𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum
Dan Allah Malam tambaya ce Dani kamar haka : Da azumi ne bayan an kira sallar magriba naci dabino nasha ruwa, naje zanyi alwala ina tsugunnawa sai na ga jini ya zo min kuma ban gansa a kan pant dina ba.
Ina tunanin adaidai lokacin ya zo. Shin yaya azumina ?
Na biyu kuma ina da matsala ne duk bayan kwana 8 da gama
period dina akwai wani ruwa mai yauki da yake zubo min Wanda likitoci suke cewa
ovulation period toh idan yana zuba ina ganin 'dan jini-jini aciki, kuma yana
daukar lokaci kafin ya daina zuba har sai yakai lokacin zuwan wata al'adar, ko
kuma brown ɗin ruwa ya dinga zuba shi ma haɗe da jini kuma ba
lokacin al'adata bane ko yau na yi wanka toh gobe zai iya dawowa toh gaskiya
ina rikecewa game da ibadata cikin azumi nagani har sau 2 Dan Allah yaya batun
ibadata da azumina??.
Dan Allah zan iya yin azumin ahaka? kuma idan na daina
ganinsa dole sai na yi wanka?
Dan Ina wahala duk randa ban gansa ba sai na yi wanka
kuma ajima kaɗan zai sake dawowa Dan Allah abani fatawa yana daga cikin
jinin hailata ne ko kuma na cuta ne??.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
1. Amsar tambayarki ta farko : Azuminki yayi. Tunda jinin
ya zo ne bayan faɗuwar rana.
2. Amsar tambayarki ta biyu : Akwai hadisin Ummu A'diyyah
(ra) wacce tace "Sun kasance (su matan sahabbai) ba su yin la'akari da duk
wani digon jini ko gurbatacce jini (Coffee Colour) da duk wani fatsi-fatsi idan
ya zo musu bayan sun riga sun yi wankan tsarki (bayan kammalar jininsu na
haila).
Bisa wannan dalilin ba za ki sake wanka dan kinga irin
wanann ya digo miki ba. Wankeshi kawai za ki yi kici gaba da sallarki.
Sai dai idan kika gan shi ya dawo bisa kalar jinin haila
da siffofinsa, to sai ki dena yin sallah har sai ya dauke. Kuma za ki dora
lissafin kwanakinsa ne a kan wadancan kwanakin da kikayi na haila. Idan
lissafin yakai kwana 15 shike nan sai ki yi wanka kici gaba da yin ibadarki.
Jinin ya zama na Istihadha ke nan. Bazai hana yin sallah ko azumi ba. Sai dai wajibi ne ki rika yin sabon tsarki, da sabuwar alwala kafin kowacce sallar farilla. Kuma za ki iya haɗa azahar da la'asar, hakanan ki haɗa Maghriba da isha'i .
WALLAHU A'ALAM.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.