𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, ya gida ya azumi, don Allah malam ina da tambaya, in lokacin hailata ya zo ina yin kwana 6 da shi, to wannan karon ya zo min na yi kwana 6, sai na ga alamun tsarki na yi wanka na yi azumina na rana daya, washe gari na sake tashi da azumi daidai ƙarfe Tara na safe sai na ga wani jini yana fita, to wannan jinin na hailan ne ko kuma istihada ne? Kuma ya matsayin azumin jiya da na yi kuma zan rama ne ko kuma yana nan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, duk matar da jinin haila ya zo mata
sau biyu a cikin kwana goma sha biyar, to da jinin farko da na biyu duka haila ɗaya ne, misali
kamar yadda kika ce; kin kasance kina yin al'ada na kwana shida, da kwana
shidan suka cika, da aka kwana biyu sai ya dawo, to a nan tun da tsakanin jini
na farko da jini na biyu ba a sami kwana sha-biyar ba, to za ki lissafa shi ne
a matsayin jinin farkon nan ne ya sake dawowa, saboda malamai sun bayyana cewa
Sai idan jinin haila ya cika kwana sha-biyar bai ɗauke ba ne yake
zama jinin istihala, kuma a tsakanin haila zuwa wata haila sai ya kai kwana
sha-biyar musamman a maz'habar Malikiyya, a wata maz'habar kuma kwana sha uku,
saboda haka wannan jini da ya sake dawo maki ba jinin ciwo (istihadha) ba ne,
jinin hailan nan ne ya sake dawowa.
Shi kuma hukuncin azumin da kika yi na ranar farko da
jinin ya yanke, wannan azumi ya inganta, amma azumin washe gari da jinin ya
sake dawo maki, wannan azumi ya ɓaci, za ki rama shi in Allah ya kai mu bayan sallah,
saboda duk azumin da aka yi shi a cikin jinin haila wannan azumin bai inganta
ba, idan ma da gangan aka yi, to ya zama laifi domin Shari'a ta hana, idan kuma
da kuskure ne kamar wannan, to babu laifi, saboda Allah ya yafe wa al'ummar
Manzon Allah ﷺ abin da suka yi shi da kuskure, kamar yadda Annabi ﷺ ya faɗa a wani hadisi.
Allah ne masani.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.