Ticker

6/recent/ticker-posts

Banbancin Tsakanin Jinin Haila Da Na Cuta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullah... Malam muna godiya Allah ya sa a mizani... Tambayata ita ce dan Allah wanne alamomi mace za ta duba ta gane jinin haila da na cuta... Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu Wa Rahmatullah. Amin na gode. 'yar'uwa jinin cuta shi ne jinin da ke zubo wa mace ba a lokutan da ta saba ganin al'adarta ba, saboda wani rashin lafiya, ko kuma daga wata jijiya. Amma shi kuwa jinin haila jini ne na ɗabi'a da ke zubo wa mace a cikin ranakun al'adarta na wata-wata.

Ana iya bambance tsakanin jiinin haila da na cuta ta hanyoyi kamar haka:

Jinin haila jini ne mai duhu, kuma yana da shinshi ne maras daɗi ko bashi-bashi, a wasu lokutan yana yi wa mace raɗaɗi a farkon lokacin zuwansa.

Shi kuwa jinin cuta ba shi da duhu, kalarsa jazur ne, kuma shinshi nensa ba ya bashi-bashi .

Haila tana wajabta hana yin sallah da azumi, da saduwa da iyali, kuma tana wajabta yin wankan tsarki idan mace ta tabbatar ta sami tsarki. Saboda faɗin Allah Maɗaukakin sarki a Alƙur'ani cewa: "Idan suka yi tsarki, to sai ku zo masu ta inda Allah ya umarce ku" Suratul Baƙara (222).

Da kuma maganar Manzon Allah ga Faɗima 'yar Abu Hubaish cewa: "Idan haila ta zo maki, to sai ki dakatar da yin sallah, idan kuma hailar ta ɗauke sai ki yi wanka kuma ki yi sallah". Albukhariy (320), Muslimn (333).

Amma shi kuwa jinin cuta, jini ne gurɓatacce da ba ya hana yin dukkan ibadoji, kuma ba ya wajabta yin wankan tsarki idan ya ɗauke. Duk wanda jinin cuta ke zuwa mata ana hukunta ta ne a matsayin mai tsarki, sai dai dole ne sai ta riƙa yin alwala a lokacin kowace sallah, ba za ta yi alwalar ba sai lokacin sallar ya shiga.

Allah Ta'ala ne mafi sanin dai-dai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/I08Ƙc4ehEctLMSfks5awuZ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments