Daga tarkar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.
Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Email: bagidadenlema2@gmail.com
Phone: 07031961302
1.0 Gabatarwa
Rawar da adabin Hausa, musamman fannin waƙa, yake takawa wajen gina al’ummar ƙasar Hausa daɗaɗɗiya ce. Tun fari dai Hausawa sun yi amfani da waƙar baka cikin wasanni da tatsuniya domin su cusa wa ‘ya’yansu tarbiyya da al’adu. Wannan rawa ta ci gaba tsawon zamunna har zuwa yau cikin
sigogi mabambanta. Lokacin da rubutacciyar waƙa ta shiga
cikin rayuwar Hausawa, sai rawar da adabinsu ke takawa ta wannan fuska ta faɗaɗa ta kuma ƙarfafa. A wannan muƙala za a yi ƙoƙarin
bayyana hanyoyin da za a iya amfani da rubutattun waƙoƙi domin aiwatar da yaƙi da rashin tarbiyya a wannan zamani cikin Nijeriya. Waɗannan hanyoyi kuwa za su ƙumshi na da da na yanzu.
Ƙumshiyoyin da ke bukatar bayani a wannan muƙala su ne, “yaƙi” da kuma “tarbiyya”. Saboda haka bari a yi bayanin tun yanzu.
Ƙamusun
Hausa ya bayyana kalmar “yaƙi”, da cewa, ‘far wa
wasu mutane da faɗa domin a
mulke su’.
Idan aka faɗaɗa wannan ma’ana sai a ce, ‘ɗaukar
mataki ko matakai domin a kawar da wata ɗabi’a ko al’ada ko cuta daga rayuwar al’umma’.
“Tarbiyya” kuwa wannan ƙamus ya
fassara ta da cewa,
Koyar da hali na gari; hali na gari[i]
Shi kuwa kalamin ‘rashin tarbiyya’, yana nufin babu hali na gari,
a yayin da ‘yaƙi da rashin tarbiyya’ ke nufin ɗaukar mataki ko matakai na kawar da hali ko halaye marasa kyawo’. Ya kamata a lura da cewa duk waɗannan bayanai suna jinginuwa ne
ga al’ummar da
ake magana a kai. Misali, sutura mai rufe al’aurar mutum al’ada ce a
wannan ƙasa tamu, muddin dai ba za a yi
amfani da ita a mummunar hanya mai cutarwa ga al’umma ba. Rashin sanya sutura mai rufe al’aura ga mutum rashin
tarbiyya ne a Nijeriya. Amma an nuna wa wannan marubuci wani gida a wata ƙasa ba ta Afirka ba inda aka ce wurin shaƙatawa ne da kowa ke cire suturarsa ko suturarta. Kuma ba a yarda
ka zauna da sutura ba! Tirƙashi!
Bahaushe dai ya ce, ‘Abincin wani gubar wani’!! Bari dai muƙalar ta fara nomanta.
2.1 Hanyoyin Amfani da Waƙa a Ƙarni Na 17 Zuwa Na 19
A nan idan aka ambaci zamanin da, manufa ita ce, lokacin da ya
shafi wajajen ƙarni na 17 zuwa na 19, amma
musamman ƙarni na 18 da na 19. An kuwa mai
da hankali kan ƙarnonin 18 da 19 ne saboda
dalilai biyu: kasancewar tarihi ya fi taskace rubutattun waƙoƙin zamanin fiye da na kafin sa,
sannan a zamanin ne waƙoƙin suka
samu ranar shanya, suka bunƙasa suka
kuma zama cikin al’adun Hausawa, jini da tsoka.[i]
A shekara ta 1754 ce aka haifi Shehu Usmanu ɗan Fodiyo wanda jama’ar zamaninsa ba su yi kuren baki ba da suka
kira shi nur al
zaman, wato, “hasken zamani”. Da shi da ƙanensa da
‘ya’yansa da sauran mabiyansa sun yi amfani da
rubutattar waƙa don su aiwatar da wa’azi ga jama’arsu
domin su jaddada addinin Musulunci. Su ne suka mai da waƙoƙi tamkar yadda a yau hukuma take
amfani da kafafen watsa labarai domin faɗakar da jama’a game da
manufofinta. Shehu ya lura da cewa Hausawa suna sha’awar waƙa, waƙa kuwa ta kasance ɗaya daga
cikin hanyoyin da mallaman addini ke amfani domin yaɗa addini tun bai iso ƙasar Hausa ba. Waƙar
Larabci da aka fi sani da “Ƙurɗaba”, ta isa misali, domin kuwa har yau ana koyar
da ita a nan ƙasar Hausa, duk kuwa da cewa ta
yo tafiya tun daga ƙasar Andalus (Spain a turance) [i][i], kuma a
zamani mai tsawon gaske.
Su Shehu Usmanu sun rubuta waƙoƙin ne don su ƙarfafa wa’azin da suke yi a makarantunsu da sauran
wuraren da suke yin wa’azin.
Misali akwai “Waƙar Wa’azu”[i] da
“Waƙar Mai Dare Duk Da Safiya” da “Tsarn Mulki Irin Na Musulunci” waɗanda Mallam Abdullahi ƙanen Shehu ya rubuta. Akwai kuma waƙar “Tabban Haƙiƙa” da “Waƙar Lalura” waɗanda shi Shehu ya rubuta. Nana Asma’u ‘yar Shehu
ita ma ta rubuta, kamar “Waƙar Tsayin Alƙiyama” da “Kirarin Ahmada”. Haka shi ma Malam Isa, autan Shehu da aka haifa
bayan rasuwar mahaifinsa, ya rubuta waƙar “Haƙƙin Mumini
A Kan Mumini”. Ya kuma
fassara wasu waƙoƙin
mahaifinsa da na yayarsa Nana. Mallam Abdullahi Mai Boɗinga ya yi tahmisin waƙar Shehu wadda Malam Isa ya fassara da sunan da ta shahara da shi,
wato “Ma’ama’are”.
Waɗannan waƙoƙi da sauransu masu yawa[i] sun kasance ga hannuwan almajiran
Shehu da na Mallam Abdullahi da na mabiyansu. Haka kuma akan rera su a
masallatai daga su almajiran, kuma akan karanta wa almajiran makarantun allo
lokaci lokaci.[i] A fadar sarakuna
ma akan rera waƙoƙin.[i] Misali, akan aiwatar da wannan
al’ada a gidan wazirin Sakkwato.
Marubuta waƙoƙin ƙarni na 17 – 19 ba
rubuta su suka yi suka ajiye kurum ba. A’a, sun rubuta su ne domin su ƙarfafa
karantarwa da wa’azin da
suka yi ga jama’arsu. Sun
rubuta su ne a matsayin wata hanya da suka yi wa al’ummarsu tarbiyya mai kyawo, su kuma yaƙi rashin tarbiyya. A taƙaice,
hanyoyi da aka bi domin yaƙi da
rashin tarbiyya a wancan zamani na ƙarni 18
da na 19 su ne, rubuta da fassara waƙoƙi cikin harsunan gida, da yaɗa su cikin ƙasa ga al’umma ta hannuwan ‘yan makaranta, da rera su a masallatai da
wuraren wa’azi da
makarantu, da kuma karanta ko rera su a fadar sarakuna. Haka nan kuma matan
aure kan gayyato mata dattawa da ke da baiwar rera waƙoƙin domin su yi musu hira ta
tsawon yini a gidajensu. Kada kuma a manta da rawar da ‘yan taru[i] suka
taka. Wannan ƙungiya ce da Nana Asma’u ‘yar Shehu ta ƙirƙiro domin ilmantar da mata. Ƙungiyar
ita ce za a iya a kira da sunan ‘Shiri na farko a wannan nahiya na bayar da
ilmi kyauta ga duk ilahirin mata na daular da Shehu Usmanu ya kafa’. Ita ce
makarantar tafi-da-gidanka domin a duk ƙauyen da ‘yan taru suka biya a kan hanyarsu ta zuwa
Sakkwato ko komawa zuwa ƙauyukansu, sukan tafi ne suna
rera waƙoƙi. Idan
ko a gida suke sukan je gida gida su rera su. A yau watakila a kira wannan a
Turance da, Free
Mobile Education For All Women!
3.1 Hanyoyin Amfani da Waƙa a Ƙarni Na 20 Da Na 21
Ƙarni na 20 ya fara da zuwan Turawan Ingila a ƙasar Hausa, suka yaƙi ƙasar gaba ɗaya har
sai da suka shimfiɗa mulkin
mallaka, lamarin da kuma ya assasa canjin hanyar rayuwa. A sakamakon haka sai
amfani da waƙoƙi ya ɗauki sabbin manufofi ƙari kan waɗanda jama’a suka gada daga zamanin da ya gabata.
Tun da fari dai malaman addini sun faɗaɗa manufar yin wa’azi da
ilmantar da mutane kan addini, wato yaƙi da
jahilcin addini, zuwa yaƙi da baƙin da suka zo suka yaƙe su,
suka kuma kawo al’adunsu da
ba su yi daidai da addinin ƙasar
Hausa ba. Waƙar “Zuwan Annasara”[i] ita ce manazarta ke ganin ta fara wannan sauyi, wanda ya
kasance yaƙi da alƙalami domin ba a iya yaƙar Turawa
da takobi a lokacin. Malam Abubakar Maikaturu da ɗalibinsa Malam Ibrahim Halilu suna daga cikin malaman ƙasar Sakkwato da suka yi wannan ƙoƙari.[i]
Cikin shekarun da Turawa suka yi suna shimfiɗa mulkinsu da al’adunsu, marubuta waƙoƙin Hausa sun ci gaba da amfani da
waƙoƙin domin su tarbiyyantar da yara
da manyan ƙasarsu. Wato sakamakon abubuwan
da Turawa suka kawo sai aka samu malamai iri biyu: da waɗanda suka ci gaba da amfani da waƙa domin ƙarfafa tarbiyyar Musulunci kamar
yadda malaman ƙarni na 18-19 suka yi; da kuma
malamai waɗanda ke
amfani da waƙa domin cusa tarbiyya mai tafiya
tare da sabon zamani, wato Turawa da abubuwan da suka kawo. A cikin waɗannan malamai na kashi na biyu
akwai marubuta waƙoƙi kamar
Malam Sa’adu
Zungur da Malam Mu’azu Haɗeja da Malam Umaru Nasarawa
Wazirin Gwandu. Irin waɗananan
malamai sun yi amfani da waƙoƙi domin su wayar da kai ko su faɗar ko su tarbiyyantar da jama’a kan abubuwan da zamani ya kawo. Akwai waƙoƙinsu kamar ‘Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya’ da ‘Tutocin Shehu Da Waninsu’ da kuma ‘Yadda Ya
Kamata Najeriya Ta Zama’[i]. Haka kuma akwai waƙoƙi kamar ‘Gargaɗi Ga ‘Yan Makaranta’ da ‘Waƙar Nijeriya’ da ‘Hausa Mai Ban Haushi’, duk suna cikin cusa
tarbiyya a fannoni mabambanta[i].
Ya kamata a lura da cewa daga cikin abubuwan da Turawa suka kawo a
ƙasar Hausa akwai na’u’rori da
kafafe waɗanda suka
taimaka wajen amfani da waƙa domin
cusa tarbiyya ko yaƙi da rashinta. Waɗannan kuwa sun haɗa da rediyo da talibijin da
sauransu. Ko bayan hanyoyin da suka saba da su tun shekaru aru aru, malamai sun
kuma yi amfani da waɗannan na’urori da kafafen watsa labarai don cusa tarbiyya
ko yaƙi da rashinta.
Abin da ya fito fili shi ne, waƙa dai ta
taka rawa wajen cusa tarbiyya tun daga ƙarni na
18 har zuwa yau da take cikin takawar. Yanzu muƙalar za
ta mai da hankali ga yadda za a inganta wannan rawa, da ma ƙarin wasu hanyoyin.
Ya kamata a tattara hanyoyin amfani da waƙa waɗanda aka
ambata tun farkon wannan muƙala har
zuwa nan. Hanyoyin kuwa su ne:
1. Rubuta waƙoƙi domin ɗalibai da sauran jama’a.
2. Rera waɗannan waƙoƙi a gaban shugabanni (kamar idan
malamai suka ziyarci sarakuna suka nemi su yi musu wa’azi).
3. Rera su a masallatai.
4. Rera su a makarantun allo.
5. Rera su da ƙungiyar ‘yan taru ke yi daga ƙauyuka zuwa birane, kamar daga ƙauyen
Tcehe zuwa Sakkwato, musamman cikin watan azumi, lokacin da suke sauraren
tafsirin Nana Asma’u.
6. Rera waƙoƙin a
gidaje ga matan aure.
7. Fassara wasu waƙoƙin manyan malamai daga wani harshe zuwa Hausa. Misali, “Waƙar Begore” ta Mallam Tukur Ɗan Binta wadda Nana Asma’u ta fassara daga Fulatanci zuwa Hausa, da “Waƙar Ma’ama’are” wadda
Shehu Usmanu ya yi da Fulatanci ɗansa Malam Isa ya fassara zuwa Hausa. “Waƙar
Daliyya” ta
madahu wadda Shehu Usmanu ya yi da Larabci, Ɗangaladiman
wazirin Sakkwato, Bello Giɗaɗawa ya fassara ta zuwa Hausa.
8. Yi wa wasu waƙoƙi tahmisi kamar “Waƙar Ma’ama’are” da Malam Isa ya fassara, sai Mallam Abdullahi Maiboɗinga ya yi mata tahmisi.
9. Rubuta waƙoƙi domin
rerawa a taron siyasa.
10. Buga waƙoƙi cikin
jaridu.
11. Rera waƙoƙi a
gidajen rediyo da talibijin.
12. Rera wa ‘yan makarantun Islamiyya da na Boko waƙoƙin da malamansu kan rubuta.
13. Sanya waƙoƙin cikin
kase-kases da faifan konfuta.
3.2 Tsakuren Baitoci A Lokutan Labarai Da Jawaban Shugabanni
A yanzu ne ya fi dacewa idan aka hukumta cewa a duk lokacin da
shugabanni tun daga Shugaban Nijeriya har zuwa shugabannin ƙananan hukumomi za su yi jawabi ga ‘yan ƙasa, ko a fili ko cikin kafafen
labarai, to lalle a tsakuro wani ko wasu baitocin da suka dace da jawabin da
zai yi. Haka kuma za a yi idan za a karanta labarai. Da yake ana yaƙi ne da cin hanci da rashawa ana iya amfani da waɗannan baitoci ko ɗaya daga cikinsu a rera kamin
shugaban ya soma jawabinsa ko kamin a fara karanta labarai:
3. Yaƙi da rashin yin tarbiya
Cin hanci rashwa shan giya
Sata da fashi Najeriya
Sun kinkima ba mu da lafiya
Ƙuma cuta sai Najeriya
Doki koya mai taƙama
Aka yi da matsi mai gardama
Sa mai ƙaimi ka yi mai tsuma
In ka ƙyale har yat tuma
Rame zai kai ka cikin ƙaya
5.Kai shugaba in ka hanƙure
Kuma kai shayi yaƙ ƙetare
In ka hora yah hinjire
In ka yi laho yas sandare
Zai ɓata dubu Najeriya
Taushe haƙƙi na mutum shikai
Zalumci shi na ɗai shikai
Kowa ya san yi nai shikai
Wani bai cewa an taimakai
Halin manyan Najeriya
Jinsin wasu in ya kangare
Aika musu soja su tsattsare
Ka hana su tudu su yi gangare
Mabuga karnai na nan tare
Yi da gaske ka bar wani
tausaya
8. Ji takaici ni kam ya isan
Sarkin sata mai son shi zan
Shi riƙe samu gona ta zan
Mulkinai mu ko duk mu zan
Banzar banza Najeriya
(Alƙali Alhaji Haliru Wurno:Yaƙi Da Rashin Tarbiyya Da Rashawa)
A nan Haliru Wurno yana magana ne da shugaban ƙasa ko gwamna. Ya kasance wanda ke yi wa shugaba tunatarwa ko ma
ba shi labari kan yadda wasu ‘yan ƙasar nan suka zamo da kuma manufarsu ga ƙasar da mutanenta. Haliru yana son shugaba ya tashi tsaye ya nuna
halin ba sani ba sabo. Wannan tunatarwa za ta sa wa shugaba ƙaimi wurin tabbatar da cewa doka ta yi aiki sosai.
Akwai kuma baitocin da ke yin kira ga Shugaba da ya bi waɗannan masu cuta wa ƙasa guda guda don a hukumta su. Suna da yawa don Haliru bai bar
kowa ba:
23. Sannan a biyo ga sarakuna
Da ciyamomi da akawuna
A bi hakimmai sanatotuna
A bi darakatoci ko’ina
A tsare su tsaro Najeriya
24. Ka ba su amana ci sukai
Fasa-ƙwabri shina nan yi sukai
Doka ko ka yo ƙi akai
Doka ko ɗai yasat
sukai
Ta nakkasa mu mun sha wuya
Haliru bai tsaya nan ba sai da ya fito ƙarara ya bayyana mummunar rayuwar da wasu shugabanni da ke ƙarƙashin Shugaba ke yi. Haliru sai
da ya ja kunnen Shugaba da kada ya saki fuska:
Ikon banza na shi akai
A ci rashwa hanci ci akai
Manyan nan su nay yad da kai
Fadar kowa yau shi akai
Yi da gaske ɗumi bari dariya
35.Wac ce a yi mulki ba matsi
Iko na ko ko yamutsi
A gama da wuta ta yi tartsatsi
Ta game tawaye da tabbatsi
Su lafa cilas su bi gaskiya
Cewa mulkin ga ka san na kai
Ba mulki na ba da za shi kai
Ga bukata kowa ba shi kai
In babu biyayya sariƙai
Ka zama manya Najeriya
A yi sata bayyane an gani
An kam mai mai abu na gani
A hana mai ba shi da magani
Ko ya tafi ya yi ta gunguni
Bai bai mai sata ya ƙiya
Amma gyara cilas akai
Ba don bisa son ran fasiƙai
In an ƙi a yo haka an sakai
In an bi bukatar sariƙai
Wannan mulkin bai moriya
An ɗauki ƙaho an ƙarfafa
Ya gina gida ya kallafa
Ji haya shika yi ya yo ƙafa
Kangonai har yaƙ ƙarfafa
A biɗe shi a binciki gaskiya
40.Mai ɓaɓatu azzalumi
Doka ta yi mai takunkumi
Shaiɗanin nan algungumi
A rufe shi a bar shi shi sha gumi
Shi bi dokokin Najeriya
Wannan waƙa da ire-irenta sun dace ainun da
a riƙa amfani da su a kafafen labarai
maimakon waƙe-ƙaƙe da raye-rayen Turawa da ake cika kunnuwan matasa da su dare da
rana.
3.3 Sanya Baitocin Waƙa Kan
Allunan Sanarwa
Lokacin da marubucin wannan muƙala yana ɗan makarantar sakandare ya sha
karanta wata takardar yekuwa a titunan Sakkwato da na Birnin Kabi inda yake
makarantar. Saƙon da wannan takardar yekuwa take
isarwa shi ne, “a daina shan ƙwaya mai
firgitarwa”. A kan
takardar sai aka yi zanen wani matashi mai yamutsattsen gashi a kansa, idanunsa
turu-turu kuma jajir, ga shi kuma sanye da tsumma. Sai aka koma gefen wannan
matashi aka rubuta ɓaro ɓaro:
ƊAN ƘWAYA GA ƘARSHENKA ! !
Wannan yekuwa ta yi tasiri ainun kan mai wannan muƙala domin ta hana shi shiga gungun 'yan makaranta mashaya ƙwaya!!!
Akwai tarin waƙoƙin da ke faɗakarwa
irin wannan takardar yekuwa. Za a samu nasara mai girma idan Hukumar Labarai da
Al’adu ta
tanadi waɗannan waƙoƙi, ta yi amfani da baitocisu ta
rubuta takardun yekuwa ta kuma lilliƙa su ga
allunan sanarwa cikin garuruwa. Dubi wannan misali:
25. Can a cikin gari ka gina masallaci daidai,
Kuma bayan gari ka yo hotel, to kai ko dai,
Ai hanya guda mutum shika
bi, shi ad daidai,
Ba shi zamo muzabzabi ba
shi ce ya yo daidai,
Wanga irin dagwalgwale ni
kam ban gane ba.
26. Namiji da macce na rawa
haɗe shin,
ko culture na?
Tambayi Baba Soja mai
culture ko mina na?
Mu kam dai ga namu addini
shi halɗi na,
Halɗi ko ga namu addini ya zam ɓarna,
Kuma Baba Soja ya yi kurum
bai tanka ba.
27. Sai dai na ga Baba Soja shina
son amsa min,
Harkaz zamani shina da saninta
shi koya min,
Ni ban gane inda ake ba sai ya
nuna min,
Amma Baba Soja am bari dus
son gyara min,
Gyaran dud da kai yi don
banjo ban amsa ba.
(Alhaji (Dr.) Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu:Gargaɗi Ga
Matasa)
Ba lalle ne a rubuta dukan baitocin kan takardar yekuwa ɗaya ba. Hukumar Labarai da Al’adu ita ce ta fi sanin yadda za ta yaɗa su, amma fa tare da shawarar
manazarta waƙoƙi. Ga
wani misali:
10. Don Allah Mallama am ji
jawabina
Daɗa ko ki so shi ko ki ga aibi na
In na faɗe shi na san haƙƙan na
Ilminki babu amre shibci na
11.
Ilminki babu amre sharri na
Sheɗan ka ɗunguza ki cikin ɓanna
Ki yo ta
ba ki dubin aibi na
Kullun faɗin kikai injoyin na
12.
Sai radda kig ga ke rasa mai son ki
Duw wanda
kin nuhwa bai dubin ki
Mai son
ki dauri ya bar shawak ki
Sannan ki
sa kiran yo ni kaina
(Sambo Waliyyi Giɗaɗawa: Waƙar To Da Ke Nike)
3.4 Rubuta Da Rera Baitocin Waƙa Cikin Azuzuwa Da Allunan Sanarwa
Makaranta ita ce mai gina tarbiyya ta biyu bayan iyaye. Dalili ke
nan da ya sa ba a wofintar da ita ba a duk tsawon zamani, tun daga lokacin
jihadi har zuwa yau. Yadda za a iya inganta wannan hanya ita ce a ƙarfafa rubuta da rera waƙa ko
baitocinta cikin azuzuwa da allunan sanarwa na makaranta. Malamai musamman na
fannin ilmi su suka kamata su ba da shawara kan ina ne za a yi amfani da wane
irin salo. A ganin wannan muƙala a ƙananan makarantu ya fi dacewa a rubuta a kuma rera waƙoƙin. Za a lilliƙa takardu masu baitocin waƙa a
bangunan cikin aji. Haka kuma zai dace a riƙa rera
baitocin ko ma dukan waƙoƙin cikin
aji tare da yara a duk lokacin da aka ga ya dace. Dabarar Alhaji Shehu Shagari
wadda ya kwaikwayi malaminsa babbar dabara ce a nan. Yakan rubuta baitoci domin
yin bita da ƙarfafa darussan da ya karantar da
yaransa. Ya shiga aji ya rera tare da su.[i] Haka
kuma zai dace idan malamai suka riƙa rera wa
ɗalibansu
ire-iren waɗannan waƙoƙi. Waƙar “GargaɗI Ga ’Yan Makaranta” ta Wazirin Gwandu ta dace ainun ga ‘yan makarantun furamare. Ga
kaɗan daga
baitocin wannan waƙa:
4. Ku 'yan uwana duk ku zo,
Ku ji gargaɗi in na faɗai.
5.
Zancen ga ba ni naf faɗe-
shi
ba, Mallamina yaf faɗai.
6. Almajirai muke ni da ku,
Gun
malami muke tun daɗai.
7. Malam ka yo mana gargaɗi,
Mu
tsaya mu ji shi mu ko riƙai.
8. Ahnajiri ɗan malami,
Don
shi ka renonai daɗai.
9. Ya ce ɗiyana duk ku zo,
1n
ba ku jalli kwat tsarai.
10.
Shi zai ci riba duk da riba
Arziki
sai an faɗai.
11. Ba dukiya zan ba ku ba,
Jallin
da baki zan faɗai.
12. Wada naf fi so ku taho
ku ji,
Ku
tsare da kyau in na faɗai.
13. Kowat tsare shi shi
tabbata,
Babban
rabo na nan garai.
14. Wada anka so almajiri,
A
ishe hali mai kyau garai.
15. Duka lokacin sallah
shina-
Tsare,
duk da tasbi ag garai.
16.
Mai hankali mai girmamawa,
Har
a san ladabi garai.
17. Shi fake amanam malami,
Shi
tsare umurninai garai.
18. Na gabansa ko ba
malami-
Ba,
shi zan tsaron girma garai.
19.
Tsararsa duk shi fake mutum-
cin
nasu har irli, tsarai.
20. A ishe shi ba shi da
twakara,
Kuma
hanƙurewa ag garai.
21. Da cikin aji da cikin
gari,
A
ishe haIin girma garai.
22. Kyawon hali shi am
mutum,
Sannan
a so ilmi garai.
23. A cikin aji in an
shiga,
A ishe akwai himma garai.
Bayan da Wazirin Gwandu ya bayyana yadda ya kamata ɗan makaranta nagari ya kasance,
sai kuma ya kawo halayen ɗan
makaranta mara halaye nagari. Ga kaɗan daga ciki:
36. Ibi1isu na shaiɗanu na,
An gane
taurin kai garai.
37. Mutakabbiri na, makiri,
An gane
girman kai garai.
38. Ga fakon amana shi da ɓe-
ra ɗai, yawan ɓarna garai.
39. Ko an yi foro ba shi
ji,
Halin
batsalci ag garai.
40. Babba da yaro ɗai garai,
Duk
babu mai girma garai.
41. Tsararsa bai da
tagomashi,
A cikinsu
don fitina garai.
42. Ga twakara da yawan faɗa,
Haka
nan yawan ƙara garai.
43. Tcintce gare shi da
tsegumi,
Haka
nan yawan ƙarya garai.
44.
Ko ya fadi, mu ba mu amsa,
Tun da
kissoshi garai.
45. Da cikin aji da cikin
gari,
Kowa shi
nemi tsari garai.
46.
Mugun hali ɓarnar
mutum,
Ko da
akwai ilmi garai.
47. Balle daƙiƙi na balidi,
Babu
amfani garai.
48. A cikin aji in an
shiga,
Abada
yawan barci garai.
49.
Ai gwamma kwananai, zama,
Falken
yawan yaya garai.
50. Fashi shi kai bai
zakkuwa,
Bisa lokaci
makara garai.
51. Da fita aji ya garzaya,
Wajjemmu
ba matsaya garai.
52. In son ganin samnan
kakai,
Tafi can
tashar mota tarai.[i]
Ya kamata a ƙarfafa nazarin ire-iren waɗannan waƙoƙi da suka ƙunshi saƙonnin tarbiyya cikin manyan makarantunmu..
Baya ga haka zai dace a riƙa kakkafa
allunan sanarwa a wurare daban daban cikin makaranta. Waɗannan allunan sanarwa za su
kasance ɗauke da
baitocin da ke ƙunshe da saƙonnin tarbiyya. Ga misalin irin waɗannan baitoci:
28. Jami’a ban barin ta sai na taɓe ta
Don sanin
martabam mazauna cikinta
Masu ilmi
da hankali ag gare ta
Bincikawa
da gaskiya sai ɗiyanta
Hece
tarke sukai da ƙaiƙai ga
tsaba
29. Na ji
kumyag ganin kaɗan za su ɓata
Martabaj
jami’a da hallan zamanta
Sheɗanad dud da za ta taso gwaninta
Jami’a
yaf fito sani ya mugunta
Bai
da rana gare mu in ban da ruba
(Alhaji
Garba Gwandu: Gaskiya, Bulaliya Ta Biyu)
Waɗannan baitoci misali ne na ire-iren baitocin da suka dace a kafa
allon da ke ɗauke da
su a kan hanyar malamai ta zuwa azuzuwan makaranta da wuraren tarukansu, kamar
majalisar jami’a. Ga
wani misali:
13. Akwai
wasu malammai na tauye maki[i]
Ga ɗalibbansu ko da sun yi kirki
Su
ja wani can su isammai da aiki
Amana
kun ga tun nan ta yi miki
A
iske malami na ƙuntatawa
14.Sanina
mallami matsayin uba na
Ga su ko ɗalibai manyan ɗiya na
Su duka
nashi na haka za mu zamna
Malam sad
da ya ƙi tsaron amana
Sani
yaka wa jafa’i bai tunawa
15. Abin
da ka girgiza ni ga lokacinmu
Ga
malammai masoya shiryuwarmu
Amana ta ƙaranta bale gare mu
Abin ga
wane wuri na za shi kai mu
Ganin
ulama’u sun shiga barkacewa
(Alhaji Garba Gwandu:Amana Hanyar Shiriya)
3.5 Ƙarfafa
Gasar Rubuta Waƙoƙi Kan Tarbiyya
Daga cikin hanyoyin da suka shigo na amfani da waƙa don bunƙasa ta da kuma shirye-shiryen
hukuma, akwai shirya gasar waƙoƙi a inda kuma manazarta waƙoƙi kan gabatar da muƙaloli don
tattaunawa. Waƙoƙin da
irin wannan shiri kan haifar suna da matuƙar amfani
saboda ingacinsu da kasancewarsu wata hanya da ke buɗe ido ba ga al’umma ba kurum, har ma da su mawaƙan kansu. Ta nan ne za su goge ga shirya waƙa. Ta nan ne za a samu waƙoƙi masu nagartattun jigogi, ciki har da na tarbiyya. Ya kamata
Hukumar Labarai da Al’adu ta ƙarfafa wannan hanya. Ta wannan hanya gwamnati za ta iya samar da waƙoƙin da ke cusa tarbiyya ga
al’umma. Haka kuma hukuma na iya kwaɗaita ma jama’a yin
amfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo don yaɗa baitoci masu amfani.
A ƙarshe, mai karatu na iya cewa muƙalar nan ta yi kira ga Hukumar Labarai da Al’adu, alhali kuwa Gwamnatin Tarayya take da
wannan hukuma kuma tilas ta rungumi dukan ƙabilun
Nijeriya. Wannan batu haka yake, kuma ba lalle ne wasu ƙabilun Nijeriya su kasance suna da rubutattun waƙoƙi ba, sai dai na baka. A wannan
fuska, matsalar mai sauƙi ce. Hukumar Labarai da Al’adu da makamantanta na jihohin, da ma sauran
hukumomi kamar makarantu, na iya amfani da waƙoƙin baka don yin yaƙi da
rashin tarbiyya da karɓar
rashawa. Hikimomin da ke cikin rubutattun waƙoƙi akwai su cikin na baka domin da waƙar baka
da rubutatta duk sunansu waƙa kuma
bori guda suke yi wa tsafi. Dukansu da ire-iren salo ɗaya suke isar da saƙonninsu ga jama’a, salo
kuwa shi ne asirin waƙa.
KAMMALAWA
Wannan muƙala ta yi ƙoƙarin bayyana yadda aka sha yin yaƙi da rashin tarbiyya a ƙasar
Hausa ta yin amfani da rundunar rubutattun waƙoƙin Hausa. An fara kai farmaki da wannan runduna aƙalla tun a ƙarni na 17, kuma tun daga lokacin
rundunar ba ta karaya ba. Dubarorin da kuwa ta yi amfani da su sun haɗa da almajirai da ke nazarin waƙoƙin, da rera su a masallatai da
fadar sarakuna, da cikin gidajen ma’aurata da kuma kafa ƙungiyoyin ‘yan taru.
Amfani da waƙoƙin ya ci
gaba musamman ta fuskar miƙa su ga
almajirai, su kuwa su rera wa jama’a ko a ƙofofin gidaje ko kuma a
masallatai. Haka kuma akan rera waƙoƙin a tarukan siyasa kamar yadda muka ga su Sa’adu Zungur da Mu’azu
Haɗeja da Aƙilu Aliyu suka fara yi, har zuwa rera su a gidajen watsa labarai
kamar rediyo da talibijin da shafukan zumunta na yanar gizo da naɗiyarsu cikin kases-kases ko faifan
konfuta.
MANAZARTA
1. Abdulƙadir, Ɗ. (1979), Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da Da
Na Yanzu, Lagos:
Nijeriya.
2. Adamu,
S. A.S. (babu kwanan wata da maɗaba’a), Bassu al- Aɗaa’i: Sharh Ƙurɗabi, Dutse:
Jigawa, Nijeriya.
3.
Ahmad, A. S. (1983), ‘Rayuwar Marigayi Abubakar Maikaturu Alƙanci Sakkwato Da Waƙoƙinsa’, kundin
digiri na farko, Sokoto: Jami’ar
Sakkwato.
4.
Ainu, H. A. (1984), ‘Malam Ibrahim Khalilu Marina Tsamiya Sakkwato
Da Waƙoƙinsa’, kundin digiri na farko, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.
5. Aliyu,
A.A, (2007), Fasaha Aƙiliyya, Zariya: NNPC.
6. Al-Qurtubi,
Y.I.Y.A.Y. (r. 303H.), Manzuumat al- Qurtubiyy fi al- Ibaadaat ala
Mazhab al- Imaam Maalik, Sokoto: babu sunan maɗaba’a da shekarar bugawa, amma wanda ya ɗauki nauyin sake bugun shi ne, Alhaji Muhammadu Mahi ɗan Malammai Kanwuri Sakkwato.
7.
Boyd, J. (2000), The Caliph’s Sister: Nana Asma’u
1793-1865- Teacher, Poet and Islamic Leader, London: Newbury House,
900 Eastern Avenue.
8.
Bunza, A.M. (2002), Yaƙi Da Rashin Tarbiyya, Lalaci, Cin Hanci Da Karɓar Rashawa, Lagos: Ibrash Islamic
Publications LTD.
9. Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya (2006), Ƙamusun
Hausa, Kano: Jami’ar Bayero.
10. Ɗangambo, A. (2007), Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa, Zariya:
amana publishers ltd.
11.
Department of Nigerian Languages (2013), Zauren Waƙa: Journal of Hausa Poetry Studies vol.1No 2, Zariya: Ahmadu Bello University
Press.
12.
Department of Nigerian Languages, ƊUNƊAYE:
Journal of Hausa Studies vols. 1-5, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
13.
Department of Nigerian Languages ALGAITA: Journal of
Current Research in Hausa Studies vol. 1 No 1-4, Kano: Jami’ar Bayero.
14.
Department of Nigerian Languages (2013), Zauren Waƙa: Journal of Hausa Poetry Studies vol. 1, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
15.
FAIS Journal of Humanities vol. 3/I (2004),
Kano: Jami’ar Bayero.
16. Giɗaɗawa, A.M.B. (2006), Bargon Hikima, Sokoto: Cibiyar Nazarin Hausa,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
17. Haɗeja, M. (180), Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, Zariya: NNPC.
18.
Junaidu, S. (1990), ‘Resistance to Western Culture in the Sakkwato
Caliphate: a Lesson to Generations Yet Unborn’ cikin A.M. Kani da K.A. Gandi
(editoci), State and Society in the Sokoto Calphate (1990),
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
19. Kani,
A.M. da Gandi, K.A. (editocin, 1990), State and Society in the Sokoto
Calphate, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
20.
Muhammad, Ɗ (edita) (1990), Hausa Metalanguage, Ibadan:
University Press Limited.
21.
Omar, Dr.S. (2014), ‘Yantarun Nana Asma’u Ɗanfodiyo: Tsarinsu da Taskace Waƙoƙinsu, Lagos:Zeetma Investment Limited.
22.
Omar, S (2013), Fasahar Mazan Jiya: Nazari a kan Rayuwa da
Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja, Kaduna: Garkuwa Media Services
LTD.
23. Sa’id,
B (1978), ‘Gudunmawar Waƙoƙin Masu
Jihadi”, kundin
digiri na biyu, Kano: Jami’ar
Bayero.
24. Shagari,
A.S. (1978), Waƙar
Nijeriya, Zariya:
NNPC.
25.
Sokoto, I.J. (2007), Tsarabar Waziri Buhari da Waziri
Junaidu ga Manazartan Waƙoƙin Hausa, Sokoto:
Al-Amin Printing LTD.
26. Talata
Mafara, M. I. (1999), Daular Usmaniyya 1-3, Abakwa, Kaduna:
Nadabo Print Production.
27. Usman,
B. B. (2006), ‘Hikimar Magabata:Nazarin Ƙwaƙƙwafi a kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru NasarawaWazirin Gwandu
(1916-2000) da Waƙoƙinsa’, digiri na uku, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
28.
Yahaya, I.Y. (1988), Hausa A Rubuce:Tarihin Rubuce-Rubuce
Cikin Hausa, Zariya:NNPC.
29.
Yahya, A.B. (1986), “Tattalin Zaɓen Rubutattun Waƙoƙin Hausa Domin Yara”, hukumar Nigerian Book Development Council ta shirya a Kaduna, an
buga cikin FAIS
Journal of Humanities vol. 3/I (2004), Kano: Jami’ar Bayero.
30.
Yahya, A. B. (1990), ‘The Significance of the 19th Century
Poetry Teachingss’ cikin, A.M. Kani da K.A. Gandi (editoci), State and
Society in the Sokoto Calphate, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
31.
Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna:
FISBAS Media Services.
32.
Yahya, A.B (2001)“Dangantakar Waƙa Da
Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa” cikin Harsunan
Nijeriya xix, Centre for The Study of Nigerian Languages, Bayero
University, Kano, p.94-109, Kano.
33.
Yahya, A.B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Kaduna:
FISBAS Media Services.
34. Yahya A.B. da Ainu, H.A. da Idris, Y.
(editoci) (2015), SAI ALU:Sharhi Kan Waƙoƙin Da Aka Yi Wa (Dr.) Aliyu Magatakarda Wamakko, Zariya:ABU Press.
35.
Yakubu, A.M. (1999), Sa’adu Zungur: An Anthology of the
Social and Political Writings of a Nigerian Nationalist, Kaduna:
Nigerian Defence Academy Press.
36. Zungur,
S. (1968), Waƙoƙin Sa’adu
Zungur, Zariya:
NNPC.
0 Comments
Rubuta tsokaci.