Dukkan Mu Ba Za Mu Kuɓuta Ba A Kan Wannan Hakkin A Gaban Allah

    Muna wani zamani wanda duk unguwar daka shiga idan ka lissafa gidajen aure za ka samu iyaye maza da yawa sun mutu sunbar iyaye mata da tarin 'ƴa'ƴa.

    Za ka samu kuma iyayen mata basuda wata sana'a mai karfi a hannunsu da suke yi da take taimaka musu wajen iya kula da ciyarwa da tufatarwa dama karatun yaran nasu.

     Sannan kuma za ka samu a cikin unguwar a maƙontansu akwai masu tarin arzikin da za su iya taimaka musu, ALLAH ya ba su rufin asiri amma ba za su taimakesu da komai ba, sai gulma.

     Akwai wanda za ka ga yawon bara mahaifiyarsu take yi, tana nemawa kanta da yaranta abin da za suci, amma kuma maƙobta basa iya taimaka mata, kuna sun iya su koma gefe suyita gulmarta.

     Koda da addu'a ne basa taimaka musu, kuma wata ƙilama sanda mahaifinsu nada rai ya yi taimako iri-iri a cikin wannan unguwar, amma da zarar ya koma ga ALLAH babu mai kula da nasa matan da yaransa.

     Sai kaga marayu suna galaibaita a gari, yara nata shiga harkar daba, ga sata, kaga maraya ya zama ɗan neman maza, duk saboda ya sami abin da zaici.

     Zakaga marainiya ta zama karuwar lungu duk saboda ta sami abin da za suci su sha, ko ta zama ƴar maɗigo saboda ta rasa taimakon Al'ummar unguwarsu, kuma sai a koma gefe anata gulmarta, ai duk zamuje mu tarar da ALLAH.

     Idan kaga mutanen unguwa suna magana a kansu, to an sami wata marainiya ta yi ciki, ko an sami wani maraya ya yi sata kodai ya aikata wani abu mara kyau, to anan ne zakaji anzo ana musu jaje, agama a koma gefe ayita zaginsu, ai zamuje mu tarar da ALLAH.

     To lallai mu sani suna da hakki akanmu, dolene mu kula da cinsu da shansu, da karatunsu, da kuma tarbiyyarsu domin ALLAH ya wajabta mana hakan, kamar yadda ya wajabta mana na 'ƴa'ƴanmu.

     Domin girman hakkin maƙobci a gurin ALLAH kai kace maƙobci zai iya cin gadon maƙobcinsa.

     WALLAHI dukkanmu sai ALLAH ya tambayemu a kan cinsu da shansu, da tarbiyyarsu da lafiyarsu, sun yi bacci mai daɗi ko basuyi ba, suna da lafiya ko basuda ita, sunje makaranta ko basuje ba.

     Rashin kiyaye haƙƙoƙin jununmu ya sa bama samun nutsuwar rayuwa, ga kuɗin ga komai amma babu nutsuwa, shi ya sa ALLAH ya cire albarka a rayuwar mu.

     Babu wani maƙobci da zai kwanta da yunwa alhali maƙobcinsa yana da abinci a wadatacce a cikin gidansa, face sai ALLAH ya yi masa azaba a kan yabar maƙobcinsa ya kwana da yunwa.

     Idan kuwa aka dafa abinci a gidanka, sai maƙobcinka ya jiyo ƙamshin girkin gidanka, to wajibi a gareka ka aika masa da wannan abu da aka dafa a gidanka, inba hakaba, sai ALLAH ya tambayeka hakkin ƙamshin da ya ji kuma baka bashi ba.

     Wani kuma za ka ga ɗan uwansa yana da gidaje sunfi 5 a unguwarsu na haya, amma ga ƙaninsa ko yayansa yana yawon haya, bazai iya taimaka masa da koda ɗaki ɗaya ba, ya zauna da iyalansa ba, kai kace mutum shi yakewa kansa Arzuki.

    ALLAH TA'ALAH ka ba mu ikon aiki da abin da muka karanta.

    ALLAH ka yafe mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.