Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin wai idan mutum zai yi tsayuwar dare, sai ya yi shafa'i ya bar wuturi, sai bayan da ya kammala tsayuwar daren, mene ne ingancin hakan?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin wai idan mutum zai yi tsayuwar dare, sai ya yi shafa'i ya bar wuturi, sai bayan da ya kammala tsayuwar daren, mene ne ingancin hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan Zance Ba haka yake ba, Yin Wuturi ga Mai tsayuwar dare, kala biyune.

Na farko: za ka iya yin wuturinka bayan Sallar Isha'i, Sannan idan kasamu dama Allah ya taimakeka ka farka cikin dare ka yi ƙiyamullaili, raka'a biyu biyu, Ba za ka sake yin wani wuturin Ba a ƙarshe.

Na Biyu: za ka iya jinkirta wuturi izuwa ƙarshen dare, idan ka kammala tsayuwar darenka saikayi Wutirinka daka ƙarshe..

Kamar Yanda Aka tambayi Shaik Bin Baaz Rahimahullahu a kan irin wannan tambaya yabayar da irin wannan Amsar a cikin, Maj mu'u fatawa dinsa (11/312).

 Sai dai Wasu Malamai Suka ce: Wanda ya fi shi ne ka jinkirta yin wuturi din zuwa ƙarshen tsayuwar daren, karka yishi afarkon dare..

Saboda hadisi ingantacce da ya zo a kan hakan Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Kusanya ƙarshen sallar ku da daddare ta zama wuturi, ).

Duka biyun In mutum ya yi babu laifi akwai sahihan hadisai akai.

Amma Na biyunne ya fi falala, wanda za ka bari saika gama sallar daren sananna saikayi wuturin aƙarshe.

Fatawa lajnata ta yi fatawa dana biyunne, Ƙar-ƙashin fatawa ta (207) a cikin mujalladi na (7).

WALLAHU A'ALAM.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments