiwa kyautar Allah
    Kowas samai shi ya wala
    Ilmi mai fid da mutum zilla
    In ba ka da shi kullum illa
    Kaka yi jama’a mu biɗo ilmi 
    (Alhaji Garba Gwandu: Ilmin Gaba Da Furamare).

    Mun riga mun ga cewa mai ilmi shi ke walawa, mai kuɗi kuwa maigadi ne. Wani amfani na ilmi shi ne, mai shi yana da daɗin zama, kuma masanin yadda ake fuskantar matsalolin rayuwa ne. Wanda kuwa bai da ilmi mai dame kome ne, ya ƙara durmuya cikin wahala sannan kuma ya durmuyar da na tare da shi.

    Aƙilu Aliyu wani magabacin Garba Gwandu ne wanda shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a fagen faɗakar da jamaarsa kan muhimmancin ilmi. Cikin raha da annashuwa Aƙilu ya faɗakar da mu game da darajar ilmi inda ya ce:

    A mazanmu har matanmu yara da manya

     Jama’a mu san ilmi muna tarawa

    Shi ne Kadaura ilmu babbar gayya

     Inuwa mayalwaciya wajen hutawa

    ...

    Da za a yarda a ba ni fili in yi

     ‘Yar tambaya sannan a ban amsawa

    ...

    Shin ko akwai namu ba wani ilmi ba

     Mai kai mutum ƙolƙoliyar ɗorawa

    Watakila dai amsarka ai kuwa ba shi

     Ilmi yake hana duk shiri karyewa

    (Aƙilu Aliyu: Kadaura Babbar Inuwa).

    Abin da Garba Gwandu ya ce mai fitar da mutum daga ‘zilla’ ne shi ne Aƙilu ya yi amfani da salon kinaya ya kira shi kadaura, inuwa kuma babbar gayya. Ilmi mahutar ɗan Adam ne, cike da niima. Niimarsa ba ta lisaftuwa. Shi ne mai ɗaukaka mutum ya kai shi inda kowa ba zai iya kaiwa ba. Shi ne mai cire ƙangin bauta. Shi ne mai gyara ƙasa idan ta sukurkuce, alamurranta sun daddame. In ba shi ba duk abin da aka nemi amfani da shi don wannan gyara aikin banza ne.

    Shi kuwa Malam Salihu Kwantagora ya damu ne da ganin cewa jama’arsa ba su ba ilmi da kuma bincike muhimmanci a rayuwarsu ba. A waƙarsa mai suna Girman Sani Ga Mutum, ya jaddada haka:

    Shi kau mutum da sani ya samo ɗaukaka

     Da ya tsere kowa ba kamarsa a duniya

    ...

    Ai babu jayayya bisa ga faɗin haka

     In kun tunane sai ku ƙara tunanniya

    Samun sani ke ƙara ƙarfafa bincike

     Yin bincike ke ƙara ƙarfafa aniya

    ...

    Da sani mutum yas sami ikon aikata

     Manyan lamurran nan na ɗakin duniya

    Su ne kamar saƙa da ɗunki tun daɗai

     Su ne mutum yaf fara koyo ya iya

    ...

    Labudda sai da sani ake iya bincike

     Kana a san nasarar lamurran duniya

    ...

    Samun sani yas sa mutum yin ƙoƙari

     Domin shi bincike al’amurran duniya

    Sai mui kwatanci zamanin da muke ciki

     Mai ƙoƙari shi yac ci riban duniya

    ...

    Sha’anin mutum na ba da mamaki ƙwarai

     Da ayukkansa da yai bajinta ya iya

    Fara da jirgin railway ka tsaya da kyau

     Mi yaf fi jirgi ba da mamaki niya

    Daga ƙoƙari fa mutum ya sami shi yi shi duk

     Mu tuna da nacin bincike baki ɗaya

    ...

    Komo ga mota lura ga jirgin sama

     Kai hankalinka ka je ka leƙa gidan waya

    ...

    Don ƙoƙarinmu da bincike muka san haka

     Gaba kau abin ke yi a kullum safiya

    Kuma ba mu mantawa a kullum ma tuna

     Manyan mutanen nan da za su samaniya

    Su gano wata wane mutum! To kun ji fa

     Nan ne tunane yay yi kauci yat tsaya

    (Salihu Kwantagora: Girman Sani Ga Mutum).

    Salihu Kwantagora yana magana ne kan ci gaban da ɗan Adam ya samu albarkar ilmi da kuma aiwatar da bincike. A haƙiƙanin gaskiya ci gaba ne da Turawa suka samu. Ba mu yan baƙi ko ƙasashen da ke tasowa ba. Mu me muka yi dangane da bincike? Ko akwai wani ci gaba da muka yi bisa ga wanda kakaninmu suka yi? Alal misali, a fagen noma me muka yi na kyautata kalme, ko sungumi? Wace irin sarrafawa muka yi wa kashin shanu baya ga wadda muka gada daga kakani? A fagen makamai me muka ƙirƙiro sama ga makaman da su Shehu Usmanu ɗan Fodiyo suka yi amfani da su? Idan amsar duk waɗannan tambayoyin ita ce babu, ke nan ba mu da sani, ba mu ƙoƙarin tara shi balle daɗa mu aiwatar da bincike domin mu san nasarar lamurran duniya. Mun yi watsi da biɗar sani saboda haka tilas mu miƙa wuya ga abokan gaba. Kai ba abokan gaba ba kurum, ga kowa ma tilas ne mu miƙa wuyanmu gare su muddin dai su sun tara sani.

    3.0Kammalawa

    Matsalar wannan al’umma ita ce yaudarar kanta da take yi ta kowace fuskar rayuwa. A yau ba ilmi ne yaranmu suke nema ba. Takardar shaida ce muradinsu. Saboda haka suke neman dai malami ya san su, la’alla ya tausaya musu wajen gyaran jarabawa. Ta kai ma yau har hadisin tausayawa ɗalibai kan rubuta cikin takardun jarabawarsu. Yaudara da addini ke nan. Malamai kuwa ba ilmi muke neman mu tara ko mu yi aiki da shi ba. A’a muradinmu shi ne a ce mana ‘mallam wane ne, ho ɗi ja!. Alhali kuwa mene ne muka ɓarkata? Ƙololuwar ƙwazonmu ba ta shige tunanin tun kaka da kakani ba. Shaihin malamin dabbobi a wannan ƙasa tamu ba ya jin kunyar yau ya tara jamaa ya gabatar musu da maƙala a kan hanyar da za a bi a ruɓanya yawan awaki idan suka ƙaranta a ƙasa, ko kuma yadda za a iya sa duk awakin karkarar nan su kasance da jar fata! Shi kuwa mai ilmin kimiyyar lantarki ba ya bari ɗalibansa su gwada tunaninsu, sai dai ya ƙarfafa musu aiwatar da ‘bincike’ kan harhaɗa wayoyin kaskon lantarkin ƙarfin rana. A wurinsa wannan bincike ne. Ko dai ba kome, kasaken shigowa aka yi da su daga ƙasashen waje. Su kuwa shugabanni sun dogara ga irin kwarzantawar da kafafen yaɗa labarai za su yi wa ɓaɓatunsu na yaudara. Da ma dai bambaɗawansu ne. Sun yarda da cewa muddin dai suka tsara magana aka yayata ta a kafafen yaɗa labarai, a kwana a tashi talakawa za su ɗauki maganarsu a kan farar gaskiya. Su ce sun kashe biliyoyin Naira wajen giggina ɗakunan karatun da suka fara rushewa tun ba a shige su ba.

    Yau mun yi watsi da ilmi da aiwatar da bincike har mun zamo abin da Mu’azu Haɗeja ke cewa a waɗannan baitoci nasa:

    Mu ne raƙuma su buzaye

     Duka inda suke so sa ja mu

    Lokoto lokoto mun miƙa wuya

     Sai in da suke son tsaishe mu

    (Mu’azu Haɗeja:Mu Nemi Ilmi).

    Wannan shi ne matsayinmu a duniya. Turawa sun mai da mu raƙuma ko ma

    ƙasa da haka. To idan ba haka ne ba ina dalilin dagewar da suke yi cewa kada wata ƙasa ta mallaki makaman ƙare-dangi alhali su suna da su jibge, bila adadin, kuma har kwanan gobe bisa ga sabunta su suke? Ba mu da ilmi kuma ba mu aiwatar da bincike. Hasali yaudarar kanmu muke yi ta hanyar maimaita bincike da kuma baje takardun shaida na matakan ilmi dabam daban ba tare da ɓarkata kome ba. Lokaci yana neman ya ƙure mana alhali ba mu yi kome ba. Mu yi tunani, shin idan ba mu tar da kowace irin fasaha ba, shin idan ba mu iya ƙirƙiro makamai daidai da na sauran ɓangarorin duniya musamman Turawa ba, shin idan muka dogara ga sai an tallata mana kome, mu saya mu yi amfani da shi ba tare da sanin kome game da shi ba, shin kuwa akwai abin da zai hana mu zamo raƙuma?! Babu mai sayar maka da makamin da ya ko yi daidai da nasa balle wanda ya fi shi.

    Makomarmu ɗayan biyu ce: ko dai mu ci gaba da yin watsi da matashiyar da waɗannan marubuta masu basira da hangen nesa suka yi mana, in ya so mu tabbata a matsayin raƙuman Turawa; ko kuma mu saurari kiransu da kunnuwan zukatanmu, mu tashi tsaye. Wannan tashi tsaye kuwa ɗayan biyu ne dangane da hanyar da muka zaɓar wa kanmu: juyin juya-hali ko jihadi. Duk zaɓin da muka ɗauka tilas ne mu kawar da yanayin da ke ci tattare da jiga-jigan da ke wanzar da shi.

    Wassalamu alaikum wa sallallahu ala man la nabiyya ba’adahu, amin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.